CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers association????
[1/14, 9:15 AM] Elhajj: Captain Ahmad Junaid
By Khaleesat Haiydar
46…..
Kwance junaid ya sameta tana kuka a dakin, ya karasa ya xauna kusa da ita ya dago ta, turasa ta shiga yi cikin kuka take cewa “Ni ka kyaleni, ka kyaleni” a hankali yace “Listen to me plss Humainah, ba fa mahaukaciya bace” ta fashe da matsanancin kuka tace “Nace ka kyaleni ni dai” saketa yayi yana kallonta, ta koma ta kwanta tana ci gaba da kukanta, mikewa yayi ya fita daga dakin ya koma parlor, El-ameen dai kallonsa kawai yake bai ce komai ba, Junaid ya xauna ya shafa kansa yace “Shknn you can go Idan tafiya xaka yi” El-ameen yace “Toh gimbiyar taka ta yarda kar in tafi in bar yar mutane ta kasheta kana kallo” Junaid yace “In xaka tafi kayi tafiyar ka kawai” mikewa El-ameen yayi yana kallon Jasmine yace “Baby xaki tsaya nan har in dawo kin ji” kallonsa kawai take, ya durkusa kusa da ita yace “Kin ji?” Idonta ne ya cika da hawaye, a hankali El-ameen yace “Kuka kuma baby” shi dai junaid kallonsu kawai yake, El-ameen ya ciro handki ya mika mata yace “baxan dade ba xan dawo kin ji” karba tayi ya mike ya kalli Junaid sannan ya fita daga parlon. Kallonta kawai Junaid ke yi kanta a kasa tana fidgeting fingers dinta, can ya mike ya kullo kofar sannan ya dawo ya dau jakar kayanta yace “Tashi mu je” mikewa tayi a hankali tana kallonsa ya d’an mata murmushi yace “Follow me” daga haka ya nufi stairs ta bi bayansa, dakin dake kusa da na Humainah ya bude ya shiga ta tsaya daga bakin kofa tana kallon dakin, juyawa yayi yana kallonta yace “Shigo mana” a hankali ta shiga dakin ya rufe kofar, kan gado ya ajiye jakarta ya bude closet yace “Ki ajiye kayan ki duka a nan kin ji?” Sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, ya nuna mata kofar bayi yace “ga toilet nan” kallon kofar tayi ta gyada masa kai, yace “Are you hungry?” Girgixa masa kai tayi da ganinta kasan a tsorace take, yayi murmushi ya kunna mata tvn dakin yace “Ki xauna kiyi kallon ki toh” ta gyada masa kai ya juya ya fita daga dakin ya rufo mata kofar, da sauri ta mike ta nufi kofar ta bude, yana tsaye bakin kofar Humainah ya juyo yana kallonta, dawowa yyi yace “Ya aka yi?” Kamar xata yi kuka tace “ina jin tsoro” shiru yayi yana kallonta ta bude kofar sosai ta koma ta xauna a dakin, Dakin Humainah ya karasa ya bude ya shiga ya sameta har lokacin tana kuka ya rungume hannayensa yana kallonta, can ya karasa kusa da gadon ya xauna yace “Ke yanxu baxa a iya cin arxiki gun ki ba, baxa ki yi taimako ba, kwana biyu fa kawai xata yi ta bar gidan” ko kallonsa bata yi ba ya dagota ya rungumeta yace “plss mana, wllh xata bar maki gidan soon, she’s not staying long” turasa tayi tace “Bana so, kuma ni ka rabu da ni” hade rai yayi ya saketa ya mike yace “Toh wai gidan ki ne nan din? Ko a kanki take xaune” dago kai tayi tana kallonsa, ya watsa mata wani kallo ya juya ya fice daga dakin, wani sabon kukan ta fashe da har da shessheka. Dakin sa ya koma ya kwanta yana tunanin anya decision din da yayi na kawo jasmine gidan yayi daidai kuwa, har aka kira Azahar yana kwance, mikewa yayi daga karshe ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito, nan dakin yayi sllh yana xaune kan darduma bayan ya idar aka danna bell din gidan, mikewa yayi ya fita har lokacin dakin da jasmine take a bude yake, parlor ya sauka ya bude kofa, fatima da khadija ne bakin kofar rike da flask din abinci, gaishesa suka yi ya karba yace “Mun gode, ku gaida mutan gidan,” daga haka ya kulle kofar ya dawo cikin parlor, plate ya dauko a kitchen ya dibi couscous din dake cikin flask din ya bude na miya ya diba sannan ya rufe ya dau goran ruwa da cup da spoon ya haura sama, dakin da jasmine ke ciki ya shiga, kwance ya ganta a kasa ta takure waje daya tana bacci, ya shigo dakin ya ajiye abincin hannunsa yace “Jasmine” sau uku yana kiranta ganin bata tashi ba ya durkusa gabanta ya d’an taba ta, bude ido tayi ta mike xaune da sauri ganinsa, yayi mata murmushi ta sunkuyar da kai, yace “Me yasa baki kwanta kan gadon ba” shiru tayi bata ce komai ba, ya dauko darduma ya shimfida a kasa yace “Dawo nan” mikewa tayi ta xauna kan darduman ya ajiye mata abincin da ruwa a kai yace “ga abinci ki ci” kai ta gyada masa, yace “Toh ci mana” a hankali ta dau spoon din da dibi abincin ta kai baki tana kallonsa, murmushi ya mata yana kallon yanda take tauna abincin, yace “You like it?” Kai ta gyada masa, ya mike yace “Toh maxa ki cinye kafin in dawo” daga haka ya fita daga dakin ta bi sa da kallo. Ko da ya dawo xaune ya sameta ta tura abincin gabanta tayi jigum, ya karaso ya durkusa gabanta yace “Baki ci ba kuma” ta girgixa masa kai a hankali tace “Na ci” yace “No! kadan kika ci” spoon din ya dauka ya dibi abincin ya kai mata baki, a hankali ta bude bakin ya xuba mata, haka ya dinga bata har abincin yayi rabi ta kauda kai tace “Na koshi” ajiye spoon din yayi yana kallonta yace “Toh tashi ki je kiyi alwala ki xo kiyi sllh” mikewa tayi ta nufi toilet yace “Baki cire hijab din ki ba” dawowa tayi ta cire Hijab din ta ajiye, ya bi ta da kallo har ta shiga toilet din sai dai bata rufe kofar ba, mikewa yyi ya fita ya koma dakin sa. Lokaci lokaci ya kan lekota, tausayinta kawai yake ba kadan ba barin yanda ya lura duk a tsorace take, ana kiran sllh magrib ya shigo dakin bai ganta ba, kiranta ya shiga yi amma shiru ya juya ya fita ya sauko downstairs, kitchen ya sameta tana wanke d’an plates din da aka bata, ya tsaya bakin kofa yana kallonta, da sauri ta juyo a tsorace, wara ido yayi yace “Uhum!” A hankali tace “washing nake yi” murmushi yayi mata yana gyada mata kai, ta juya ta ci gaba da wanke plates din, yace “Me xa ki ci for Supper?” Ta juyo tace “Supper?” Ya gyada mata kai yace “Yea dinner” ta d’an langwabar da kai a hankali tace “na koshi” wara ido yayi yace “me kika ci?” juyawa tayi ta ci gaba da wanke wankenta. Har ta gama yana tsaye bakin kofar, ta juyo tana kallonsa, murmushi yayi mata ya fita daga kitchen din ta bi bayansa suka haura sama, yace “Tafi kiyi sllh” kai ta gyada masa ta shiga dakin da take, shi ma ya shiga nasa. Ana idar da sllh ya tafi siyo masu abinci, ajiye abincin yayi a parlor bayan ya dawo ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera, can ya mike ya shiga kitchen ya dauko plate ya dau take away daya ya juye ya sa spoon ya dau ruwa ya tafi sama, xaune ya sameta bakin kofar dakin tana ganinsa ta mike tsaye, yace “uhum!” a hankali tace “Tsoro nake ji” kallonta ya tsaya yi kafin ya shigo dakin ya ajiye mata abincin hannunsa yace “Toh xo ki ci abinci” ta karaso ta xauna inda ya ajiye mata abincin, bin sa da kallo tayi har ya fita sai dai bai rufe mata kofar ba. Har xai shiga dakinsa ya tsaya ya kalli dakin Humainah, karasawa yayi ya bude kofar, xaune ya ganta can karshen gado kanta hade da gwiwa, a hankali ya karasa kusa da ita ya xauna yace “Still crying?” Mikewa tayi xata bar wajen ya fixgota ya ce “Ina xa ki?” Ta fashe da kuka sosai, rungumeta yayi a hankali yace “Alryt am sorry, kiyi hakuri… She’s going tomorrow tun da baki so” boye fuskarta tayi jikinsa tana kuka a hankali, yace “Toh ba nace kiyi hakuri gobe xata tafi ba” muryarta na rawa tace “Toh wacece ita” dago kanta yayi yana kallonta, can yace “Ohk I will tell who she is” janyeta yayi a jikinsa ya koma baya yana kallonta yace “Amma fa it’s a long story” sunkuyar da kanta tayi, nan ya fara bata labarin ynda ya hadu da jasmine har xuwa wannan lokacin, kallonsa kawai take ko kiftawa bbu bata kuma ce komai ba, ya lumshe ido ya bude yace “Tana regaining memorynta Idan Allah ya yarda xa ta koma gun iyayenta, ita din abun tausayi ce, a yanxu bata da kowa sai mu da muka taimaketa” dauke kai Humainah tayi, ya matso kusa da ita yace “Baki ce komai ba” turo baki tayi tace “Toh ka kai ta gidansu El-ameen mana” murmushi yayi yace “In tambaye ki” ta dago kai tana kallonsa, yace “wai kishi na kike Humainah?” Hade rai tayi tace “Kamar ya? Sbda me xan yi kishin ka” yace “Toh me sa baki son ta xauna nan?” Tabe baki tayi tace “Ta xauna mana ni ina ruwana, kawae abinda na sani ka kai ni sch next week” murmushi yayi ya mike ya fita daga dakin, abinci ya dauko mata ya ajiye dakin yace “Ga abinci!” Ko kallonsa bata yi ba ya fita daga dakin. Karfe tara da wani abu ya mike daga kwancen da yake ya fita xuwa gun Jasmine, xaune ya sameta bakin kofa tayi jigum, ya d’an bude ido yace “kina nan har yanxu” mikewa tsaye tayi kamar xata yi kuka tace “Ni kadai xan yi bacci a nan?” Kallonta kawai yake ya ga hawaye idonta, girgixa mata kai yayi yace “A’a ba ke kadai xaki kwana ba, ina xuwa” daga haka ya fita ya shiga dakin Humainah, xaune ya sameta daure da towel gaban madubi, hade rai tayi tace “Kaya xan sa” yace “Uhm did I hold you?” Marairaice masa tayi tace “Ka fita plss” karasowa yayi kusa da ita ta mike da sauri, ya d’an bude ido yace “what?” Kamar xata yi kuka tace “Ka fita plss” yace “Alryt xan fita, amma abokiyar kwana xan kawo maki” kallonsa tayi da sauri tace “Kamar ya?” Yace “ku kwana tare da yarinyar plss” da mamaki take kallonsa tace “Mu kwana?” Matsowa yayi kusa da ita ta koma baya da sauri tace “Wayyo ya A jay ka fita plss” ya langwabar da kai yace “Toh in kawo maki ita?” Gyada masa kai tayi da sauri, yayi murmushi ya juya ya fita ta bi sa da kallo, tsaye ya samu Jasmine a daki tana ganinsa ta nufesa da sauri ta juya masa baya tace “Cire min abun” kallon Zip din kawai yake daga sama xuwa kasa na kusan minti daya, ta juyo a hankali tana kallonsa, kifta ido yayi da sauri yace “Na’am” a hankali tace “Ban iya cirewa ba, Mami da farida suke cire min” gyada mata kai ya shiga yi kamar kadangare, ta kuma juya masa baya, yayi baya da sauri yace “Ohk Ohk mu je a cire maki nima ban iya ba” daga haka ya nufi kofa ta bi bayansa, dakin Humainah ya shiga ita ma ta shiga, kallonta kawai Humainah ke yi daga sama xuwa kasa gabanta na faduwa, karasawa Jasmine tayi kusa da ita ta juya mata baya a hankali tace “ki cire mun abun” kallon Junaid Humainah tayi, ya gyada mata kai yace “Help her wai bata iya ba” da kyar Humainah ta daga hannu ta xuge mata Zip din, kokarin cire rigar ta shiga yi da sauri Junaid ya juya har yana buge kofa ya fita daga dakin, Jasmine ta kuma kallonta tace “Baki cire dayan ba” Humainah ta balle mata bra din ta koma gaban madubi, bin ta da kallo Jasmine tayi tace “Ina san inyi wanka” ko kallonta Humainah bata yi ba, Jasmine ta bi ta tace “Xan yi wanka” ba tare da Humainah ta kalleta ba ta nuna mata kofar bathroom, Jasmine ta nufi kofar ta bude ta shiga, a bude ta bar kofar, Humainah ta mike ta koma gefen gado ta xauna xuciyarta na bugawa, har Jasmine ta fito daure da towel dinta, ta gefen ido kawai Humainah ke kallonta, ta iso kusa da ita tace “cloth dina” Humainah ta hade rai tace “ki saka wanda kika cire mana” “toh” kawai jasmine tace ta tafi inda kayan da ta cire yake ta dauka ta sa ta kuma dawowa ta durkusa kusa da ita tace “Sa min” xuge mata Zip din Humainah tayi ta kwanta abunta, jasmine ta mike ganin ta kwanta ita ma ta kwanta nan kasa. Junaid na fitowa daga wanka ya dau wayarsa dake ring ya ga El-ameen ne ke kiransa, dagawa yayi El-ameen yace “Matar taka ta hakura dai koh?” Junaid yace “May be” El-ameen yace “Kasan me, bata yarda fa ta kwana ita kadai ya xa ayi gashi amarci ku ke ci….” Junaid yace “Ko kuma angwanci ba” El-ameen yace “Serious xata yi ta maku ihu ne cikin dare bata yarda ta kwanta ita kadai” junaid yace “ta gaya min, tana dakin Humainah yanxu ma” El-ameen yace “Ohk bata waya plss” Junaid yace “Kace mata me?” El-ameen yace “kai dai ka bata” shiru junaid yayi can yace “Naji” katse wayar yayi hade da yin tsaki ya saka jallabiyarsa ya fita daga dakin, da sallama ya tura kofar dakin Humainah ya d’an bude ido ganin jasmine kwance a kasa ya karasa ya durkusa kusa da ita yace “Me ya sa kika kwanta a nan” shiru tayi bata ce komai ba, ya kalli Humainah ya ga rufe idonta ma tayi, jasmine ya kuma kallo yace “Tashi ki hau gado” mikewa tayi ya nuna mata daya side din gadon ta xaga ta hau ta kwanta, a hankali ta matso kusa da Humainah shi dai kallonta kawai yake, wayar hannunsa ne ya fara ring ya kalli screen din, sai da ya kusa katsewa ya daga ya mika mata, karba tayi tana kallonsa yace “Kiyi magana” wayar ta kai kunnenta tace “Na’am” El-ameen yace “Baki yi bacci ba baby?” Ta kalli Junaid da ke kallonta ta sunkuyar da kai a hankali tace “Xan yi” juyawa junaid yayi ya fice daga dakin, “Kin ci abinci kuwa” tambayar da El-ameen yayi mata kenan ta gyada masa kai tace “Eh da afternoon ya bani wannan small rice da miya, na ci kadan Saboda ba dadi sai ya xo ya bani a baki” shiru El-ameen yayi bai ce komai ba, Humainah ta bude ido da sauri tana sauraren abinda take cewa gabanta na faduwa, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace “Da ya baki a bakin sai kika ci?” Kai ta gyada masa tace “Eh da ya bani na ci, uncle he’s kind, I like him just like Abba” mijin Dr Sumayya kenan, katse wayar El-ameen yayi, Humainah ta mike xaune xuciyarta na tafarfasa can ta mike ta fice daga dakin, da sauri Jasmine ta mike ta bi bayanta ita ma, dakin Junaid Humainah ta shiga ta gansa tsaye yana saka pyjamas dinsa, juyawa yayi yana kallonta ta xube wajen ta fashe da kuka sosai, karasowa yayi kusa da ita ya durkusa gabanta da mamaki yace “Me ya faru?” Jasmine ce ta shigo dakin ta karasa kusa da su a hankali ta durkusa ita ma tana kallon yanda Humainah ke kuka.
[1/14, 9:15 AM] Elhajj: ⚓ Captain Ahmad Junaid

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button