CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

By Khaleesat Haiydar✍????

49…..

Jasmine na haurawa sama ta bude kofar dakin Junaid ta shiga, xaune yake yana game da laptop, ya daga kai yana kallonta har ta karaso ta xauna kasa tana kallon game din tace “Irin na Saif” son din Dr Sumayya, jin Junaid bai ce komai ba ta daga kai tana kallonsa suka hada ido, sunkuyar da kai tayi, yace “Idan xaki shiga daki ki fara yin sallamah a amsa maki sannan ki shigo kin ji” dago kai tayi tana kallonsa da ganinta kasan bata gane abinda yake nufi ba, ya lumshe ido ya mike ya isa kusa da kofa ta bi sa da kallo, yana rike da kofar yace “before coming in, sai kin fara cewa Assalamu Alaikum, idan kika ji ance Wa’alaikis salam, sai ki shigo” shiru tayi tana kallonsa still, ya dawo dakin ya xauna yace “Say Assalamu alaikum!” Sunkuyar da kai tayi a hankali ta fadi, yace “Good, sai kinji ance maki wa’alaiki assalam sai ki shigo, tashi kije ki fadi in ji” mikewa tayi ta koma gun kofar ta tsaya a hankali tayi sallaman, girgixa mata kai yayi yace “No! Waje xaki ki tsaya ba nan ba” ta bude kofar ta fita tayi sallaman, ya amsa ta shigo kanta a kasa, kallonta kawai yake har ta iso inda yake bata dago ba, hawaye ya gani idonta, yace “Ohh kuka kike?” Bata ce komai ba kuma bata dago ba, ya d’an tabe baki yace “uncle din naki ya tafi kenan?” Ta girgixa masa kai hawaye na gangarowa daga idonta tace “Yace in kira Captain” kallonta kawai yake, cikin sanyin murya yace “Xauna” ta xauna kasa, yace “Kukan me kike?” Girgixa masa kai tayi bata ce komai ba, xai yi magana wayarsa ya soma ring, dauka yayi ya ga El-ameen ke kiransa ya ajiye wayar ya mike ya fita ta bi sa da kallo can ita ma ta mike ta bi bayansa. Tun daga stairs El-ameen ke kallonsa har ya sauko, ita dai Humainah kanta na kasa, Yana daga tsaye yace “Ya aka yi?” El-ameen yace “Am going” Junaid yace “Allah ya kiyaye hanya” jasmine na jin El-ameen yace going ta dawo kusa da shi da sauri ta durkusa tace “Uncle bag dina yana daki” ya langwabar da kai yace “Mami ai bata dawo ba baby, amma tace gobe xata dawo sai goben in xo in dauke ki koh” wani kuka ta fashe da tana kallonsa tace “Nooo” da mamaki yake kallonta ganin irin kukan da take, ta mike ta xauna kusa da shi ta kamo hannunsa tana kuka tace “Dont leave me plss Uncle, take me with you” ya girgixa mata kai yace “Toh ina xan kai ki baby mami bata nan, she’s coming back tomorrow sai in xo in dauke ki” ta fashe da matsanancin kuka har da bubbuga kafa tace “Nooo!” juyawa junaid yayi xai koma sama El-ameen da ya ma rasa me xai ce mata yace “Dalla kai kuma meye haka Ahmad magana xa muyi” junaid ya wani hade rai yace “Ka fadi abinda xaka fadi mana” mikewa Jasmine tayi tana kuka har lokacin tace “I want to go and bring my bag…” El-ameen ya hade rai yace “I will flog you fa,” cikin kuka tace “Nooo!” Humainah dai sai kallon ikon Allah take, El-ameen ya mike yace “You are telling me no koh, bari in nemo bulala yanxu, I will so flog you” dawowa kusa da shi tayi da sauri tana kuka tace “Plsss” ya nuna mata kujera yace “Toh xauna kar in mare ki yanxu, ki rufe min baki kuma” xaunawa tayi tana kokarin hadiye kukan, ya kalli junaid yace “Mu je” daga haka ya dau makullin motarsa da waya ya nufi kofa, ta mike da sauri ta fashe da wani sabon kukan tace “Uncle” ya hade rai yana kallonta yace “Koma ki xauna” komawa tayi ta xauna ya fita daga parlon, Junaid ya tabe baki ya bi bayansa, mikewa Humainah tayi ta haura sama, Jasmine ta dinga rusa kuka iya karfinta, sai da suka isa gun mota El-ameen yace “look junaid ka rage shige ma yarinyar nan tunda matar ka bata so, beside bai ma kamata ka fiffita ta kan matar ka ba, duka duka yaushe aka yi auren har xaka dinga shiga hakkinta haka, kawai yanxu a samo tsohuwar da xata dinga mata duk wasu abubuwan xai fi…..” Katse sa Junaid yayi yana masa wani kallo yace “Abinda nayi niyyar yi kenan or you take her out from my house tunda yanxu kam kafi kowa son kula da ita da nema mata lafiya on like lokacin da take kan bola, ni sai in cire hannu ma in bar ka da ita tunda na mata mai wuyar, you can take her to wherever you wish for all I care Ahmad” daga haka ya juya ya bar wajen, El-ameen ya bi sa da kallon mamaki har ya shige gate ya kulle, juyawa yayi xuciyarsa na tafarfasa ya shiga motarsa ya bar layin. Ko da Junaid ya shigo parlon samunta yayi tana ta rusa kuka, ko kallonta bai yi ba ya haura sama. Har magrib Jasmine na parlon tana kuka, ya sauko ya fita xuwa masallaci ba tare da ya kalleta ba, sai da Humainah taji fitarsa sannan ta sauko parlon, daga bakin stairs ta tsaya ta dake tace “Xo mu tafi sama” ko kallonta Jasmine bata yi ba, ta karaso cikin parlon tace “Mu je” Jasmine tace “Am not going” juyawa Humainah tayi ta koma sama abun ta. Bakwai da wani abu Junaid ya shigo parlon rike da leda a hannunsa, ajiye ledan yayi yana kallon jasmine yace “Je dauko jakar taki in kai ki gun sa” kallonsa tayi kamar bata gane me yace ba, ya hade rai yace “I said go and bring your bag” mikewa tayi tana goge idonta ta tafi sama, ba a dau lokaci ba ta sauko rike da jakar tana kallonsa tace “Ban ga daya takalmin ba” kallonta kawai yake, ya dake yace “Ina xan kai ki?” Tace “Wajen uncle” yace “Toh mu je” kofa ta nufa tana cewa “Na bar ma Antyn nan daya takalmin” ya bi ta da ido har ta bude kofa xata fita yace “Kehh!” Juyowa tayi tana kallonsa ya karasa inda take tsaye ya hade rai yace “Daga yau kika sake kira min uncle a gidan nn sai na baki mari” kallonsa take irin bata gane ba din nan, ya duka dai dai fuskarta yace “From henceforth, I mean from now on kar ki sake kiran uncle a gidan nan” fixge jakar yayi ya jefar parlor ya kamo hannunta ya shigo da ita ya rufe kofar ya saketa ya haura sama. Xube wa wajen tayi ta dinga rusa kuka har da shessheka, tana nan xaune ya sauko xai tafi masallaci yin isha, bai ko kalleta ba ya fita daga parlon, ko da ya dawo kitchen ya shiga ya dauko plate ya debi abincin da ya siyo daxu ya haura sama ya shiga dakinsa, bai iya ya ci abincin ba ya ajiye kawai ya koma kan gado ya kwanta duk ya rasa me ke masa dadi, tv ya kunna shi ma haka ya dinga kallon absentminded, bude kofar dakin aka yi Humainah ta shigo, ta tsaya daga kusa da gadon tace “Ka bani waya xan kira Abbana” ba tare da ya kalleta ba yace “ban da kati” kallonsa ta tsaya yi, can ta juya ta fice. Lumshe ido yayi ya bude ya dau wayar ya shiga kiran El-ameen, El-ameen dake kwance daki yana danna waya ya tsura ma sunan dake kan screen din ido har ya katse, aka kuma bugowa nan ma har ya katse bai daga ba, bayan kusan minti biyu text ya shigo masa, bude content din yayi ya karanta kamar haka “Just want to say am sorry, i get I wasn’t suppose to, but I dunno whatever happened wasn’t right, am just trying to say sorry…..” Screen d’in ya tsurawa ido har ya gama karanta text d’in snn ya ajiye wayar, indai Ahmad ne ya saba da halinshi na idc attitude, ajiye wayar yayi yaci gaba da abinda yakeyi, K’arfe take as Junaid ya fito, d’akin Humainah ya leqa yaga bata nan da alama toilet ta shiga, jan k’ofar yayi ya maida ya rufe ya sauk’o, kwance take k’asan tiles har ta gaji da kukan bacci ya soma d’aukarta, dab da ita ya k’araso ya k’urawa kyakkyawan fuskarta ido da Lashes d’inta suka kwanto kamar tayi fixing, sosai jikinshi yayi sanyi ganin har lokacin da d’an siririn hawaye shimfid’e a fuskan, a hankali yayi tapping jakarta da janyo ta mak’ale kamar wacce za a kwacewa yace “Jewel”, a hankali ta bud’e idonta tana kallonshi, ya sunkuyo daidai fuskarta yace “Wake up”, sai lokacin ta tashi da sauri tana k’are mishi kallo kamar yanzu ta soma ganinshi, tana son furta Uncle amma tana tsoro dan yayi warning d’inta da kada ta sake k’ira mishi wani Uncle, a hankali bakinta ke twitching hawaye na dad’a gangarowa idonta, ido ya rintse kawai ya kamo hannunta tareda janyota jikinshi ya rungume, ba shi ba har ita k’irjinta bugawa yakeyi, ido ta lumshe tana sauk’e ajjyar zuciya, cikin wata iriyar murya yace “am sorry Jasmine”, itadai shiru kawai tayi tana sauraronshi, a hankali ya janyeta daga jikinshi ya d’ago hab’arta yace “am sorry okay?”, yasa hannu ya share mata hawayen dake fuskarta, gaba d’ayanta yarinyar tausayi take bashi, mik’ewa yayi tareda kamo hannunta ya tayar da ita yace “Kinyi Sallah?”, kai ta girgiza mishi yace “kiyi min magana, don’t nod”, a hankali tace “banyi ba”, yace “Shiga kiyi alwala, I will b here waiting for you”, ba musu tayi hanyan toilet d’in dake palo, saida taje bakin k’ofa snn ta sake juyowa taga ita yake kallo kamin ta shige toilet d’in, yana zaune ta fito ta d’auki hijab d’inta dake gefe ta saka, har ta idar da Sallah idonshi na kanta yana observing yanda take Sallahn, ta d’an jima zaune bayan ta idar snn ta kalleshi tace “Av prayed, nace Allah ya bani lafiya”, kai ya kad’a yace “that’s good, kullum ki dinga yin haka kinji?”, tace “toh”, ya mik’e yana maida wayarshi aljihu yace “zaki rakani?”, kallonshi ta tsaya yi da manyan idonta kamar batasan mey yace ba saida yayi murmushi snn yace “I mean would you like to go out with me?” Har zatayi nodding kanta tayi maza tace “Toh”, yace “Good saka Hijabinki mu tafi”, tana gama sawa ta dubeshi da manyan milky eyes d’inta tace “Shoe d’ina ban ganshi ba kuma nace na barwa waccan Aunty”, kallonta yayi kawai yace “muje, we will buy another one”, lokaci lokaci yake juyowa ya kalleta yana driving, itakam kanta ta jingina jikin glass tana ta kallon garin, a Jifatu yayi parking, ce mata yayi ta zauna ta jirashi ya shiga ya gama siyayyan da zaiyi snn ya fito, takalmin da ya mik’a mata ta saka tana jin dad’i snn ya wuce dasu Royal Joint, a nan yayi musu order abinci suka wuce gida, hannunshi riqe da abincin da ya siyo ita kuma riqe da na shoe d’in da ya siya matan, suna shigowa gida daidai nan Humainah na sauk’owa kan bene, wani irin fad’uwa, da murna Jasmine ta kalli ledan shoes dake hannunta snn ta kalli Humainah dake tsaye tace “Aunty kinga new Shoe d’ina da wannan Uncle d’in ya bani, he is nice, kema kice mishi kinaso ya baki”, Humainah dake tsaye gabanta na bugawa juyawa tayi ta koma d’aki, Jasmine ganin ta tafi yasa ta juyo da kallonta ga Junaid da yake kallon inda Humainah tabi, tace “Aunty nan ma A siya mata irin shoe d’ina”, kallonta kawai yayi yace “Jeki d’auko plate”, ledan da yake hannunta ta ajiye tayi kitchen, zaune ta tarar dashi yana danna waya, d’agowa yayi ya dubeta ganin ta tsaya mishi a ka yace “Sit down and serve yourself the food”, zama tayi ta janyo leda d’aya ta bud’e ta shiga zuba fried rice d’in a plate ta fara ci, tashi yayi ya d’auki d’ayan ledan ya haura sama dashi, d’akin Humainah ya tura duk wutan d’akin kashe yake, kunnawa yayi ya k’arasa shigowa, a tsakiyan gadon ya ganta kwance ta dunqule waje d’aya, zama yayi bakin gadon bayan ya ajiye ledan hannunshi, sau biyu yana k’iranta yajita shiru, a hankali ya d’agota dan yasan ba bacci take ba, fuskarta da ya kumbura dan kuka ya k’urawa ido , hannu yasa ya shafi hawayen yana murzawa da d’an yatsanshi yace “Sana’ar da kika samu kenan yanzu?”, turashi ta shiga yi daga jikinta, firmly ya riqeta, ganin ta kasa kwace kanta yasa ta fashewa da wani irin kuka tana sulalewa k’asa tace “ni ka sakeni ka fitamin daga d’aki”, har ranshi yakejin kukan nata, d’agota ya sakeyi yace “Humainah mey ke damunki wai for crying out Loud?, me kike so?”, shiru tayi mishi taqi cewa komai tana ci gaba da kukan, a hankali ta d’ago tana share hawayenta tace “Ka maidani gidanmu, inason ganin Abba na”, wani irin kallo ya bita dashi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button