CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske writers association????⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

87___88

Durkushe ya ganta a dakin tana kuka, tana ganinsa ta hadiye kukan ta hade rai sosai, hade rai shi ma yayi yace “Did you just say something?” Mikewa tayi tana masa wani kallo tace “We the royal blood don’t say things twice….” Dariya sosai ta basa, sai dai ya dake bai yi ba ya Karasa gabanta yana kallonta, ko dar bata nuna ba duk da a tsorace take ganin yanda fuskarsa ke a daure, wani murmushi yyi yace “Mind you gidan Capt Ahmad ne nn ba so called royal home din ku ba” tabe baki tayi ta juya masa baya tace “I don’t care where I am, I Still remain who I am…” kallonta ya shiga yi daga sama har kasa can ya gyada kai yana murmushi ya juya ya fita. Da rana El-ameen ya xo gidan, suna xaune parlor da Junaid ganin bai ga Zahrah ba sai Humainah dake kitchen, yace “Captain rowar ganin amaryar ake min” Junaid ya mike yace “Noo Not at all…” Daga haka ya haura sama ya tura kofar bedroom dinta, xaune ya sameta tana ganinsa tayi saurin goge hawayen fuskarta ta dauke kai, daga nn bakin kofa yace “ki fito ku gaisa da El-ameen…. Miss Royal being” wani kallo ta masa sai kuma ta mike ta dau hijab ta saka tayi ficewarta daga dakin ta bar sa tsaye, da murmushi fuskarta suka gaisa da El-ameen sai dai bata yrda sun hada ido ba, El-ameen na ganinta yasan kuka tayi, kallon Junaid da ya tsiri danna waya yyi sai dai bai ce komai ba, ita kuma ta mike, da har xata koma sama sai kuma ta nufi kitchen, Humainah dake hada stew ta kalleta ta dauke kai ta dalilin faduwa da gabanta yayi, Zahrah ta dake tace “Sannu da aiki” Humainah tace “Yauwa, thanks” kallon kayan lambun dake ajiye kitchen din Zahrah tayi ta karasa ta dauka ta nufi washing basin ta shiga wanke su, ita dai Humainah bata ce komai ba sai satan kallonta take, har ta gama wanke su ta dauki chopping board da wuka ta shiga yankasu, bayan kusan minti goma Zahrah tace “Ki ara min wayar ki” Humainah tace “Yana daki” har suka gama aikin bbu wanda ya sake cewa komai, ko da Zahrah ta dawo parlor bata ga El-ameen ba alamar ya wuce, sama ta nufa Junaid ya bi ta da kallo don yyi mamakin kitchen da ta shiga, can Humainah ma ta fito ta nufi sama ita ma ya bi ta da ido can ya mike ya bi bayanta, Zahrah na haura wa sama dakin da tasan na Humainah ne ta bude ta shiga, can kan gado ta ga wayar ta dauka ta xauna gefen gado, Humainah ta shigo dakin, sosai tayi mamakin ganinta xaune dakin, bata ce komai ba ta tafi gaban mirror, Bude kofar aka yi Junaid ma ya shigo, still yyi bakin kofa yana kallon Zahrah, kallo daya tayi masa ta dauke kai, ta mika ma Humainah wayar tace “bude min pattern” Humainah ta karba Junaid ya fixge wayar hannunta yana kallon Zahrah yace “Wa xa ki kira?” Ba tare da ta damu ba tace “Abbana” juyawa yayi ya fice da wayar, tabe baki tayi ta kalli Humainah ta mike ta nufi kofa, Humainah ta bi ta da kallo har ta fita ta juyo tace “Idan kin xuba abinci ki kira ni, we don’t eat alone at home” daga haka ta fita, mamakinta sosai Humainah ta dinga yi, tana xuba abincin kuwa ta dawo sama ta bude kofar dakinta ta kirata, mikewa Zahrah tayi ta fito suka sauka kasa a tare, nan kan carpet Humainah ta ajiye masu abincin, Zahrah ta xauna ta tankwashe kafa ta dau spoon ta fara cin abincin, xaunawa Humainah tayi ita ma ta dau cokalin ba tare da ta kalleta ba ta shiga cin abincin, Zahrah ta d’an kalleta tace “How month pregnant are you?” Kallon mamaki Humainah tayi mata da kmr baxata tanka ta ba sai kuma tace “five” Zahrah ta langwabar da Kai tace “Ohk…. But me yasa mijin ki yake behaving yanda yake yi?” Humainah bata kalleta ba bare ta sa ran amsa, aka bude kofar parlorn Junaid ya shigo don dama yana waje, kallon mamaki yake masu can ya karaso parlon ya xauna yana kallon Humainah yace “Did you cook with me” kan tace komai Zahrah ta amshe tace “Of course No, not with her condition, just go get something outside to take!” Kallon Zahrah kawai yake can ya mike ya nufi stairs sai a snn yayi murmushi ya haura sama. Da daddare Zahrah na fitowa daga wanka ta xauna gaban mirror don yi shafe shafenta aka bude kofar dakin, duk da ynda gabanta ya fadi hakan bai sa ta juyo ba sai shafa lotion dinta take, tsaye yyi bakin kofar yana kallonta, ta gama shafanta ta mike ta nufi kan gado don daukar sleeping wear dinta, bin ta yyi da ido har ta dau kayan, ganin cire towel din xata yi yasa shi juyawa ya fice daga dakin ya rufo, murmushi tayi a xuciyarta tace you should have stay, tana gama shirya wa ta fito ta shiga dakin Humainah, Humainah dake kwance don ta gaji bayan dinner da ta girka ta bi ta da kallo, kwata kwata ta ki sakewa da ita, Zahrah ta xauna kan gadon ta dau remote tace “I hate staying alone… We don’t do that at home” powering din Tv tayi ita dai Humainah bata ce mata komai ba. Daga karshe rufe ido ma tayi kmr ta fara bacci, xaman kusan minti talatin Zahrah tayi can tayi kwanciyarta kan gadon, bude ido Humainah tayi da sauri tana kallonta, ta gyada kai tace “Yeah, I am spending the nyt here” Humainah bata ce komai ba ta rufe idonta kuma, Zahrah ta gyara kwanciyarta ta ja duvet ta ci gaba da kallonta, bude kofar dakin aka yi Junaid ya shigo, ya buda ido yana kallon Zahrah, ko kallonsa bata yi ba idonta na kan tv, Humainah dai tayi kmr bacci take, juyawa yyi kawai ya fita daga dakin. Washegari da asuba Humainah ce ta fara tashi ta tada ta, sllh tayi ta fita ta bar ta dakin ta tafi kitchen, tana fita Junaid ya shigo, ya hade rai yana kallon Zahrah da ke kan darduma yace “Me ya shigo dake dakin matata, don ki koya mata girman Kai da unnecessary Royalism din ki koh?” Bata ko kallesa ba bare ya sa ran samun amsa, sosai hakan ya kona masa rai ya daka mata tsawa yace “Ba magana nake maki ba kika kyaleni” nn ma dai ko kallon gefen da yake bata yi ba, juyawa yyi ya fice daga dakin xuciyarsa na tafasa, sai a snn ta kalli bakin kofar ta gefen ido ta mike, ita ma ta fita ta shiga bedroom dinta tayi wanka ta shirya cikin wani lace mara nauyi da ya amsheta sosai, gyara dogon gashinta tayi ta daure a baya ta bar dankwalin a kafada ta sauka, ba wani aiki ta taya Humainah ba sai tambayoyi da ta isheta da shi kmr yar jarida, Humainah ta jera komai kan dining Zahrah ta xauna tana kkrin daukan cup tace “Yanxu sai ki je kiyi wanka kiyi kwalliya wa mijin ki…” Humainah bata ko kalleta ba ta wuce sama, tana tafiya sai ga junaid ya sauko cikin shirin Uniform, har ya karaso dining din idonsa na kanta, shayin ta kawai take sha, ya ja kujera ya xauna ya hade rai yace “A royal Home din ku ba’a koya maki gaisuwa ba ne koh” bata dago kai ba bare ta tanka sa sosai haka ya kona masa rai, sai a snn yasan ashe shariya na da ciwo, wani tsawa ya mata yace “Kee!” Dago manyan idonta tayi ta hade rai tana kallonsa can ta mike ta kwabar da cup din tean hannunta ta nufi sama kmr xata tashi sama, bin ta da kallo yyi baki bude, tunda yake shi mace bata taba yi masa haka ba, fasa breakfast din ma yyi gaba daya ya koma sama ya dau wayarsa da car key ya bar gidan. Sai wajen biyar ya dawo gida har lokacin ransa ba dadi, xaune suke parlor tana gyara Humainah gashi, ya wani hade rai yace “Duk ku bar parlon nn Immediately” ba tare da Zahrah ta kallesa ba tana ci gaba da combing gashin Humainah tace “And may we know y?” Karasawa parlon yyi cikin tsawa yace “ku bar min parlor nace” Zahrah ta yatsine fuska ta kwashi kayan gyaran gashin tace “it doesn’t call for shouting! Maman baby tashi mu je” Humainah ta tabe baki ta tafi sama, Zahrah ta bi bayanta, xaunawa yyi kan kujera yana tunanin hukuncin da xai dauka kan Zahrah bai taba tunanin shariya da daukan kai na da ciwo ba sai ynxu, ranan ma tare Zahrah ta kwana da Humainah, shi dai bai ce masu komai ba, washegari ya gama shirin fita aiki ya sauko downstairs ya samesu tare suna breakfast, yana kallon Zahrah yace “Royal being, har yanxu bayin na ki basu iso bane ko dama kawai fadi aka yi” ko kallon inda yake bata yi bare ta tanka sai cin potatoe da ketchup dinta take, tsaye yyi yana kallonta, can yace “I can see you are deaf…” mikewa tayi irin ya takurata din nn a fusace ta yi hanyar stairs, bin ta yyi ya fixgota ya hadata da jikinsa kan yace komai cike da tsiwa tace “Me yasa ka fiye takura ne Mr man, get away from my life, i hate disturbance, I don’t want….” Bai bari ta kai karshe ba sai jin kiss tayi, Humainah dake kallonsu dama dauke kai tayi ta ci gaba da jujjuya potatoe din gabanta, turata yayi yana mata wani kallo sai kuma ya juya ya nufi kofa da sauri, bin sa da kallo tayi a tsorace, can ta saci kallon Humainah sai kuma ta tafi sama da sauri, Junaid ya kusa minti goma xaune cikin motar kafin ya tada motar ya bar gidan. Har rana Zahrah bata fito ba, wajajen Karfe uku ganin ta fara jin yunwa ta fito daga dakin, bbu kowa parlon ta shiga kitchen ta hada tea ta fito ta dawo sama dai dai lokacin da Humainah ta fito daga dakinta, har Zahrah xata mata magana sai taga ta wani hade rai kmr bata ganta ba ta sauka kasa, Zahrah ta juya ido hade da tabe baki ta shige dakin ta. Da yamma kusan a tare Junaid ya shigo gidan da Hajja, ya wani hade rai ganinta, ita din ma ko amsa gaisuwarsa bata yi ba ta shige parlor tana kwala ma Humainah kira, Humainah dake kwance daki ta fito da sauri jin muryar Hajja, rungumeta tayi cike da jin ddin ganinta, Hajja ta turata tana kallonta daga sama har kasa tace “Ramar meye wnn Humainah, daina baki abinci yyi don yyi aure ko yaya?” Humainah tayi ‘yar dariya tace “Ni ba Ramar da nayi Hajja” Hajja ta kalli sama murya can kasa tace “Yar sarkin na sama koh?” Humainah ta gyada mata kai kawai, Hajja ta tabe baki tace “Xata ci ubanta, ko da kuwa shugaban kasa ne uban nata….” Shigowar Junaid ya sa tayi shiru ta balla masa harara, dai dai lokacin da Zahrah ta sauko jin muryar Hajja, hajja ta tsuke fuska sosai, daga inda take tsaye ta gaida ta Hajja ta saki salati tana tafe hannu tace “Yanxu ‘yar nn kya gaida Uwar da ta haifi uwar ki a tsaye?” Kallonta kawae Zahrah take, Hajja tace “Toh wnn ba dab’iar arxiki bane, don da Humainah ce ko kaffara baxan yi ba baxa ta yi haka ba, ba fa masarauta kike ba yanxu!” Wani kallo junaid yake ma Hajja don ji yyi kmr ya shaketa, Zahrah ta juya ta koma sama, bin bayanta yayi Hajja tace “Munafuki, hbayaala har ta fara girki ta basa yaci ne?” Humainah dai bata ce komai ba Hajja ta ce “Toh shi ma xae ci uban nasa ne” tsaye Junaid ya ganta gaban mirror, da kmr baxae karasa ba sai kuma ya karasa kusa datace ita, juyo da ita yyi yana kallonta yace “Me yasa kika gaisheta a tsaye!” Bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, tambayar ya kuma maimaitawa nn ma dai shiru kke ji, a fusace yace “Don me xan dinga maki magana kina share ni” ga mamakinsa har lkcn bata kalli inda yake ba, ya fixgota yace “Wllh na sake maki magana kika share ni I will…” kallon mamaki yake mata ganin bama ta da niyar kallonsa, can ya juya fita. Har dare Hajja bata bar gidan ba tana dakin Humainah, Junaid ya samu Humainah dake kitchen tana xuba ma Hajja abinci yace “Zahrah ta ci abincin?” Bata kallesa ba tace “I don’t know!” Ficewa yayi daga kitchen din ya koma sama ya shiga dakinta, xaune ya sameta ya karasa kusa da ita yana kallonta kana ganinta kasan tayi kuka, bai san lokacin da ya durkusa gabanta ba ya kamo hannunta yace “Zahrah!” Kallonsa tayi bata ce komai ba, ya matsa hannunta a hankali, sauke idonta tayi kasa, can underneath his breathe yace “My arrogant princess!” Bata dago ba bare tace komai ba, ya lumshe ido ya bude a hankali yace “Meye amfanin miskilanci da girman kai Jasmine!”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button