CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers Association????
Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar

33…..

Mikewa Hajiya tayi da sauri tana kallon kafar Jasmine tace “Balki tashi ki ga ikon Allah” da sauri Umma ma ta tashi ta bude baki tana kallon kafarta, a hankali Junaid ya tura kofar parlon ya shiga gabansa na faduwa, babu kowa parlon ya karasa ciki yana rike da hannunta har lokacin ya isa 3 sitter ya xaunar da ita shi ma ya xauna ya kalli Hafsat ya nuna mata gefen jasmine, ta karaso ta xauna suka sa ta tsakiya, kalle kallen parlon kawai jasmine ke yi, yana son xuwa ya sanar ma Mumy xuwansu amma yana tsoron kar ta bi sa, haka suka ta xama parlon, Hafsat dai sai kallonsa take ganin bai da niyar ta shi ya sanar da mutan gidan xuwansu, fatima ce ta fito parlon, ta d’an xaro ido ganinsa tace “Lah Ya Ahmad!” yace “Kira Mumy” kallon Hafsat tayi ta gaida ta, Hafsat ta amsa da murmushi, ta juya tana kallon Jasmine ita ma ta gaida ta, kallonta kawai Jasmine ke yi kmr idonta xa su yi magana, Junaid yace “Leave ki je kiyi abinda na sa ki” juyawa tayi ya bar parlon tana mamakin abinda yasa taki amsa gaisuwarta, Junaid ya kalli Hafsat da sauri yace “Tana fitowa sai ki gaisheta duk me xata ce kiyi ta bata amsa kawai” Hafsat ta gyada masa kai, ba a dau lokaci ba Mumy ta fito parlon, kwata kwata bata dauka da gaske Junaid yake ba, murmushi dauke fuskarta ta karaso tana kallonsu ta xauna tace “Sannun ku da xuwa” Hafsat tace “Yauwa Mama ina yini” tace “Lafiya lau, ya hanya” Hafsat tayi kasa da kai tace “Alhmdllh,” ganin hankalin Mumy na kan Hafsat Junaid yyi saurin cewa “Tana gaishe ki Mumy” ya fadi hakan yana nuna Jasmine, Mumy ta kalli Jasmine don ita dai bata ji tace komai ba, ta dai yi murmushi tace “Lafiya lau, sannun ku da xuwa” Hafsat tayi saurin cewa “Yauwa Mama” Mumy ta kira fatima ta fito tace “Dauko masu ruwa fatima” kitchen ta shiga ta fito da tray ta nufi fridge ta bude ta fiddo ruwa da drink ta dawo parlon, kusa da Jasmine ta ajiye tray din ta kuma komawa kitchen ta dawo da snacks, Jasmine ta kalli Junaid da gabansa ke ta faduwa ta fara kokarin sauka kasa ai da sauri ya riketa yanda bbu wanda xai lura, ya jawo remote yayi powering tv, tvn na kawowa ta koma ta xauna tana kallo, sallaman su Umma da Hajiya yasa xuciyarsa kusan shigewa cikinsa, suka karaso parlon su Suhaima na biye da su a baya ko warce da murmushinta a fuska, Hajiya tace “Ashe bakuwar har ta iso ko a sanar da mu, sannun ku da xuwa,” Mumy tace “Ae kuwa, da wai idan sun tashi tafiya xa su shiga su gaida ku” Umma tace “Allah sarki” Hafsat tace “Ina yinin ku” suka amsa mata a tare, Mumy dai sai kallon mamaki take ma jasmine dake ta kallo kamar her life depend on it ganin bata gaida su ba, Junaid ya lura da hakan hankalinsa ya tashi ba kadan ba, su kansu su Umma kallonta suke, Hajiya tace “Toh wai wacece surkuwar ta mu a ciki” Junaid na shirin cewa Hafsat ce, Hafsat ta riga sa ta hanyar nuna masu jasmine, ya xaro ido don shkkn tasa ta samesa, Umma tace “Ikon Allah, sannu Amaryar mu” nan ma dai ko dagowa Jasmine bata yi ba idonta na kan TV, Hajiya tace “Toh fah, anya amaryar nan na jin mu kuwa” Hafsat tayi saurin cewa “ba ma ta jin dadi ne muka fito…” Umma tace “Ikon Allah, ana burin auren lafiyayya shi kuma ra’ayinsa kenan bawan Allah, Allah sarki naga ma kamar ciwo gareta a kafa don bbu takalma ku ka shigo” lumshe ido Junaid yayi a hankali ya bude, shi kam ya shiga uku da matan ubansa, Mumy dai bata tanka su ba ta kalli fatima tace “Xubo masu abinci fatima” Guri Hajiya ta nema ta xauna tana cewa “Tun da baki gare mu bari mu xauna” Junaid ya watsa mata wani kallo ta gefen ido, Umma ma ta xauna tana cewa “Toh baxa a kai ta gun Hajja ba tun da tana nan…” Gaban Junaid yayi wani mugun faduwa jin sunan warce ta kira, Mumy tace “Xa su je” Hajiya tace “Ya kamata kam, ai da mun san da xuwansu da ko ‘yar girki ne mun yi” kallonsu kawai Hafsat take ko ba a gaya mata ba tasan matan ubansa ne, Fatima ta fito daga kitchen rike da warmer din abinci da plates da spoon, Junaid ya kalli Mumy a hankali yace “Baxa su ci ba Mumy” Hajiya tace “Suka gaya maka? Ke xo ki ajiye masu” Ko kallonta bai yi ba, fatima dai ta dire abincin gabansu, a hankali Mumy tace “Xuba mana” Bude kofa aka yi Humainah da Khadija suka shigo Hajja na biye da su a baya tana cewa “Don jaraba mutum ya kwaso uban tafiya a rasa abinda xa a hada sa da sai wani tsinannen taliya can, tsiya dai a gidan Muhammadu ta kare…” Khadija na ganin Jasmine tayi still bakin kofa da mamaki, Humainah kam kallo daya ta masu ta nufi daki, Hajja ta karasa shigowa parlon tana bin kowa da kallo tace “Xaman me ake haka, me ya faru” Hajiya tayi murmushi tace “Kishiyar ki Ahmad ya kawo mana mu gaisa” Hajja ta washe hakora tace “Ikon Allah, tana ina” lumshe ido Junaid yayi ya jinginar da kansa jikin kujera don yasa tasa ta kare kawai, Umma tayi murmushi ta nuna mata jasmine tace “Ga ta can kamar bebiye ba uhm ba uhm uhm,” Hajja ta karaso baki har kunne tace “Ke don baki da kunya har gida xaki xo kwacen miji, to ahir dinki ni da Amadi mutu karaba” shi dai Junaid har lokacin yaki bude ido, ji yake kamar yayi tsuntsu ya bar parlon, Hafsat ma duk ta rasa abun yi a lokacin, fatima ta bude kulan me dauke da hadadden spaghetti ta shiga xubawa, Hajja ta dunguri Jasmine tace “Ya hure maki kunnen kar ki gaisheni kenan koh, to ba karamin aiki na bane in kora ku ke da shi wllh” juyowa Jasmine tayi da sauri tana kallonta, wani kara da ya tsorata occupants din parlon ta saki da karfi, Hajja na tuntube tayi kofa da gudu tana salati a tsorace, fatima ma dake gabanta tuni ta rufa ma Hajja baya, Hajiya da Umma da su Suhaima duk aka mike a tsorace, Mumy ma ta mike tana kallon Junaid, juyowa Jasmine tayi ganin ta kora Hajja, idonta ya sauka kan spaghettin da fatima ta fara xubawa a plate, wani karan ta kuma saki a rikice ta daga kafarta tana matsawa kusa da Junaid kamar xata shige jikinsa tana kallon taliyar, ae sai ga Umma da Hajiya ma bakin kofa da gudu ‘ya yansu na biye da su a baya, Mumy kanta barin wajen tayi, Khadija ta karaso da sauri ta dauke taliyar tunawa da tayi haka ta ma indomie ranan, Hajiya ta saki salati tana tafa hannu tace “Al-qur’an mahaukaciya ce” Hajja ta dafe kirji tace “Mahaukaciya kuma” Mikewa Junaid yayi ya dagota, da gudu Hajja tayi waje su Hajiya suka rufa mata baya da gudu su ma, Mumy tace “Ahmad” tsayawa yayi ya juyo a hankali yana kallonta, sake hannun Jasmine yayi ya karasa kusa da ita cikin sanyin murya yace “Na’am” jin bata amsa ba ya dago kai yana kallonta ganin yanayin fuskarta yasa jikinsa yayi sanyi sosai, strictly tace “Wacece yarinyar nan” kasa ce wa komai yayi ta masa wani tsawa tace “Ba magana nake maka ba” a hankali yace “Ita nake son aure, Mumy it’s a long story… Am sorry i hide everything for you, tana da brain disorder ne, so…” Mari Mumy ta sauke masa, Humainah dake tsaye bakin kofar daki tana kallon duk abinda ke faruwa ta juya a hankali ta bar wajen, lumshe idonsa yayi ya bude, Hajiya na tafe hannun ta saki shewa tace “Maganar Suhaima dai ya tabbata….” Hajja ta leko parlon tace “Amma na tausaya ma gwalma’da’dden rayuwar ka Ahmad, ka rasa shegiyar da xa ka kawo mana matsayin surka sai mahaukaciya, to Allah sai ya mana hisabi da kai, kuma maxa ku kira min ubansa duk inda yake ya dawo yaga me ya haifa ma kansa…” Hafsat da tausayin Junaid ya rufeta ta juya ta nufi kofa, da sauri Suhaima ta fincikota tace “Ke kuma algunguma munafuka har da yi ma mahaukaciyar jagora koh…..” Mari me lafiya Hafsat ta sauke mata, Hajja tace “Kambu Ramaa!” Tun kan ta rama Hafsat ta kuma sauke mata wani, Muhibba da Sadiya suka yi kanta, ta fixgi wani vase dake parlon tace “Duk yar iskar da ta matso kusa da ni wlh sai na buga mata kuma babu abinda xai faru don baku son wanene ubana ba, yau Allah ya ga dama kuma sai ya daura maku haukan nan, kuma mahaukaci ai mutum ne, ba sonku Allah ya fi yi a kanta ba da ya bar ku da hankalin ku, ku ba abun farin cikin ku bane d’an ku xai yi jihadi ma, ga dai gida kamar babba amma karami ne” jefar da vase din hannunta tayi ta fice daga parlon, Hajja tace “Kaji gantalalla k’awar mahaukaciya kawai, uban waye hamagon uban naki, to mu dai xuri’armu babu mahaukaci, ke ubanki yayi jihadin ya aureta mana yar buhu kawai” tuni Hafsat ta kusa gate abunta, Hajja ta fashe da kuka tace “Ni kuu kira min Muhammadu ya xo ya ga abun da muke gani, Ahmad ya cuce mu, ya xo ya ga sa6on da Ahmad ya tafka, amma duk laifin uwarsa ce wllh kuma mu dai Allah ya isa, ina laifin ka fiddo ‘yar uwar ka Humainah a matsayin warce xaka aura, ko ka xabo cikin kannin nan naka Suhaima da Muhibba, toh ni ina ya samo mahaukaciyar ma tukun” Mumy da har idonta ya kawo ruwa ta kalli Junaid da kansa ke kasa tace “Maida ta inda ka daukota kuma minti talatin kawai na baka kaje ka dawo” juyawa yayi yana rike da ita ya nufi kofa, Hajja da su Hajiya da suka ji kamar suyi shewa ana rige rigen gudu aka bar bakin kofar. Junaid na ganin dishi dishi ya nufi mota da ita, driving kawai yake amma bai ma ganin gabansa da kyau ji yake kamar a sama yake tafiyar ma, ihun da jasmine tayi da karfi yasa idonsa ya bude sosai, sai a sannan yaga irin tukin da yake da ihun da jama’a ma suke yi, kokarin kauce ma babban motar da yake kokarin karo da yayi, amma hakan bai yiwu ba don sai da suka yi karo bayan haka ya juya kan motar yayi gefen titi yayi cikin jama’a nan ma yaje ya buge da pole, sama sama ya dinga jin abinda Jasmine ke cewa, iya karfinta take cewa Umminta…. Umminta, Wayyo Umminta…. daga haka bai sake jin komai ba kuma bai sake sanin abinda ke faruwa ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button