CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers Association ????
Captain Ahmad Junaid

   _By Khaleesat Haiydar_✍????

2….

Junaid na isa gidan su El-Ameen yyi parking daga waje ya shiga, Sumayya kanwar El-Ameen ya samu xaune falo da kawayenta biyu, ya karasa cikin falon cikin tafiyarsa ta k’asaita, yi tayi kmr bata gansa ba ta ci gaba da ba kawayenta labarin da take, gaida shi kawayen nata suka yi suna kallonsa, don Capt Junaid ko namiji bae masa kallo daya, ya amsa gaisuwar su ba tare da ya dube su ba yana kallon Sumayyar yace “Ke yayanki na gida?” Ba tare da ta kallesa ba tana yatsine fuska tace “Nima bn sani ba” wayarsa ya ciro aljihunsa ya shiga kiransa, Kawayen nata biyu duk suka xuba masa ido, El-Ameen na d’agawa Junaid yace “are yhu at home?” El-Ameen yace “Yea are you coming?” Wani kallo ya watsa ma Sumayya ya katse wayar ya nufi dakin El-Ameen, Husnah ta sauke wani ajiyar xuciya tace “Kai Sumayya waye shi, ya hadu wllh, don Allah ni dae ki hada ni da shi, yyi min ni dae plss” Sumayya tayi dariyar rainin hnkli tace “Uhm Kinga gayen nn irin mace masa da nake a da, na so shi kmr raina amma he looked into my face nd told me baya sona, I cried my life dat day, gashi i downgraded my sef telling him I love him” bude baki duk suka yi suna kallonta, Fiddausi tace “Tabdi! Toh meye hadin ku da shi? D’an uwanku ne?” Tsaki Sumayya ta ja ta dauki lemon gabanta ta shiga sa. Xaune ya samu El-Ameen kan laptop da siririn farin glass a idonsa yana danne danne, El-Ameen ya kallesa yace “Uhnn! Our great Capt Ahmad Junaid Murnai, kaga yanda ka kara kyau ka koma kamar wani Egyptian kuwa” Junaid ya tabe baki ya xauna gefen makeken gadon dakin yace “You will neva change” El-Ameen yyi murmushi ya tura laptop din gabansa ya juya yana fuskantarsa yace “I missed you a lot frnd, am glad you are back” Junaid ya shafa kansa yace “Sai kace gaske,” El-Ameen ya kura ma farin shirt din jikinsa ido yace “Wait! Ciwo ka ji Captain” Junaid ya kalli shirt dinsa da sauri ya ga jini daga gefen shirt din, El-Ameen ya mike yace “What’s dat? The shirt looks dirty ma” girgixa kai Junaid yayi ya shiga unbuttoning din shirt din yace “Wata mahaukaciya ce wllh” El-Ameen ya kwalalo ido yace “Mahaukaciya kuma” Junaid yace “Yea!” Nan ya ba El-Ameen lbrin abinda ya faru a hanyarsa ta xuwa, El-Ameen yace “Eyya! Poor her, but kai me ya kai ka rike mahaukaciya ma banda abun ka” Junaid bae ce komae ba ya mike ya nufi bathroom, wanka yyi ya fito sanye da Bathrobe din El-Ameen ya goge jikinsa ya bude wardrobe ya fiddo wasu kayan abokin nasa ya sa. Bayan Magrib yace ma El-Ameen xae koma gida, El-Ameen yace “Haba frnd baxa ka raka ni gun Iman ba plss, wllh ban san me xan ce ba idan na je, gashi Mami fushi take da ni, escort me plss, dama jira nake sai ka dawo sai mu je” Junaid yyi d’an murmushi yace “Ohk buh bari in kira mumy kar taji shiru har ynxu” Bayan isha suka bar gidan bayan Capt Junaid yyi ma Ummin El-Ameen sallama, A motar Junaid suka tafi El-Ameen na tukin, El-Ameen ya lura da yanda Junaid ya kafa ma tagar motar ta inda yake xaune ido yana kallon waje, El-Ameen xae yi magana ya ji Junaid yace “Dr d’an tsaya nn don Allah in ga ko an kwance mata igiyar, it’s gud ace anyi hkn” El-Ameen ya kafa masa ido sae kuma ya tabe baki ya daga shoulder ya gangara gefen titi yyi parking, Junaid ya bude motar ya fita, tana nn xaune kan bolan, rike da wani bakin Leda a hannunta, rungume hannayensa yyi yana kallonta, El-Ameen ya dafa sa yace “let move on Capt, they’ve freed her” juyawa Capt Junaid yyi suka koma motar suka bar wajen, suna isa gidan El-Ameen ya kira Iman da nmbr da Ummi ta basa, kanwar ta ce ta fito tayi masu iso har falo ta cika su da drink, mahaifiyarta ta fito suka gaisa ta bar palon, ba a dau lkci ba Iman ta fito sanye da wata doguwar riga me adon stone blue da gold, tayi rolling kanta da plane blue mayafin kayan, kyakkyawa ce ba kadan ba, ta karaso falon kamshin turarenta ya cika ko ina ta xauna, kallon Junaid El-Ameen yyi, Junaid ma ya kallesa, suka shiga kallan kallo, ganin El-ameen yaki cewa komai Junaid ya d’an yi gyaran murya yana kallonta yace “Ina yini Hajiya” amsawa tayi ba tare da ta kallesu ba, Junaid ya d’an taba El-ameen alamar yyi magana mans, a hnkli El-Ameen ya matso kusa da shi murya can kasa yace “Me xan ce mata plss” ae Junaid bae san lkcn da ya fashe da dariya ba, El-Ameen ya tsaya kallonsa sai shi ma ya saka dariyar, nan suka dinga dariya kamar tababbu suka yi me isan su suka yi shiru, Junaid ya shafa kai yana kallonta yana murmushi yace “Ehm dama Ummi ce tace in rako El-Ameen wajen ki…. Shine muka xo” El-Ameen yace “Eh Ummi ce tace in xo gurin ki shine ya rako ni” kala bata ce masu ba, Junaid ya mike yace “Toh shknn mu xa mu koma sai mun sake dawowa” El-Ameen ma ya mike yace “Eh xa mu koma, sae wani lkcn, mun gode kwarai” mikewa tayi tace “Allah ya kiyaye” daga haka ta haura sama ta bar su tsaye parlon, dariya suka dinga yi cikin motar barin Junaid, El-ameen ya ja motar suka bar anguwar daga karshe, sae da El-ameen ya kai kansa gida sannan ya fita suka yi sallama Junaid ya koma driver seat ya ja motar ya bar layin, yana isa inda mahaukaciyar take yyi parkin yana kalle kallen inda xae ganta daga cikin motar, sae bae bae ganta ba ya ja motar ya nufi gida. Yana jiran masu gadi su bude masa gate kiran mum dinsa ya shigo wayarsa, jan motar yyi ya shiga compound din ya nufi parkin lot yyi parking snn ya fito, ganin motar Abba yasa shi kallon agogon wrist dinsa ya ga har goma ya kusa, bangaren mumy ya nufa, tsaye ya sameta palo tana rike da wayarta ta rungume hannu, yyi murmushi yace “Ga ni na dawo Mum,” ta hade rai tace “Daga ina kake hka Ahmad?” Ya shafa kansa yace “na gaya maki Gidansu El-Ameen na tafi mum, na raka sa xance ne” yana murmushi ya k’are maganar, mumy tace “Zance! Lallai ba ayi abun arxiki ba kenan” dariya yyi lkci daya ya hade rai yace “Allah mum mun yi magana me ma’ana, infact ni ne ma nayi don shi shiru yyi wai kunya” Mumy tayi dariya tace “Au, kace ka kora masa budurwar knn in har kai kayi magana, tab!” Dariya shi ma yyi ya mata side hug yace “Kai Mumyna ni din ne ban iya magana ba” murmushi tayi tace “Kaje gun Abba yana neman ka” ya saketa yace “Ohk Mum” kofar da xae sada sa da part din dad dinsa ya nufa, xaune ya samesa babban falonsa yana kallon news lkci daya yana shan fruit salad din dake kan d’an table gabansa, Hajiya Fatee na xaune gefensa, sae step sisters dinsa su uku gaba daya suna palon, xaunawa yyi kasan lallausan rug din yana kallon Abbansa yace “Barka da dawowa Abba” Abba yace “Yauwa daga ina kake naga baka duty ae” yace “Naje gidansu El-Ameen ne Abba,” kallon Hajiya Fatee yyi yace “Ina yini Hajiya?” Tayi murmushin da bai kai ciki ba tace “Lfya lau, ya aikin” yace “Alhmdllh” Muhibbah ce ta shigo falon da sallama rike da bowl din kankana da akayi slicin, ta duka ta ajiye gefen Abba, xama tayi tana kallon junaid da ya maida hankalinsa kan Tv tace “Ina yini yaya” amsawa yyi ba tare da ya kalleta ba, Hajiya Fatee sae kallonsa ta gefen ido take, mikewa Junaid yyi yace “Sae da safe Abba” Abba yace “Yauwa ka ba Muhibbah dubu ashirin xa tayi amfani da su a makaranta gobe wae,” yace “toh Abba” daga nn yyi ma Hajiya Fatee sae da safe, kanninsa ma suka yi masa sai da safe ya fice daga falon rai a bace, mikewa Muhibba tayi ta bi bayansa, bae tarda mumy a palo ba, hka yasa ya nufi bedroom dinta ya sameta har ta kwanta, xauna wa yyi daga gefenta yace “Kin kwanta mum?” Tace “Har ka fito?” Yace “Eh mum” peck din goshinta yyi yace “Gudnyt mum, xan tafi in kwanta” tace “Toh Allah tashe mu lfya, make sure kayi alwala kayi addu’a kafin ka kwanta” yace “In’sha Allah mum” mikewa yyi ya kashe mata wutan dakin ya rufe mata kofa ya fita, dakin da kanninsa suke ya bude, Aisha ce ke waya ita ko Fatima tayi bacci, ya rufe kofar ya fito parlor, xaune ya tarda Muhibbah tana jiransa, yyi mamakin rashin ganin Hijab a jikinta don da hijab ta shigo palon Abba, kauda kai yyi ya fita daga parlon ta mike ta bi bayansa, yana isa part dinsa ya bude ya shiga ya juya yana kallonta ganin tana kokrin shigowa yace “Ki jira ni a nn malama” rufe kofar yyi, ta hade rae ssae tana kallon kofar, tsaki tayi ta bude ta shiga, ganin bae palon ta nufi bedroom dinsa, ya dauko kudin zae fito suka kusa cin karo, wani tsawa ya daka mata yace “Are yhu insane xa ki biyo ni daki” kallonsa ta tsaya yi, yyi tsaki ya bangajeta ya fice a fusace, bin bayansa tayi ba tare da ta ji haushi ko kadan ba, a palo ya jefar da kudin ya nufi kofa ya bude yace “Leave yanxu!” D’an tsaki tayi ta duka ta dauki kudin ta fice, ya kulle kofarsa ya sa key don wani mugun haushinta yake ji a gidan. K’asa bacci yyi daren ranan, duk juyin da xae yi sae mahaukaciyar nn ta fado masa, hankalinsa ne ya tashi don shi dae bae mata komae ba illah taimakon yaron da yyi, mikewa yayi daga karshe ya nufi bayi ya dauro alwala ya fito ya shimfida pray mat ya shiga nafila, sae kusan Karfe uku da rabi bacci ya daukesa. Da asuba ruwan sama ya sakko kamar da bakin kwarya, kmr jiya yau ma bae fita mosque sllhn asubahin ba sbda ruwa, ruwan dumi ssae ya hada yyi wanka don ko kadan bae son sanyi shi, ya shirya cikin uniform dinsa ya dauki babban kadigan na uniform me kalan Navy blue ya sa snn ya fito falo rike da rain coat dinsa, sae da ya tabbatar wayoyinsa na aljihun wandon uniform din jikinsa snn ya fito balcony ya saka rain coat din da hulansa ya nufi bangaren Mumy, a balcony ya cire rain coat din ya bude kofa ya shiga, tana kitchen da mai aikinta sai fatima suna hada breakfast, ya shiga kitchen din ya gaisheta ta amsa da cewa “Ka tashi lfya, ya ruwa?” Yace “Alhmdllh mumy” Fatima ta kallesa tace “Gud morning ya Ahmad” yace “Morning” ya fita kitchen din, tea kawae ya sha da kwae shi ma sae da mum ta takura sa wae ya makara xuwa aiki, har balcony ta rakosa tace “Baxa ka shiga gaida ‘yan gidan da Abba ba kenan” ya dan tsuke fuska yace “Am late mum,” tace “Toh Allah ya tsare” rain coat dinsa ya sa yace “Ameen” snn ya nufi parkin space, kusan a tare suka jero da Suhaima dake rike da lema tayi shirin makaranta, ko kallonta bae yi ba ya bude motarsa ya shige ta nufi tata motar tana kallonsa, jan motar yyi ya danna horn aka bude masa gate ya fice. A hnkli ya ke driving din har ya iso inda mahaukaciyar jiya take, samun kansa yyi da parking gefen titi yana kalle kallen inda xae ganta idonsa ya sauka kanta, xaune take cikin ruwan ta hade kai da gwiwa, duk ta jike da alama tun da ruwan ya sauko bata bar wajen ba, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujera yana ci gaba da kallonta, duk jikinsa yyi sanyi, da kyar ya iya jan motarsa ya bar wajen ganin yana bata lkci, shi mutum ne me tausayi da raunin xuciya kamar mace, har ya isa office bae da sukuni, colleagues dinsa duk suka lura da shi suka kuma tambayesa ko Lfya yace bai jin ddi ne, Karfe biyar saura ya bar gun aikin, driving kawae yake cikin rashin kuxari, bae bi hanyar da xae ga mahaukaciyar ba ya canxa hanya, ko parking din arxiki bae yi ba ya bude motar ya nufi part din mumyn sa, kwanciya yyi kan dogon kujera ya rufe idonsa gam, Mumy ce ta fito daga kitchen ganinsa a kwance tace “Lfya Ahmad” jin bae ce komae ba yasa ta karasa kusa da shi tace “Ahmad!” Bude idonsa da ya kada yyi ya mike xaune ya dafe kansa, taba jikinsa ta shiga yi da damuwa tace “baka da Lfya ne?” Lumshe ido yyi ya kwanta jikinta ta rungume sa tace “Talk to me mana son, me ya faru?” A hnkli yace “Kai ne ke man ciwo Mumy” tace “Ci abinci mu tafi asibiti” da sauri yace “No mum, xan sha magani” hade rai tayi tace “Wani maganin xa ka sha, sau nawa kke sha bae maka aiki ba, so kake ka dauko min magana gun Abba koh” shiru yyi ta mike ta nufi dinning ta dawo rike da kulan abinci da plate da spoon, fried rice din ta dibar masa ta ajiye snn ta koma kitchen ta hado masa tea, bae son mum din tasa ta daga hankalinta shi yasa ya daure ya dinga cin abincin don kwata kwata bae da appetite. Mikewa yyi da ya gama Mumy tace “Ka tafi ka canxa kawae mu tafi clinic” yace “Toh” snn ya fita xuwa bangarensa, wanka yyi ya canxa uniform din jikinsa xuwa kananun kaya, ya d’an kwanta yana tunanin karyar da xae ma Mumy ta hakura da xuwan su asibiti, dubara ce ta fado masa ya mike da sauri ya dauki wayarsa ta fita, xaune ya sameta palo ta shirya tana jiransa, murmushi yyi yace “Mumy ynxu El-Ameen ya kira ni, I told him m nt ok, shine yace I shud cum over ya duba ni” hararansa Mumy tayi tace “Yhu should come over dai kuyi hira, my frnd mu wuce clinic” marairaice mata yyi ya mata side hug yace “Haba mum, ga ni da amini likita kice mu je clinic, kinga baxae ji ddi idan ban je ba plss”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button