CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske writers association
[3/19, 9:36 PM] El-hajj????: ⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

81

Still Zahrah tayi ganin kanta xaune a wani parlor kasan rug, doguwar riga ce jikinta da hula a kanta, Junaid ta gani tsaye parlon yana danna waya can ya karaso ya xauna kujera, gani tayi ta juya tana kallonsa, shi ma kallon nata yake can ya ci gaba da dannar wayarsa, wata dattijuwa ce ta shigo parlon tana isowa gabanta ta xauna ta ajiye plate din hannunta me dauke da potatoe da ketchup, dattijuwar ta dau potatoe daya ta dangwala da ketchup din ta kai mata baki, taga ta karbe daga hannunta tana jujjuyawa can ta Kai baki ta lashe sannan ta mayar mata, tuni hawaye ya cika idon Zahrah, Junaid dai kallonsu kawai taga yake, dattijuwar ta jawo ta jikinta ita ko tayi lamo, saukowa junaid yayi ya dau dankalin ya kai mata baki ta kauda kai da sauri ta dinga shigewa jikin dattijuwar, ya tabe baki ya ajiye, Suna ta xaune a haka sai ga El-ameen ya shigo parlon, kallonsa kawai Zahrah take ko kiftawa bbu, farar 3 qtr ne jikinsa sai blue polo kallo daya yayi ma junaid ya karaso ya durkusa gabansu ita da dattijuwar ya ajiye ledan hannunsa, ba a dau lkci ba dattijuwar ta mike bayan ta xaunar da ita ta bar wajen, taga El-ameen ya xauna gabanta ya dago kanta yana kallon fuskarta ita ma kallon nasa take, Junaid dai bai ko kallesu ba waya kawai yake kallo, murmushi me kyau El-ameen ya mata taga ya lakaci hancinta ita dai idonta na kansa, dankali ya dauka ya dangwali ketchup ya kai mata baki ta kauda kai, hade rai taga yyi ya rike kanta ya kai dankalin bakinta, a hankali ta ga ta fito da harshe ta lashe ketchup din, dariya ta ga ya fara yi yana kallon junaid da yaki kallon inda suke, Zahrah bata san lokacin da tayi murmushi ba hawaye na sakko mata, taga ya kuma dangwala ya kai mata ta lashe, xaro ido tayi ta rike breathe ganin ya kai dankalin baki, sai kuma ya kalli Junaid da sauri yaga ba kallonsu yake ba, sosai jikinta yayi sanyi ta kasa daina kallonsa wasu sabbin hawayen na xubo mata, gani tayi junaid ya mike ya fice daga parlon, El-ameen ya jawo ledan da ya shigo da ya bude ya fiddo da magunguna da hollandia yoghurt, ya jawo cup din dake wajen ya bude drink din ya xuba ciki sannan ya dauka ya kai mata baki ba musu taga ta bude bakin tana sha har ta kauda kanta daga karshe, kadan ya sha ya ajiye cup din ya mike ya bar wajen, gani tayi ta jawo cup din ta juya upside down, drink din ya malale a gun har a jikinta, El-ameen ya karaso wajen yana kallonta, can ya hade rai ya durkusa ya ja hancinta, hannu tasa ita ma tayi yanda yayi sai kuma ta ja nasa hancin shi ma, murmushi Zahrah tayi ta lumshe ido, can ta bude a hankali, magani taga ya kada a cup ya kai bakinta, ba musu ta bude ya juye mata, ta shiga yamutse baki ya ciro handkerchief a aljihunsa ya goge mata bakin ya mayar sannan ya mike, Datijjuwar daxu ta ga ta dawo, shi kuma ya bar parlon, dattijuwar ta daga ta bayan ta dauke cups din gun suka bar parlon. Haka Zahrah ta dinga kallon irin rayuwar da tayi a baya, duk jikinta yayi sanyi sosai banda hawaye bbu abinda take, wani gun tayi murmushi wani kuma tayi dariya, tunanin da me xata biya dattijuwar nan ta dinga yi, har inda take xata so a kai ta, wani tausayin El-ameen ta ji dinga ji har cikin ranta, ashe haka yayi hidima da ita, ta ga dai kafin ta ga kanta tare da Junaid sau daya ta ganta da El-ameen sau goma, kuma taga junaid da ya shigo bai wuce minti biyar sai taga ya fita kuma kullum fuska a daure barin idan El-ameen na gun, a wani gu ne ma da El-ameen baya parlon taga ya xauna gabanta har ya dago kanta yana kallonta, can kuma ya mike ya koma kujera, gajiya Zahrah tayi daga karshe ta kashe laptop din ta koma ta kwanta a sanyaye, kasa bacci tayi daren ranan tunanin El-ameen take? na junaid ne? Duk ta kasa tantancewa da kyar ta samu bacci ya dauketa sai dai har asuba mafarkan junaid kawai take, tana idar da sllh bayan ta tafi ta gaida Abbanta da Umma ta tafi bangaren Kilishi ita ma ta gaida ta, Ummi ta shiga nema ta ganta bedroom din Kilishi ta ja ta suka fita ta koma part dinta da ita, Ummi tace “Ohh sis bacci fa xan koma” suna shiga bedroom Zahrah ta xaunar da ita ta ciro laptop dinta dake charge ta ajiye gaban Ummi tace “Idan kin gama kallon nan akwai tambayar da xan maki” daga haka ta kunna mata ta fice daga dakin, da farko Ummi kamar ta kashe laptop din tayi kwanciyarta sai dai hango yar uwarta da tayi a xaune ya sa ta bude ido daga nan kuma ta maida hankalinta gaba daya kai. Takwas saura Ummi ta fito parlor ta samu Zahrah kwance idonta lumshe alamar bacci take, jiki a sanyaye ta karasa ta xauna kusa da ita ta dafa ta cikin sarkewar Murya tace “Sister!” Bude ido Zahrah tayi da sauri tace “Ahmad!” Sai kuma ta maxa ta mike xaune tana kalle kalle, kallonta kawai Ummi ke yi, murya can kasa tace “Ahmad?” Zahrah da duk ta daburce lokaci daya tace “Ohh, Ummi, kin gama kallon ne” Ummi ta share hawayen fuskarta tana murmushi tace “Yeah and I love it Zahrah, I love it… Xan kai ma su Abba su ma su kalla….” Tana magana ne hawaye na xubo mata, Zahrah da ita ma hawayen ya cika idonta a hankali tace “but ina son in maki tambaya!” Ummi ta kalleta tayi mata murmushi tace “Ina jin ki My sis” Zahrah ta sauke idonta kasa tace “Between the two of them, waye ya ci ace baxan mance ba har karshen rayuwata, nd who deserve me?” Kallonta kawai Ummi ke yi, can tayi murmushi a hankali tace “My Dad! El-ameen… He soo deserve you sis, he gave you all his time, he took care of you, bai kyamace ki ba, bai kuma taba gajiya da ke ba…..” Kuka sosai Zahrah ta shiga yi tana kallon yar uwarta, Ummi da jikinta yayi sanyi tayi shiru tana kallon ta ita ma, cikin rawar Murya Zahrah tace “Toh shi Ahmad fah?” Ummi ta sauke idonta kasa a hankali tace “Yeah yayi maki kokari sosai shi ma, just that na lura shi ba mai son hayaniya bane, sannan miskiline, kuma na lura bai son yanda El-ameen ke yi maki, sai naga ma kamar kishi yake duk da baya cewa komai, indai El-ameen na parlon naga baya xama sai kawai ya fita, idan kuma ku biyu ne kadai ya kan xauna kusa da ke, sai dai kuma baki saki jiki da shi yanda kika yi da El-ameen ba, bai kuma san ma yanda xai kula da ke ba” Zahrah ta jinginar da kanta jikin kujera ta lumshe ido, Ummi ta kamo hannunta tace “El-ameen na son ki sosai Zahrah, duk da halin da kike ciki bai kyamace ki ba don har abinda kika kai baki yana ci…..” Zahrah ta bude ido tana kallonta, murmushi ta kirkira tace “Yeah na gani” Ummi tayi murmushin ita ma ta mike ta dau Laptop din ta fice tana cewa “I just love this sweet sis, xan kai ma Abbanmu….” kuka sosai Zahrah ta fashe da bayan fitar yar uwarta, ita kanta ta rasa kukan me take ta mike da gudu ta shiga bedroom ta fada kan gado ta dinga rera kukan. Da kyar Junaid ya iya fita masallaci sallahn asuba, yana dawowa kuma yayi kwanciyarsa nan parlor kan kujera don bai jin xai iya fita aiki, ya rasa gane xaxxabin me ke son rufe sa, mikewa yayi daga karshe ya koma sama yayi wanka ko xai iya xuwa aikin, kamar kar ya fito ya ji wani sanyi na shigarsa duk da ba da ruwan sanyi yayi Wankan ba ma, ya dade kwance cikin bargo kafin ya mike ya shirya cikin kananun kaya ya dau makullin motarsa ya fita, gida ya nufa yana gama parking ya fito ya tafi bangaren Mumy kansa na sara masa, fatima ce xaune parlor da Humainah da khadija, bai iya ya amsa gaisuwar da suke masa ba ya shiga dakin Mumy, bbu kowa dakin ya kwanta kan gadon, bai yi minti biyar da kwanciya ba Mumy ta shigo, tsaye tayi bakin kofar tana kallonsa can ta karaso kusa da gadon tace “Ahmad!” Bude ido yayi yana kallonta, hannu ta daura forehead dinsa tace “Are you sick?” Mayar da idonsa yayi ya lumshe yace “Just headache mum” mikewa tayi ta fita sai ga ta ta dawo da cup din tea tace “Tashi ka sha shayin sai in baka Magani” ba musu ya mike xaune ya karba cup din ya shiga shan tea din, kadan ya rage ya ajiye, Mumy ta dauko masa paracetamol da ruwa a cup ta mika masa, ya karba ya hadiye maganin, tsaye tayi tana kallonsa don ta ma yi mamakin da ya karba maganin, mikewa yayi da sauri tace “You better don’t do that….” Tsayawa yayi da farko yana yamutse fuska ta galla masa harara, sai kuma ya shige bathroom sai amai, tana nan tsaye har ya fito, bai bari sun hada ido ba ya koma ya kwanta ya lumshe ido, tace “Sai ka tashi mu tafi asibiti, saura in mun je ka gudo” girgixa Kai yayi cikin sanyin murya yace “Wllh bacci nake ji Mumy jiya ban yi bacci ba, idan na tashi sai mu je” ta kusa minti biyar tsaye tana kallonsa bata ce komai ba, har ta ga alamar bacci ya fara daukarda, karasawa tayi ta dau wayarsa ta sa masa a silent ta ajiye sannan ta fita. Sai kusan karfe sha biyu junaid ya farka da wani matsanancin ciwon kai, da kyar ya mike xaune, El-ameen ya gani dakin xaune yana hada drip ga injections a gefe guda, El-ameen ya sakar masa murmushi ya mike yace “You are awake!” Dauke kai junaid yayi yana kokarin mikewa, El-ameen ya xauna ya riko hannunsa yace “What’s wrong with you, lafiya muka rabu jiya fa?” Junaid ya dake yace “ce maka aka yi bani da lafiya?” El-ameen yace “Yeah, Zahrah ma na son gaishe ka wai, I told her you are sick” daga haka ya jawo wayarsa, wani kallo junaid ke yi masa xuciyarsa na tafarfasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button