CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske Writers association????
[3/19, 9:36 PM] El-hajj????: ⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

75…..

Washegari da ya kasance litinin misalin karfe takwas na safe Zahrah ta fito daga part din mai martaba bayan ya bata umarnin da ta tafi ta gaida Ummanta da stepmum dinta kilishi, bata yarda ta kwana ko ina ba sai gun sa tunda shi kadai ne bai gujeta ba, kuma ga bakin da suka dinga tururuwan xuwa ganinta tun a daren jiyan hakan yasa tayi xamanta gun Abbanta, a nan part din nasa tayi shiryawarta ta saka kayan da jakadiyar Umma ta kawo mata da safen, bangaren Ummanta ta nufa fuskarta rufe da hular alkyabbar jikinta don bata son kallon da ake mata, xuciyarta fal tunanin Junaid ta dinga tafiya a hankali, ta rasa dalilin da ya tsaya mata a rai haka, har mafarkinsa sae da tayi daren jiya, gashi ko ganesa ta tabbatar baxa tayi a hanya ba da xa su hadu, bata damu da mutanen da ta dinga wucewa ba wasu na gaisheta wasu na mata sannu da xuwa har ta iso bangaren Umma, xaune ta sameta parlor ga baki da dama xaxxaune parlon, da ganinta kasan har lokacin bata yi recover daga shock din jiya ba, a sanyaye Zahrah ta karasa har tsakar parlon ta duka ta gaida mutanen dake ta kallonta ko wannensu ya amsa mata cike da fara’a, karasawa tayi gaban Ummanta ita ma ta gaisheta, amsa mata tayi cikin sanyin murya tana kallonta, kasa ci gaba da tsayawa gun Zahrah tayi, ganin Umma taki sakewa da ita, ta mike kawai ta fice hawaye cike idonta, bangaren Kilishi ta nufa nan ma baki ta samu fal a parlon, ba laifi kilishi ta ja ta jikinta hawaye na sakko mata tace “Sannu Zahrah, Allah ubangiji ya kara mana tsawon rai mai amfani….” Rungumeta Zahrah tayi tana kuka, nan ta dinga lallashinta tace “Gode ma Allah xatayi da bawan Allahn da ta dalilin sa ta dawo gida yanxu” jikinta ya kuma yin sanyi sosai ta ji banda taga junaid bbu abinda ke damunta yanxu, mikewa tayi tana share hawayen ta, Ummi ta gani tsaye ita ma tana hawayen, da sauri ummin ta karaso ta rungumeta tace “I missed you sweet sis….” Zahrah bata iya cewa komai ba sae hawaye, janye jikinta tayi ta fita daga parlon, a hanya ta hadu da yayanta tana ganinsa xata canxa hanya ya janyota ya rungumeta, rufe fuskarta tayi a kirjinsa, a sanyaye yace “Welcome back Lil sis, ba gudun ki muke ba, it’s just…..” Girgixa kai yayi lokaci daya idonsa ya kada yace “We missed you Zahrah” bata iya ta ce komai ba sai kai da ta gyada masa kawai, yace “Baki je gun bakon da ku ka xo tare ba” goge fuskarta tayi tace “yanxu xan je” saketa yayi yace “Yea ki tafi yanxu, nima daga can nake” gyada masa kai tayi ta nufi bangaren saukan baki inda El-ameen yake, Xaune ta gansa parlor yana waya, ta nemi gefe ta xauna sai kallonsa take, yana gama wayar tayi saurin dauke idonta daga kansa, ya d’an bude ido yace “Good morning princess” d’an murmushi tayi tace “Good morning” yana murmushin shi ma yace “How you!” Ba tare da ta kallesa ba tace “Am good,” yace ‘Happy to be home ryt?” Lumshe ido tayi ta bude ta gyada masa kai, yace “My wife said I shud send her regards” kallonsa tayi tana murmushi tace “Am grateful” yace “In the next 1hr xa mu kama hanyar katsina” da sauri tace “Amma ai da ni xa a je koh?” Yace “No I don’t think so….” Bata fuska tayi tace “Nima nace xan je” dariya yayi yace “Ohk ohk!” Shiru tayi sai kuma tace “Nuna min hoton matar ka” da mamaki ya kalleta yace “Really” bai jira cewarta ba ya dauko wayarsa ya bude ya shiga gallery ya nemo hoton Hafsat ya mika mata, mikewa tayi ta karasa kusa da shi ta karbi wayar ta dawo ta xauna, kallonta kawai take sannan ta kallesa tace “She’s… She’s beautiful!” Murmushi yayi yace “Ohh tnxx” kallon hotunan ta shiga yi, can ta mike da sauri tace “Ohh this is me” mikewa yayi ya koma kusa da ita yana kallon wayar ya ga hoto ne da yayi masu ita da Hafsat, gyada mata kai yayi yace “Yea, ke da Hafsat” a sanyaye ta ci gaba da kallon hotunan taga duk hotunanta ya fi yawa a wayar, ajiye wayar tayi ta koma ta xauna ta lumshe ido, yana kallonta yace “What?” Bude ido tayi ta girgixa masa kai cikin sanyin murya tace “Have you taken breakfast?” Gyada mata kai yayi yace “Yea” bata kuma cewa komai ba can kuma tace “Ban san sunanka ba!” Wara ido yayi yace “I am El-ameen Ahmad…” Gyada kai tayi tace “You have the name of my dad” murmushi yayi yana kallonta, ta mike tace “Xan je gun Abba yanxu” bin ta yayi da kallo har ta fita. Karfe goma saura sarki da tawagarsa suka shirya tsaf domin tafiya kt, shiga ce yayi na alfarma irin ta sarauta, da farko bai amince Zahrah ta bi su ba sbda b’akin dake ta xuwa masarautan dominta amma yayanta na sa baki sarki ya amince su je tare, don har da shi xa’a, rungume yayan nata tayi tace “Thanks bro” Ummanta ta tafi tayi ma sallama sai a sannan Umma ta rungume ‘yar tata ta fashe da kuka, jikin Zahrah yayi sanyi ita ma hawayen ya shiga sakko mata da kyar ta fita daga dakin ta je yi ma step mum dinta sallama, Ummi ta gani ita ma ta shirya tsaf, Ummi na ganinta tace “Zahrah tare xa mu je fah” Kilishi ta kalleta tace “Mai martaba ne yace tare xa ku” bata fuska tayi tace “Yanxu xanje in gaya masa, Mumy bana son ta kara tafiya ita kadai ne….” Kilishi tayi murmushi tace “Toh Allah yasa ya amince” daga haka Ummi ta kama hannun ‘yar uwar tata suka fita, basu sha wahalan shawo kan Abbansu ba ya amince xa ta bi su, motoci biyar ne xa a tafi katsinan da, mai martaba kuma flight xai bi da Zahrah da El-ameen da Ummi, Abdul kuma xae bi tawagar Abbansa ta mota sai su hade a masarautan kano daga can kuma su dau hanyar katsina.
Karfe daya motocin tawagar sarki El-ameen suka iso masarautan Kano, ko minti talatin basu kara a Kano ba suka dau hanyar katsina, Zahrah da Ummi suka shiga mota daya da Mahaifinsu, El-ameen bai yarda ya shiga motar sarki da ya sa masa takwara ba ya hau motar gaba, uku da wani abu suka shiga garin kt, duk da El-ameen ya san ba lallai junaid na gidansu ba, can ya sa suka nufa gaba daya, hudu da minti goma suka iso kofar gidansu Junaid, El-ameen ne ya fara fitowa, sannan dogarawan sarki, kafin sarki ma ya fito tare da aminansa, Sarki na kallon El-ameen yace “Masallaci mafi kusa, xa muyi la’asar!” Masallacin kofar gidan ya shiga da su bayan sun daura alwala, su Zahrah dai na mota a xaune, hudu da minti ashirin duk suka fiffito daga mosque din, Sarki yace “Shiga kayi mana sallama da masu gidan, El-ameen ya shiga compound din, bbu kowa tsakar gidan sai Khadija dake xaune balcony din Mumy, ya karasa har inda take, ta gaishesa da fara’ar yake, amsa kafin yace “junaid fa?” Ta girgixa kai tace “yana can gidansa!” Yace “Abba fah?” Ta kalli bangaren Abba tace “Yana ciki, amma yana da baki” El-ameen yace “Su waye?” Tace “Hajja na ciki, kawu Abbakar ma na ciki sai Abokansa biyu” ya d’an bude ido yace “Meeting din me ake” shiru tayi bata ce komai ba, a hankali yace “Junaid koh?” Gyada masa kai tayi, yace “Su Hajiya fah?” Shiru tayi bata ce komai ba, yace “Mumy fa?” Kallon kofar parlon tayi tace “Tana ciki” yace “Ohk pls ki gaya min taron me ake a parlon” ta tabe baki tace “Humainah ce ta gaya ma Hajja abinda ya sa ya saketa daxu da safe” El-ameen ya d’an bude ido yace “Ta basu labarin mahaukaciya kenan” gyada masa kai Khadija tayi, El-ameen yace “Toh me Abba yace?” Hawaye ya cika idonta taki cewa komai, ya sauke ajiyar xuciya yace “Toh bai xo ba junaid din” hawaye na sakko mata tace “Tun daxu ake kiransa ya ki ya xo” El-ameen bai kuma cewa komai ba ya nufi parlon Mumy, xaune ya ganta da ganinta ba karamin kuka ta ci ba, kasa karasawa yayi cikin parlon ya juya ya fita kawai, kofar gida ya koma ya ba sarki hakuri sannan ya ce su shigo, Fitowa Zahrah tayi da ‘yar uwarta suna daga gefen mahaifinsu suka shiga gidan, har parlon Abba yayi musu iso, tuni Khadija ta mike tana kallon ikon Allah ganin jama’ar dake shigowa gidan, El-ameen ne ya fara shiga parlon da sallama ya gaida Abba da ladabi, Hajja tace “Alhmdllh kun ga babban munafukin abokin nasa nan, ae wllh sai Allah ya mana hisabi da ku….” El-ameen bai ko kalleta ba yana kallon Abba yace “Abba baki kayi daga masarautan Bauchi, mai martaba sarkin bauchi ne da kansa” Abba da ya wani xaro ido tun kan yace komai Sarki El-ameen ya shigo parlon da sallama Aminansa biyu da Zahrah da Ummi ma suka shigo sai Abdul sauran dogarawan sarki suka yi cirko cirko bakin kofa, da farko tsaye sarkin yayi ganin yanda ake kallonsa da mamaki barin Abba ya sa shi samun kujera ya xauna, parking Junaid yayi kofar gida ya tsura ma manyan motocin dake Parke a jere ido, mamaki ne ya cika sa sosai lokaci daya yaji gabansa ya fadi ya bude motar ya fita da sauri ya shiga cikin gidan, uniform ne jikinsa sai hula dake kansa, ko lura da dogarawan da suka cika compound din bai yi ba, shi dai burinsa ya ga Mumynsa, hankalinsa bai gama tashi ba sai da ya ga jerin takalma dake kofar parlon Abba, da part din Mumy xa shi kawai ya fasa ya nufi parlon Abba da sauri ya shiga.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button