CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske writers Association
Captain Ahmad Junaid

 _By Khaleesat Haiydar_✍????

18…..

Amai ta shiga kwararowa a gurin, ya mike yana kallonta har ta gama ta koma xata kwanta yayi saurin riketa, kara ta saki ta turasa da karfi xata kwanta gun aman yaki saketa, nan ta shiga kokuwa da shi ita sai ta kwanta, ya rike ta gam yace “Wait Jasmine…” ta kuma sakin wani ihun da ya tsorata shi, ae da ta turasa sai da ya kusa faduwa ba shiri ya saketa, ta yi kwanciyarta nan kasa, ya sauke ajiyar xuciya ya nufi toilet, mop da bucket ya dauko ya dawo dakin, rasa ta inda xae fara gyara wajen aman yayi, ya ajiye ya fita don kira Mama jummai, tare suka shigo dakin, ta karaso kusa da ita da sauri cike da tausayinta ta dagota tana mata sannu, ihu ta sakar mata ita ma ta kwace kanta ba shiri ta saketa ta koma ta kwanta tana mayar da numfashi, girgixa kai mama tayi ta mike ta shiga gyara wajen, tana gamawa ta kuma gwada d’aga ta a kasan tiles din still taki tashi, kyaleta tayi ta fita, Junaid ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito jin kiran isha, a nan dakin yayi sallah, yana xaune kan darduma ya ga tana juye juye a kasan da take kwance. Kallonta kawae yake cike da tausayinta don da ganinta kasan tana jin jiki, ta mike xaune a hankali ta dawo inda yake tana kallonsa ta kwanta kusa da shi, dagota yayi murya can kasa yace “Sorry Jasmine” lumshe ido tayi ta kwanta nan kusa da shi lkci daya bacci ya dauketa, ya mike ya koma can jikin gado ya xauna, har Karfe tara El-Ameen bai dawo ba, duk ya kagu ya dawo ya wuce kafin Mumy fa kirasa, tara da rabi kiran Mumy ya shigo wayarsa, k’asa d’agawa yayi don bai ma san me xai ce mata ba har sai da ya kusa katsewa sannan ya daga da sauri, Mumy tace “Where are you Ahmad” kallon dakin yayi kafin a hankali yace “Mumy, am am with El-Ameen” strictly tace “You are very stupid, within the next 10 to 15 mins ka tabbatar kana cikin gida if not xaka ga bacin raina, in kuma kaya ku ka kasa a titi ku ke saidawa da daddaren nan xaka gaya min” kamar mai shirin kuka yace “Kiyi hakuri Mumy xan dawo” katse wayar tayi, ya rike kansa, layin El-Ameen ya shiga nema yana ta ring bai d’aga ba, ya lumshe ido ya jingina jikin gado, he just don’t know wat to do, haka yayi ta kiran El-Ameen bai daga ba, Shivering yaga tana yi daga kwancen da take kan darduma, ya mike ya karasa inda take ya dago ta ta bude ido da sauri, kan gadon dakin ya kwantar da ita ya rufa mata bargo, ta cire xata sakko ya riketa da damuwa yace “You are shivering Jasmine” ba shiri ya saketa a dalilin kara me karfi da tayi masa a kai, ta sauka nan kasan dakin ta kuma kwanciya. Har goma El-Ameen bai dawo ba, Junaid ya rasa me ke masa dadi shi da bae taba yi ma Mumy musu ba, yasan kuma fushi tayi shi yasa bata kara kira ba, da yayi niyar tafiya sae ya tuna abinda El-Ameen yace masa, ya kuma san xai aikata, shine xaune har sha daya, Mama jummai ta shigo tace “Kai xaka kwana yau a nan kenan junaid?” D’an murmushi yayi yace “A’a ina jiran El-Ameen ne yace xai dawo” tace “Toh tafi daki can ka kwanta inda yake kwana xan kula da ita” Junaid yace “yana kwana nan ne?” Tace “Eh wani lkcn yana kwana can dakin don akwai alluran da yake mata da sassafe, toh duk ran da xai mata alluran a nan yake kwana, ni kuma tare muke kwana da ita saboda shiga bayi da daddare” Junaid ya gyada kai yace “Bari in jira sa a nan Mama ni ba kwana xan yi ba ai” tace “Toh” sannan ta juya ta fita. Lumshe ido yayi ya jinginar da kansa jikin gado, wani bacci ya ji na fixgarsa ya bude ido yana kallon agogo yaga sha biyu, kallonta yayi ya ga ta canxa position, a hankali ya mike ya isa inda take xai dagata ta bude ido da sauri, birginawa tayi ta bar gun ta juya masa baya, ya mike ya koma ya xauna kan gadon, xuwa yanxu kam ya gama sanin iskanci El-Ameen yayi masa, dole ko yaki ko ya so a nan xai kwana hakan ba karamin bata masa rai yayi ba, sha biyu da rabi ya kuma mikewa jin yana jin bacci sosai ya bude closet ya dau bargon da ya gani ya koma daya side din gadon ya shimfida a kasa ya kwanta dai dai yanda xai dinga ganinta, nan da nan bacci ya daukesa.
Bude ido yayi jin an bude kofa don ko k’adan bashi da nauyin bacci, El-Ameen ne ya shigo dakin yana ganinsa ya dauke kai, kallo daya El-Ameen yayi masa yana murmushi bai ma san idonsa biyu ba ya karasa gun da take kwance a kasa, durkusawa yayi gabanta ya dagota, ta bude ido da sauri, lumshe ido yayi jin xafin jikinta a hankali yace “Sorry, Jewel” xata koma ta kwanta yaki saketa, ya mike ya dauketa ya nufi kan gado da ita ya kwantar, kokarin sauka ta shiga yi da kyar, ya hade rai yace “No” bata kuma yunkurin saukan ba, ya gyara mata kwanciya ya mike ya shiga bayi, duk wannan abun Junaid na kallonsu, ya dawo dakin rike da bowl din ruwan sanyi ya bude closet ya ciro towel karami da babba ya saka karamin cikin ruwan bowl din ya dawo kan gadon ya ajiye bowl din kan bedside drawer, ya dagota yana kallonta don idonta biyu, ya dawo da bowl din ruwan gefensa ya matse ruwan towel din a hankali yana goge mata forehead dinta da shi, kara ta saki xata sauka ya hade rai yace “Wait!” Bata kuma yunkurin saukan ba, haka ya ci gaba da goge jikinta da yayi xafi sosai da towel din yana mata sorry, mikewa Junaid yayi, El-Ameen ya juya da sauri ya kallesa sannan yayi saurin rufeta da bargo yace “Ohh you weren’t sleeping dama” Junaid bai tanka sa ba ya dauke bargon da ya shimfida kasa ya mayar cikin closet, El-Ameen ya tabe baki yace “Ni ban ma yi tunanin xan dawo in same ka ba Mumy’s boy, theatre muka shiga da Abba and we came out few minutes ago, saboda nasan condition din patient dinka shi yasa na fito cikin daren nan, I ought to….” jin anyi banging kofa El-Ameen ya kalli kofar da sauri don dama yana magana ne yana matse towel a ruwa, murmushi yayi ganin ficewa yayi, ya ci gaba da abinda yake, har sai da yayi make sure temperature dinta ya dawo dai dai, still yayi ganin hawaye idonta, ya sunkuya a hankali ya goge mata fuskar yace “Am sorry Jewel, am only helping” sauka yayi daga kan gadon yaje ya xubar da ruwan ya shanya towel din a bayi ya fito, bacci ya sameta tana yi a yanda ya barta, ya gyara mata kwanciya sannan ya hada allura yayi mata da kyar don a tsorace ta farka ta fara kokuwa da shi, sai da yaga ta koma bacci sannan ya fita dakin ya shiga master bedroom duk a tunaninsa xae tarda junaid nan, sae yaga otherwise, tabe baki yayi sanin yana parlor knn, ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya canxa kaya yayi kwanciyarsa dakin, sai dai before dawn yaje dubata ya fi sau goma duk da a shigowarsa na uku ya tarda mama jummai a dakin, Karfe biyar da minti arba’in ya sauko parlor ya tarda Junaid xaune kan darduma, xaunawa yayi kan kujera yana kallonsa yace “A parlor ka kwana kenan?” Junaid ba tare da ya kallesa ba yace “Yea!” El-Ameen yace “Ohk, gud morning, yanxu dai you need to transfer some money into my account xuwa later akwae drugs din da na mata prescribing, and you know wat? Suna da tsada gaskiya or I shud just text you their names, tell you where to get them, kaje da kanka ka siyo, if you need my assistance let me know” El-Ameen ya kare maganar yana d’aga kafada, Junaid ya mike ya dauke darduman da yayi sallah yace “nawa ne kudin?” El-Ameen yace “100 nd 50k will be enough” Junaid yace “Alryt” ajiye darduman yayi kan kujera ya kalli El-Ameen yace “Na tafi, I will transfer it later in the day” bai jira cewarsa ba ya nufi kofa ya fice daga parlorn, makullin motarsa ya ciro a aljihu ya fita waje inda ya ajiye motarsa ya bude ya shiga ya kama hanyar gida, driving kawae yake amma gaba daya hankalinsa ba ya tare da shi, bai san yanda xa su kwashe da Mumy ba, toh ina ma xai ce mata ya je, gidansu El-Ameen? No yasan xata iya kiran Ummi, murmushi yayi yana tunanin randa xae samu freedom, don ya fara damunsa yanxu on like before, a waje yayi parking ya fito, gabansa ne ya fadi ganin Abbansa alamar daga masallaci yake, da kyar ya ja kafa ya isa gun gate ganin Abba ya tsaya har ya risina xai gaida Abba, Abba ya dakatar da shi yace “Daga ina kake?” Yayi kasa da kai zai yi magana Abba ya juya ya shiga cikin compound, bin bayansa yayi har suka isa part din Abba, Hajiya ke ta goge goge a parlon, Abba ya xauna kujera yana kallon Junaid, a hankali ya xauna kasa ya juya yana kallon Hajiya dake kallonsa da d’an murmushi mai wuyar fassara a fuskarta yace “Ina kwana Hajiya” tace “Lfya lau Ahmad” sunkuyar da kai yayi, Abba yace “Daga ina kake Ahmad?” A hankali yace “Tare muke da El-Ameen Abba” Abba yace “Tare a ina?” Hajiya ta dawo cikin parlon tana girgixa kai tace “kwata kwata ni hankalina bai kwanta da abotansa da yaron nan wai El-Ameen ba, yaron da bai da nutsuwa ko maganan iyayensa bai ji, kusan duk dare sai ya shigo ya fita da shi, Ahmad baxae dawo gidan nan sai kusan sha biyu wani lokacin har daya, duk ina lura da yake ni ba mai nauyin bacci bace ka sani Alhaji, to amma kar mutum yayi magana ace hassada ko kuma ace don ba d’an sa bane, amma kwata kwata Ahmad ya sauya hali a gidan nan, jiya wllh wllh khadija ca tayi min mace ta gani a motarsa da magariban nan da ya fita, to ina yaje yake dawowa yanxu, kuma duk Hajiya Amina tana ganin abinda yake baxata ce komai ba saboda ta dauki son duniya ta daura ma yaro, meye amfanin haka, in ma aure yake so ba sai yayi magana ba, ae ba wae bai isa bane” tunda ta fara magana Junaid ya kafeta da ido ko kiftawa bai yi, Abba kuwa sai kallonsa yake bacin rai karara a fuskarsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button