CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????

Haske Writers Association????
Captain_Ahmad Junaid

    _By Khaleesat Haiydar_✍????

12…..

Gidansu faisal Junaid ya nufa, yana gama parkin ya nufi babban palon gidan, babu kowa palon sae TV dake aiki ya shiga dakin faisal, kwance ya samu faisal yana waya, Junaid ya tabe baki ganin yanda yake wani kwantar da murya ko ba a fadi ba yasan da mace yake wayar, can karshen gadon Junaid ya xauna, faisal ya mike xaune yace “Babe xan kira ki ltr,” daga haka ya ajiye wayar yana kallon Junaid yace “Uhn! B’atan hanya kayi captain?” Junaid yace “No!” Faisal yayi dariya yace “A’a kae dai fadi gskya, ko wajen El-Ameen xaka yi ka mance ka yo nan” Junaid yace “What ever, Mama fa?” Faisal yace “Tana kano jiya ta tafi” Junaid yace “Allah dawo da ita lfya, kana ta shagalin ka da ‘yan mata abin ka” faisal yayi dariya ya dawo kusa da shi yace “Kai aure ma ni xanyi fa yanxu” junaid ya kallesa yace “da gaske?” Faisal yyi kwafa yace “Stay there kai da El-Ameen kuna hauka sae kun ji ma an sa min rana soon” murda kofar dakin aka yi duk suka juya suna kallon kofar El-Ameen ya shigo, faisal ya d’an bude ido yace “Show! Ko dai tare ku ke?” El-Ameen dake ta kallon Junaid yayi murmushi ya karaso cikin dakin yace “Ashe nan ka yo captain, toh what’s the meaning of going without saying a gud bye, dama daga nan gidan ku xan tafi ban mance Irish dina ba wllh tunda yunwarsa nake” Junaid bae ce masa komae ba ya fiddo wayarsa yana dannawa, El-Ameen ya xauna gefen faisal ya dafa kafadarsa daya yace “Ya aka yi guy, ya aiki?” Faisal yace “Alhmdllh mun gode Allah, muna week end yau, ya su Ummi?” El-Ameen yace “Duk lfya, plss in tambaye ka mana” Faisal yace “Ina jin ka” El-ameen na shafa kai yace “wannan abokin naka psychiatrist, I can’t recall his name yanxu, yana nan katsina har yanxu kuwa?” Faisal yace “Wai Dr isah?” El-Ameen yace “Exactly, yana nan?” Faisal yyi dariya yace yace “Yana nan, Ashe baka mance shi ba, ko jiya muna tare da shi” El-Ameen yace “Yauwa plss wani taimako nake son ka min, Gamma knife or Cyber knife xaka tambayar min a gurinsa nasan baxae rasa ba” faisal ya gyara xama yana kallonsa yace “Me xaka yi da gamma knife kuma, naga baka concentrating a field dinka na neurology yanxu” El-Ameen ya sauke ajiyar xuciya yace “ina yi mana, sosai ma, yanxun ma wani frnd dina ne ke da wata patient with mental disorder, so am putting her under medication ne yanxu, after some month idan naga ba a dace ba, I will advise him to take her to a psychiatry for psychiatrist to take over, kila a dace a can din” El-Ameen na magana ne yana kallon Junaid fuskarsa dauke da murmushin rainin hankali, junaid dae ko kallonsa bae yi ba sai danna wayarsa yake, Faisal yace “Allah sarki, xa ma a dace idan Allah ya yarda, sae dai idan ba Neurologist El-Ameen din da na sani bane,” dariya El-Ameen yayi yace “Noo, Dr El-Ameen dai, yanxu dai plss xuwa gobe ka lallaba sa ko na clinic ne ya aro min, coz nasan frnd din nawa will not afford it idan nace yaje can kasashen turai ya siya, its more than expensive” ya kare maganar yana ma Junaid wani irin kallo yana murmushi, Murmushi junaid yayi ba tare da ya kallesa ba, faisal yace “Alryt xan kirasa anjima, amma a ina xaka sa ta under medication din, clinic din ku?” El-ameen ya xaro ido yace “Sai in ce ma Abba a ina na samota?” Da mamaki Faisal yace “Kamar ya, ‘yan uwanta fa?” El-Ameen yayi dariya yace “Ohh ai d’an uwanta a dai yanxu daya ne kacal a duniyar nan” kallonsa kawai Faisal ke yi da confusion shi ko sai dariya yake, Junaid ya tabe baki ya mike ya nufi bathroom ya dauro alwala ya fito don lkcn sllh yayi, bae jira su ba ya fice daga dakin don xuwa masallaci, Faisal ya bi sa da kallo yayi dariya yace “Kai halin Junaid sae shi, toh meye ma’anar hakan da yake yi, namiji dan uwansa ma sai ya ma miskilanci ina ga mace” El-Ameen yayi dariya yace “Let him, I think yana d’an da brain disorder’n shi ma, of recent na lura da hakan, kaga sae in hada shi da patient din tawa in sa su under medication” dariya sosai faisal yayi, El-Ameen yace “Amma fa rufa min asiri kar ka gaya masa sae ya Iya daukar gaba da ni daga yanxu har bayan watanni” bayi ya nufa yana dariya, faisal na taya sa. A tare duk suka fito daga mosque din bayan an idar da sllh, Junaid ya nufi motarsa ba tare da ya kallesu ba yace “Am going home” Faisal yace “Haba so early dama ba hira ka xo mu yi ba” Junaid ya kallesa yace “Ga Dr nan sae kuyi hiran, am going home kafin Mumy ta fara kirana” faisal ya rungume hannu yana dariya yace “Ehh gskya ne kuma wannan, madarar ka na can a feeder kar ya huce koh” murmushi junaid yayi yace “Yea! Sure.” Daga haka ya nufi motarsa, El-Ameen yayi dariya yace “Allah ka nuna mana ranan da Junaid xae girma kamar mu” makullin motarsa ya mika ma Faisal yace “kaga shigar min da motata ciki, tare xa mu tafi, ltr xan dawo inji yanda ku ka yi da Dr isah” faisal yace “Ohk sai ka dawo” motar Junaid El-Ameen ya nufa da sauri ya bude ya shiga, Junaid dake kokarin tada motar ya kallesa yace “Ya aka yi?” El-Ameen ya hararesa yace “Mu je ka siya min potatoe dina mana, ko ka xaci na manta ne” murmushi junaid yayi ya tada motar ya ja suka bar wajen. Wani eatery ya tsaya ya fito ya shiga ciki, El-Ameen ya bi sa da kallo, ba a dau lkci ba ya fito rike da take away din fried Irish har hudu, ya bude bangaren da El-Ameen ya ke ya dungure masa ledojin a kan kafarsa snn ya rufe motarsa ya xaga ya shiga, dariya El-Ameen yayi yace “Toh me kenan, ni ae wannan ya min kadan” Junaid bae tanka sa ba ya tada motarsa suka bar wajen. Sae da suka hau kan titi ba tare da ya kallesa ba yace “Ina ka nufa don ni am going home” El-Ameen yace “drop me at home,” junaid ya kama hanyar gidan nasu yana isa yayi parking ya juya yana kallon sa, bude motar El-Ameen yayi yace “Gobe xa ayi diagnose dinta!” Junaid ya gyada kai yace “Allah ya kai mu” El-Ameen ya fita daga motar yace “Ka gaida Mumy” kai junaid ya kuma gyada masa sannan ya ja motar ya bar kofar gidan.

yana isa gida ya dde xaune cikin motarsa a parking lot yana danna waya, fatima ce ta leko jin bae kashe motar ba har lkcn, yana ganinta ya kashe motar ya fito ya rufe, kallo daya yayi ma Umma da fitowarta daga side din Abba knn ya dauke kai yayi side din Mumy, Umma ta bi sa da kallo ta gefen ido tayi kwafa ta nufi bangarenta. Kwanciya Junaid yayi bayan ya gaida Mumy, Mumy ta xauna tana kallonsa tace “Ga lunch dinka a dinning” yace “Toh Mumy,” Humainah ce ta fito daga kitchen ta shigo palon tace “Na gama Mumy” Mumy tace “Sannu Humainah, dauko ma yayanki abincinsa a dinning” ta juya ta tafi dinning din ta dauko warmer biyu, daya me dauke da jollof rice daya kuma farfesun naman rago, ta dauki plate da spoon ta dawo palon ta dire gaban Junaid dake kwance har lkcn idonsa lumshe, ta mike ta koma ta dauko drink da ruwa sae cup ta dawo ta ajiye, Mumy tace “Toh tashi ka ci abincin mana” mikewa xaune yayi yana kallon Humainah dake durkushe wajen har lkcn ya hade rai, ita ma haka, harara ya galla mata yace “ke wa yace ki shiga dakina ki dauki turare” ta tabe baki tace “Toh meye? kuma naga turaren kala kala ne shi yasa” Mumy tayi dariya tace “Atoh!” Ya wani hade rai sosai yace “God help yhu ki sake shiga daki na ki ga” mikewa tayi tace “Mumy xan je gun Hajja” Mumy tace “Toh kiyi mata sannu da xama” daga haka ta galla masa harara ta fice daga palon, sakkowa Junaid yayi ya xauna kan carpet yace “Yarinyar nan ta raina ni fa Mumy” Mumy tayi dariya tace “Ko dai kana ciki ne Captain” kallon Mumy yayi da sauri sai kuma ya marairaice mata yace “Ina ciki kuma Mumy, A’a ni matata na nan xuwa in’sha Allah, beside bana sha’awar auren xumunci ni” Mumy tayi dariya tace “Toh ka dinga sake mata don tunanin da Hajja da ‘yan gidan ma xa su yi kenan, idan suka ga kuna haka da ita, kasan yanxu samarin nowadays idan suna son mace sae suyi ta wani basarwa, kaga suna yawan fadace fadace da ita barin ma idan yar uwar sa ce, wae su nan kar ta gane suna sonta ta raina su, wasu har da duka wae kuma duk cikin so ne fa” dariya sosai Junaid yayi yace “Ae kauyanci knn Mumy” Mumy tayi murmushi tace “Atoh, sae ka ga daga karshe idan suka ga yarinyar na neman kubuce masu su haukace su fito fili suce su fa sai ita” dariya junaid yake yace “Kai Mumy, wannan ae sae film ba dai reality ba” Mumy tayi murmushi tace “Toh shknn, it seems you’ve neva come across dat before” yace “Uhnn toh Allah kyauta, but it kinda funny mum” abincin gabansa ya bude ya dibi shinkafar dai dai wanda xae ci da plantains da nama sannan ya rufe, yayi bismillah ya fara cin abinci, yana gamawa Mumy ta kira mai aikinta ta fito ta kwashi plates din da warmer ta kai kitchen, kiran sllhn Asr yasa shi mikewa ya shiga bayin dake Palon ya dauro alwala ya fito, fatima da fitowarta palon kenan ita ma da shirin islamiyya tace “Ya A.jay xaka yi dropping dina in jira” yace “No” kofa ya nufa ya fita daga palon. Yana dawowa daga masallaci part din Hajja ya shiga, ya sameta xaune ta sa TV a gaba, Khadija kuma na kwance tana danna waya, xaunawa yayi yana kallon Hajja dake bin sa da kallo yace “wannan kallon fa Hajja” Hajja ta tabe baki tace “Ba sai ka tsole min idon ba” Khadija ya kalla ya hade rai yace “Ranan da xan xane ki na nan tahowa a gidan nan, baki da aiki sai danne danne kin yaye islamiyya yanxu koh” Hajja ta gyara xama tace “Ai mu sai Allah yayi mana shari’a da shegen wahalallen da ya kirkiri waya a duniyar nan ya bata mana ‘ya ‘ya, yanxu ace kamar Khadija daga safe har talatainin dare wancan shegen abun na hannunta tana latsawa tana murmushi, ta fa ji tsoron Allah taji tsoron gamuwarta da shi, Allah kadai yasan tsiyar da take tsulawa a shegen abun, shi kuma Muhammadu ba mai sa ido ba, ta inda bala ya fi sa kenan don har yau bai bari Humainah ta rike waya ba, wannan bala’i da me yayi kama? kana mata magana ma bata san kana yi ba ido kyar a kan waya, amma mu je xuwa ranan da Allah xai tashi kamata sai dai yar iskan wayar tayi bindiga a hannun ki wllh” kallon Hajja kawai Junaid yake kafin ya tabe baki ya kalli wayarsa dake ringing a hannunsa ya ga El-ameen ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button