CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers Association????
[1/14, 9:12 AM] Elhajj: ⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

40/41

Mikewa Junaid yayi yace “I will think about that!” Daga haka ya nufi kofa El-ameen ya bi sa da kallo har ya fita. A haraban hospital din suka hadu da faisal, faisal yace “Ohh my God, ashe abinda ya faru kenan captain shine ko ku sanar da ni kai da El-ameen? da Childishness din ku ne ya tashi da har gida xa ku xo ku sameni” junaid yayi murmushi yace “I thought ka sani ne ai,” faisal yayi tsaki yace “Ta ina xan sani?” Daga haka ya bar sa nan tsaye ya shiga asibitin, murmushi junaid ya kuma yi ya shiga mota ya bar asibitin. Yana isa gida part dinsa ya tafi yayi alwala yayi sllhn asr sannan ya kwanta parlor, har ya fara bacci yaji an bude kofar parlon, bude ido yayi ya mike xaune da sauri, Humainah ce ta shigo parlon ta tsaya daga bakin kofa ta d’an hade rai tace “Xamu tafi tare da Hajja!” Yana kallonta yace “Ina xa ku” tace “Gidanmu!” Shiru yayi kafin yace “Ohk, yaushe xa ki dawo?” Ta tabe baki tace “Baxan sake dawowa ba, da kayana duka xan tafi ma” murmushi Junaid yayi yace “Ohk Allah raka taki gona” tace “Ameen” daga haka ta juya ta fice daga parlon, ya koma ya kwanta. Tana fita hajja ta shigo sabe da gyalenta da ‘yar jakar da ta taho da shi, tace “Toh Amadi ni dai xan tafi sai kuma na dawo kai maka amarya ko kaki ko ka so sai in ga ta tsiya, idan har ynxu ra’ayin rayuwa da mahaukaciya kake to sai ka haukatar da warce za a kai maka hakan xai fi maka rufin asiri” daga haka ta juya ta fita ya bi ta da kallo hade da tabe baki, ranan da daddare Ummin El-ameen ta xo gidan, duk yanda ta so ya gaya mata ko El-ameen yasan komai kan xancen yarinya mahaukaciya kin gaya mata yayi yace babu ruwan El-ameen, ba don ta yarda ba ta kyalesa don tasan bakinsu daya, can tace “Na ji labarin aure xa ayi maka, saura abokin ka, shi wannan kauye ma xanje dauko masa mata wallahi xan basa mamaki,” Dariya Junaid yayi yace “Kai Ummi, kauye kuma” bata tanka sa ba ta mike ta fice daga parlon. Shirye shiryen biki aka dinga yi gidansu Ahmad Junaid babu kama kafar yaro, cikin kankanin lokaci aka hada lefe akwati shidda, shi dai Junaid kallon ikon Allah kawai yake wai shi xa ayi ma aure, auren ma na dole kamar wani mace kuma har lokacin bai san matar ba dariya ma kawai abun ke basa, ana saura sati bikin ya dawo aiki da yamma yana kwance sai dai gaba daya tunaninsa na gun Jasmine yana son sanin halin da take ciki yana kuma son ganinta, kiran El-ameen ne ya shigo wayarsa ya daga, daga daya bangaren El-ameen yace “Uhm duk xumudin xama angon ne yasa ka mance da patient dinka captain?” Junaid yace “If that’s what you are thinking….” El-ameen yace “Toh yayi kyau, amma idan baka manta the very first day da ka fara xuwa min da batun ta sai da na baka shawarar ka raba kanka ka ki, yanxu ka xo kayi abinda ya dame ka, ka bar ni da ‘yar mutane, ko irin ka dinga kira ka tambayi lafiyarta babu, to Dr sumayya dai ina a week time xa su yi tafiya da mai gidanta wai…” Junaid yace “Yea! Then an min auren sai ta dawo gidana kamar yanda ka ce” El-ameen ya tabe baki ya katse wayar. Karfe biyar da wani abu Junaid ya shirya ya tafi part din Mumy yace mata xai dan fita, sabuwar motar da Abba ya basa ya dauka ya fita daga gidan, a hanya ya kira El-ameen, yana dagawa yace “Kana ina?” El-ameen yace “Me xan maka?” Tsaki Junaid yayi yace “Dalla ni ka gaya min” katse wayar El-ameen yayi, junaid yayi parking ya ji kamar ya juya, sai dai baxai iya ba sbda son ganin jasmine da yake, sake kiransa yayi yana dagawa yace “How dare you xaka katse min waya daga tambaya” El-ameen yace “Ashe ba dadi kai kake ma mutane, ni da ma kai ka haukacen wllh kayi loosing memory ko xaka rabu da wnn worst attitude din naka, gashi it’s getting worst nowadayz, ni ina gida anything?” Katse wayar junaid yayi hade da yin kwafa, ya kusa minti goma xaune motar ya kuma yin wani kwafan ya ja motar ya nufi gidan nasu, Ummi dake parlor ya gaida tace “Ni ban ga kai da abokin naka kuna shirin bikin nan ba Ahmad” junaid yayi yake yana shafa kai yace “Ae abinda ya kawo ni kenan” Ummi tace “Toh yayi kyau, da an gama naka da sati biyu in an huta xan kai nasa lefen kauye” Junaid ya fashe da dariya yace “Wllh xan maki driving din” Ummi ta hade rai tace “Am serious, dan ma ka gaya masa nake gaya maka” dakin El-ameen ya nufa yana dariya, El-ameen ya tura laptop din gabansa yace “What is making him laugh” Junaid ya buda ido yace “Baka ji a bakin Captain ba, yanzu dai tashi ka kai ni in duba yarinyar nan tunda gori ka min daxu” El-ameen yace “As you can see am busy, sai dai in baka address” junaid yace “Ba fa dadewa xa mu yi ba” “yess! ko minti daya xa muyi” cewar El-ameen yana kallonsa da kyau. Junaid ya kusa minti goma tsaye yana kallonsa kafin ya juya ya fita daga dakin, El-ameen yace “Byee!” Da daddare yana kwance bedroom Humainah ta fado masa, tabe baki yayi ya dauki wayarsa ya shiga kiranta, sai da ya kusa katsewa ta daga yace “don ma kin samu na kira ki” tace “I didn’t beg for ur call” shiru yayi sannan yayi murmushi yace “True! Yaushe xa ki dawo?” Tace “Ana saura kwana biyu bikin ka xamu dawo da Hajja” yace “Bikinsu dai” daga haka ya katse wayar, Har ya ajiye wayar ya tuna Hafsat, tun ranan da abun ya faru bata kira ba bai kirata ba, numberta ya duba ya shiga kiranta bugu uku ta daga ya mata sallama ta amsa daga daya side din hade da gaishesa, ya ce “Ya kike?” Tace “Qlau” rasa me xai sake ce mata yayi, can dai yace “Am sorry for what happened Hafsat,” tace “Ohh ba komai, ya wuce ai” yace “To nagode” tace “welcome! But a ina ka san yarinyar?” D’an shiru yayi kafin yace “It’s a long story” tace “really?” Yace “Yeah!” Labarin yanda ya fara ganin jasmine tun daga rana ta farko ya fara bata har xuwa ranan da ya kai ta gida gun parent dinsa da abinda ya faru bayan barinsu gida, Hafsat da duk jikinta yayi sanyi tace “Yanxu kana nufin ta dawo hankalinta?” Yace “Yea, amma tayi loosing memory” Cike da damuwa Hafsat tace “Allah sarki, to yanxu tana ina?” Ya lumshe ido ya bude yace “Tana gun frnd dina, buh am getting married in a week time sai ta dawo gidana har tayi regaining memory, Hafsat tace “Dat’s nyc Allah ya sanya alkhairi, ya bada xaman lafiya,” Yace “Ameen thank you” shiru tayi ya kalli agogo ya ga har sha daya ya wuce, yace “Xa ki kwanta koh?” Tace “Yeah” yace “Ohk good nyt, tnx a lot ki gaida mutan gida” tace “Ayt bye!” Daga haka ya katse wayar ya ajiye yayi addu’an kwanciya. Washegari da yamma junaid na kwance bayan ya dawo daga aiki El-ameen ya shigo parlon, kallo daya ya masa ya dauke kai, El-ameen na daga tsaye bakin kofa yace “In ka shirya ka taso mu tafi” ko kallonsa junaid bai yi ba, El-ameen yace “Ohk nayi tafiya ta” daga haka ya fice. Junaid ya mike ya shiga bedroom ya daura shirt dinsa ya dau Atm ya fita, a part din Mumy ya tarda El-ameen, ya jira har ya gama surutun sa snn yace “Mumy xa mu d’an fita yanxu mu dawo” Mumy tace “Toh Allah ya tsare” ya juya ya fita. A mota yayi ta jiran El-ameen har sai da yaga dama ya fito, El-ameen ya xaga daya side din ganin junaid a driver seat yana shiga junaid ya tada motar suka bar layin, tun a hanya El-ameen ya kira Dr sumayya ya sanar da ita xuwansu, a visitor parlor suka sauka dotan Dr Sumayya ‘yar shekara sha uku ce ta kawo masu ruwa da drink ta xauna kusa da El-ameen tana ta basa labari, junaid dai makala earpiece yayi yana danna waya, bayan kusan minti biyar Dr Sumayya ta shigo parlon suka gaisa da El-ameen, El-ameen ya fixge wayar sai a sannan ya dago yana kallon Dr Sumayya yace “Ina yini!” Tace “Lafiya lau ya aiki,” yace “Alhmdllh,” mikewa tayi ta fita tana fita sistern ta warce xata yi mate din jasmine ta shigo parlon tare da jasmine din, xama tayi kan kujera ta nuna ma Jasmine gefenta ta xauna sannan ta gaida su El-ameen, ya amsa mata da murmushi yace “Ya sch?” Tace “Alhmdllh” kallon jasmine tayi tace “Baby baki ce masu ina yini ba” sunan da Dr Sumayya ke kiranta da shi kenan a sati daya da ‘yan kwanakin da tayi a gidan, shine duk yan gidan ke kiranta da haka, shima El-Ameen dake yawan xuwa gidan sai ya dinga kiranta da haka, jasmine ta kalli farida sannan ta kalli El-ameen a hankali tace “Ina yini?” Murmushi kawai yayi mata ta sunkuyar da kai, Junaid dai sai kallonta yake ta gefen ido, El-ameen yace “Toh baki gaida wannan ba Baby” Ya fadi hakan yana nuna mata Junaid, kallonsa tayi tace “Ina yini?” Ya dago kai shi ma yana kallonta yace “Lafiya lau” daga haka ta sunkuyar da kai, El-ameen yace “Baby dawo ki xauna nan ki gaya min abubuwan da Farida ta koya maki yau” mikewa tayi ta dawo kusa da shi ta xauna kasa, Junaid ya kalli agogon wrist dinsa sannan ya ci gaba da danna wayarsa, El-ameen yace “Gaya min mana” dago kai tayi ta kallesa cikin sanyayyan muryarta tace “tace min girki ne abinda muka yi” dariya yayi yace “Da gaske, to me ku ka girka?” Ta kalli farida tace “Ya ma?” Dariya farida tayi tace “A’a tuna dai” shiru tayi kamar me naxarin sunan girkin, da sauri farida tace “Ohkk okk fried rice ne da coconut drink muka yi baby” tayi hakan ne don yanxun nan sai ta iya rike kai ta fara ihu hakan kuma zai ja Dr Sumayya ta bata mata rai, shi kansa El-ameen ya san in dai tayi stressing brain dinta wajen son tuno abu nan da nan kan xai fara mata ciwo, kuma yana daukan lokaci bai daina ba. Jasmine ta kallesa tace “Fried rice and coconut drink Mumy tace mu yi” yayi murmushi yace “Good kuma kin iya yanxu?” Girgixa masa kai tayi alamar A’a, zai yi magana junaid ya mike yace “Toh ni xan koma” El-ameen yace “ohK bani makullin motata” hade rai yayi yace “Xan yi amfani da shi ne” El-ameen ya mike ya warce makullin ya koma ya xauna, juyawa junaid yayi ya fice daga parlon. Da daddare yana kallon wani program khadija ta shigo parlon da sallama ta ajiye masa mug din hannunta, yana kallonta yace “Meye wannan?” Tace “Lipton mana” yace “Wa yace ki kawo min?” Tace “Ance kace wai in maka” yace “Ohk tnx” mikewa tayi ta fita, ya girgixa kai ya ci gaba da kallonsa, bayan kusan minti talatin yaji kamar motsi a balcony, mikewa yayi ya kashe wutan parlon ya rage na tv kadai ya dawo ya xauna, a hankali aka murda kofar parlon, ya jinginar da kansa jikin kujera idonsa na kan tv, Suhaima ce ta shigo parlon da hijab dinta har kasa, ta tsaya daga bakin kofar tana lekosa, shi dai bai juyo ba har lokacin, cikin sassarfa ta karaso cikin parlon ta na kallonsa tace “Ya Ahmad?” Bai tanka ta ba hakan yasa ta d’an yi murmushi ta xauna kusa da shi tace “Amm dama….” Mikewa yayi yana kallonta fuskar nan nasa kamar bai taba dariya ba yace “me ya shigo da ke nan?” Gabanta yayi mugun faduwa ta mike tace “Oh dama…” Juyawa tayi da sauri zata bar wajen ya fixgota, ya sauke mata wani mari me lafiya cikin tsawa yace “Nace me ya kawo ki nan” jikinta ya dau rawa tace “Wayyo kudi xa ka ban” wani marin da ya gigitata ya kuma kai mata, ya ja ta ya nufi daki da ita, kuka ta dinga yi a tsorace tana cewa “Kudi wllh na xo karba” belt ya dauka ta fasa ihu a rikice tana kiran Hajiyarsu, ya ja ta suka fito parlor ya xabga mata a jiki, wanda hakan sai da ya kusa sa ta sakin fitsari, dukanta yake kamar an aikosa, ta dinga ihu iya karfinta tana kiran Hajiya da Umma, Dama suna labe balcony, Hajiya ta saki murmushi haka ma Umma a tare suka ce “Alhmdllh” duk suka sauko compound din, sosai suke jin ihun Suhaima, Hajiya ta saki salati da karfi tana kwala ma suhaimar kira tana cewa “ina kike, me ya same ki” Umma ma ta dinga kwalo mata kira duk suka cika tsakar gidan da hayani, su khadija ne suka fara fiffitowa sannan fatima, Hajiya tuni ta nufi part din junaid har lokacin tana kwalo ma Suhaima kira, Abba ne ya fito shi ma jin hayaniya, Ya kalli Umma yace “Meye haka?” Umma tace “Yo ina muka sani Alhaji, ihunta kawai muke ta ji mun rasa inda take” Fitowa Mumy ma tayi jin abinda Umma tace, Tuni Hajiya ta isa kofar junaid ta shiga bubbuga kofar tana kiran Suhaima, bude kofar junaid yayi bayan ya lallasata iya son ransa da belt ya cillota waje ya kulle kofarsa, birgima ta dinga yi tana cewa “Wayyo Hajiyarmu bai sha ba” Hajiya da idanuwanta suka firfito ta dagota da sauri ta toshe bakinta a jikinta tace “Ba kya ji Suhaima kin tsokanesa kenan koh?” Abba ne ya karaso yana kallonsu yace “Meke faruwa ne wai?” Da sauri Hajiya tace “A’a ita ce bata ji Alhaji fitsara tayi masa daxu, mu je kawai maganinta kenan” Abba ya kwalo ma junaid kira Hajiya da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta tace “oh Alhaji don ya hukuntata shine wani abu, bata dawowa da wuri ne daga makaranta yayi mata magana tayi masa fitsara shine ya xaneta, ai ni ya min dai dai, mu je kawai Alhaji” Mumy ce ta karaso wajen Hajiya tace “Ohh Amina ku rabu da yaron nan, don ya doketa ya hukuntata shine me… Yanxu da fatima ce ai baxa ki ce komai ba” juyawa kawai Mumy tayi ta bar wajen, Abba ya girgixa kai shima ya koma part dinsa, Sumsum Hajiya ta ja Suhaima da ke kuka tana soshe soshen suka bar wajen, Umma ta hadiye yawu da kyar ita ma tayi part dinta. Wasa wasa har biki ya rage kwana biyu, banda shirye shirye babu abinda ake a gidan kamar irin shi ya zabi matar din nan, tuni ‘yan uwa da abokan arxiki aka fara xuwa daga garurruwa daban daban, sai a lokacin Junaid abun ya fara damunsa on like before da lamarin ke basa dariya, babban damuwar tasa rashin sanin wacece iyayen sa suka xaba masa, babu yanda bai yi da Mumy ta gaya masa ba ita ma tace bata sani ba, Tashin hankali gun Umma da Hajiya baya faduwa don sun rasa abun yi, komai suka yi ba nasara ciki gashi basu san wacece shegiyar da xa a aura masa ba don basu ga alamar daya daga ‘ya yansu bane, da yammacin ranan Hajja ta diro gidan, magiya junaid ya dinga mata kan ta gaya masa wacece matar tasa tace ubansa yayi kadan balle shi, sosai hankalinsa ya tashi, bayan magrib Abba yasa a kira sa, yana shiga parlon ya xauna Abba yace “Babu wani shirin da za kuyi ku, ko walima ne?” Ya gigixa kai yace “A’a Abba, walimar da xa ayi a nan gida ya isa” Abba yace “Toh shkkn, hakan it’s Ohk” ranan kasa bacci junaid yayi har kusan karfe dayan dare, wayarsa ya jawo daga karshe ya shiga neman number Humainah don yasan baxa ta rasa sanin matar ba, har ya gama ringing bata daga ba ya sake kiranta sai gashi ta dauka, cikin sanyin murya yace “Kina ji na Humainah” “Um” kawai tace masa kamar anyi forcing dinta, ya lumshe ido ya bude yace “Plss nasan baxa ki rasa sanin warce xa a aura min ba, ki gaya min wacece plss” taki cewa komai na kusan second talatin har sai da yace “Hello” sannan tace “Ban sani ba nima” yace “Plss” kamar xata yi kuka tace “Ban sani ba,” tsaki yayi ya katse wayar ya jefar. Washegari alhamis da asuba yayi shirin fita aiki ya fice ya bar masu gidan, haka ya wuni bai da sukuni ranar, yana barin gun aiki Clinic ya tafi gun El-ameen, da damuwa yace “Frnd har yanxu fa ban san wacece matar nn ba” El-ameen yayi murmushi yace “gobe idan mun kai ka xaka ganta, sbda son da Abba yake maka shi yasa yake son surprising naka” Junaid yace “Plss ka daina bata min rai more, what sort of surprise is this, and what if fitinanniya ce taki yarda da xaman yarinyar a gidan?” El-ameen ya hade rai yace “Sai ka korata nasu gidan don bata xo maka da gida ba, and tana tarewa gobe ita kuma xata tare ran lahadi don ranan Dr Sumayya xa su yi tafiya, tsaf ita ma kuma xa a gyara mata nata dakin” Junaid ya dafe kai yace “Ba haka ba frnd, kasan tana iya xuwa tayi reporting ma su Abba fa” El-ameen yace “Shit, gashi har xa a maka aure gobe baka xama mature person ba, ka ki girma har yanxu junaid, look yanxu you are going to leave a free…. When I say free I mean a free life, no more Mumy Mumy Mumy, you are going to head a family of ur own don haka ko wani decision kayi a gidan ka is right ba sai wanda parent dinka suka maka ba, from tomorrow you will be on ur own” junaid yace “Uhum?” Tsaki El-ameen yayi, can yayi kwafa yace “da rabon matar nan ta rainaka idan ta lura you don’t have a say of ur own!” Mikewa Junaid yayi yace “Baka san ni ba kenan” daga haka ya fice daga office din.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button