CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske writers association????
[3/19, 9:36 PM] El-hajj????: ⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

76……

Tsaye yayi bakin kofa yana bin kowa na parlon da kallo irin na mamaki, ido hudu suka yi da Zahrah dake kallonsa ko kiftawa babu, hade rai yayi ya juya xai fita El-ameen dake tsaye har lokacin ya kama hannunsa yana kallon Sarki da shi kansa kallon Junaid yake yace “Ahmad junaid kenan, kuma dominsa ku ka taho katsina.” Mikewa Hajja tayi da sauri tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Me yayi? Yaron da ko hanyar bauchi na san ko xa a kashe sa bai sani ba, ashe kai mugu ne Aminu ba mu sani ba….. Meye hadin jikana da masarautar Bauchi can kace ko ina?” Abokin Abba ne yace “A’a Hajja ba tashin hankali bane, ae ba mu jira mun ji me ke tafe da su ba, kuma ko gaisawa fa ba a yi ba, sannan ance sarki ne nan gabanmu ba fa waxiri ba…..” Wani kallo ta watsa masa A fusace tace “Yo ni ina ruwana da sarautarsa, ka gan ni nan ban tsoron kowa sai Allah, kuma bbu irin fitintinun da ban gani ba a duniya, ya fadi me jikana yayi masa in ji, Ahmad da ko titin da xai kai sa Bauchi bai sani ba” Abba dai kasa cewa komai yayi, don shima jiran jin me only son din nasa yayi kawai yake, Sarki kam banda murmushi babu abinda yake sai dai ba lallai ka gane murmushin ma yake ba sbda turban din kansa, Aminin sa da shi ma ya samu gu ya xauna gefensa cikin kaushin murya yace “Mind you all, ba fa karamin mutum bane xaune a gaban ku, sannan mu alkhairi ne ya kawo mu in’sha Allah, Mai martaba sarkin bauchi kenan da kansa don haka a samu nutsuwa don Allah…..” Hajja tace “Ina xa mu samu nutsuwa ba ku fadi me ke tafe da ku ba, ni dai nasan Ahmad ko cinnaka baxae iya kashe wa ba….” Sarki ya kalli Junaid yace “Toh karaso ka xauna Ahmad” tsaye junaid yayi kamar baxai karasa parlon ba gashi gabansa sae faduwa yake ya rasa dalili, sarkin bauchi kuma, is she related to the royal family? Abba ne yace “Ka kasa tahowa ke nan?” Da kyar ya d’aga kafa ya karaso ya xauna nan tsakar parlon Hajja ta xauna gefensa tace “Kwantar da hankalin ka Amadi bbu wanda ya isa ya cutar da kai matukar ina raye a doron kasa, su fadi me kayi in ji” tana magana ne tana matsar kwalla, Abba ya kalli El-ameen yace “Tafi ka kira Amina” juyawa yayi ya fita ba a dau lokaci ba ya dawo parlon tare da Mumy, k’in xama Mumy tayi ta kalli junaid ta kalli Sarki sannan Abba, Sarki ya kalli Zahrah da ke xaune daga kasa kusa da shi, sannan ya kalli Junaid yace “Kasan yarinyar nan?” Junaid ya daga kai yana kallon kwayar idonta, Sunkuyar da kai tayi da sauri ta dalilin faduwa da gabanta yayi, sai da sarkin ya kuma nanata tambayar sannan ya gyada kai kawai, Hajja da ko k’adan bata gane Zahrah ba ta yo waje da ido tace “A ina ka santa don ubanka?” Kallonsa kawai sarkin ke yi, a ransa kuwa tunani yake anya shi din El-ameen ya basa labari jiya, da irin fadin ran nan ya taimaki ‘yar sa kenan, A fili kuwa cewa yayi “Toh a ina ka santa Ahmad?” Kallon El-ameen Junaid yayi yace “Shi ma ai ya santa, ya ma fi ni saninta” Hajja ta mike tace “Atoh a hankali gaskiya dai xata bayyana don ni nasan jikana bai santa ba sai dai abokinsa” Aminin sarki ne yace “Ahmad kake koh? Toh kasani ba karamin mutum bane nan gaban ka, am repeating this, you go straight to the point and answer his questions right away, takanas ya taso tun daga bauchi domin ka don haka kar ka maida mu kananan mutane” Mumy ji tayi ta kasa tsayuwar ma, da kyar ta samu waje ta xauna tana kallon ikon Allah, Junaid kam dama ba direction dinsu yake kallo ba, Sarki ya nisa yace “Ahmad, ni ne Mahaifin Zahrah, ka kuma min abinda har karshen rayuwata baxan taba mancewa da kai ba, ka dawo min da farin cikina ka fitar da ni kunci lokaci daya, ashe har yanxu akwai sauran mutanen kirki a duniya? ashe akwai masu xuciya irin taka a duniya, kaf rayuwata ban taba jin na kaunaci mutum kamar yanda naji kaunar ka daga jiya ba, da kai na kwana a raina jiya Ahmad…..” Hajja sai wuwwulla ido take tana jiran jin me yayi ma sarkin, Sarki yace “Xan so ka ban labarin yanda ka ga Zahrah har ixuwa jiya Ahmad” k’in dagowa Junaid yayi da farko can ya dago suka hada ido da sarkin sai yaga yayi masa kwarjini, da kyar ya iya cewa “Nayi xaton El-ameen ya fadi maku ranka shi dade” Sarki yayi murmushi yace “Ehh, amma xan so sake jin labarin daga bakin ka” Junaid ya shafa kansa ya kalli Abba dake kallonsa, sannan ya dauke kai, xaunawa Hajja tayi tana jiran jin labari ita ma, Kamar baxae ce komai ba sai kuma cikin sanyin murya yace “It all happened on a faithful tuesday evening…..” Lumshe ido yayi ya bude ya shiga ga bada labarin tun daga ranan da ya fara ganin Zahrah a gefen titi, bbu abinda ya canxa daga wanda El-ameen ya fadi ma sarkin jiya, yanda ya kama mata gida da farko daga karshe kuma suka koma gidan El-ameen, irin hidima da wahalhalun da suka yi shi da El-ameen a kanta, da yanda suka boye ma iyayensu, mama jummai da suka dauko…. kai bbu abinda ya boye har gida da ya kawota da nufin aurenta da yanda iyayensa suka gane ba mai hankali bace….. Bbu wanda jikinsa bai yi sanyi ba a parlon, Hajja ta rushe da kuka tace “Ae dama nasan jikana yaron kirki ne, Allahu Akbar, xaka aikata fiye da haka ma don k’akan ka ka gado ” sunkuyar da Kai Junaid yayi ya kasa ci gaba don dama yanda yake bada labarin kamar bai son yi, Aminin sarki ne yayi Encouraging dinsa da ya ci gaba don sarkin kasa cewa komai yayi banda ido da ya tsura masa, Zahrah kam banda kuka babu abinda take jikinta yayi sanyi ba kadan ba, ita kanta Mumy hawayen ne ke sakko mata, cikin sanyin murya junaid ya ci gaba yace “I had to take her away….. muka bar gidan and…..” shiru yayi kafin ya fadi yanda suka yi hatsari bayan barinsu gidan wanda shi ne dalilin dawowan hankalinta sai dai kuma tayi losing memory ta mance komai, bai boye yanda ya janye jikinsa daga lokacin bisa umarnin da iyayensa suka basa, ya fadi yanda ya bar ta da El-ameen bai kuma bi ta kanta ba, El-ameen kuma ya kai ta gidan Course mate dinsa tayi kusan wata biyu a can, a watannin ta biyu a gidan sau daya yace yaje daga nan kuma bai sake komawa ba, har aka yi aurensa da Humainah, ya fadi shawarar da El-ameen ya basa da yanda ya amince ya maidata gidansa da xama gaba daya ya kuma sa ta a islamiyya, bai boye irin matsalolin da suka dinga fuskanta da Humainah a kanta, ya kuma fadi dalilin sa na sakin Humainah, bai rufa komai ba kan irin xaman da suka yi da Zahrahn bayan barin Humainah gidan har ya kai karshen labarin da fadin dalilin dawowar memory dinta, sai da idon kowa ya kawo a parlon, ya kusa minti biyar kansa a kasa kafin ya dago a hankali, hawaye ne cike idonsa ya mike ya isa gun Mumy ya durkusa ya daura kansa a kafarta a sanyaye yace “Ki gafarceni Mumy, nasan nayi disobeying din ki, na kuma boye maki abinda nayi which I wasn’t suppose to ko da kuwa baxa kiyi supporting dina ba shi yasa komai bai tafi min dai dai ba, forgive me plss Mumy…..” Hawaye kawai Mumy take bata iya ta ce masa komai ba, ya mike ya isa gun Abbansa shi ma ya durkusa gabansa hawaye na sakko masa yace “Ka yafe min Abba, I know I… I failed you…..”Jin Abba bai ce komai ba yasa shi mikewa a sanyaye, tashi sarki yayi ya taka har gabansa ya dafa sa sai kuma ya rungumesa yace “They will all forgive you in’sha Allah son, sannan ina me umartarka da ka mayar da matarka ka nemi gafararta…..” Daga haka ya sake sa ya isa gaban Abba yace “Ina neman alfarmar ku yafe ma Ahmad duk abinda ya maku a kan Zahrah….” Murmushi Abba yayi ya mike yace “Bai min komai ba mai martaba, Allah ya basa ladan abinda yayi, ina alfahari da kasancewarsa d’ana, yasan ba lallai in sauraresa ba a lokacin shi yasa yayi komai gaban kansa, Allah ya biyasu gaba daya da abokin nasa, is good thing sun riketa amana, ta kuma samu lafiya ta dalilin su, I am proud of them…..” Mikewa Mumy tayi a sanyaye xata fita Sarki yace “Toh Hajiya bamu ji kin ce kin yafe masa ba, ina nema masa wannan alfarmar don Allah” murmushi kawai tayi, Hajja da baki ya ki rufuwa tace “Yo wa ya sani ko bakin ciki take masa kamar yanda matan ubansa ke masa, ni dama tun ran da Amadi ya kawo yarinyar gidan na daura ido na kanta na ji ta kwanta min toh tunda yan gida suka ce mahaukaciya ce basu san xance ba ina ni ina magana ace don ba ni na haifesa ba” kallonta kawai junaid yake haka ma El-ameen dake murmushi, sarki yayi murmushi shi ma yace “Da fatan mun kafa xumunci kenan har illah maa’sha Allah” Hajja ta mike da sauri tace “toh ni makka xaka kai ni, shekarana uku rabona da can wllh” ‘yar dariya sarkin yayi yace “Kina da kujeru biyar wannan shekarar Idan Allah ya yarda” shewa tayi tace “Allah yayi maka albarka…… Sai mu je tare da Humainah da kawayena Uku” kofa junaid ya nufa xai fita daga parlon sarki ya kirasa, juyowa yayi yana kallonsa, sarkin yace “Ina gayyatar ka masarautar mu tare da El-ameen, ur labours will not go in vain” Shiru Junaid ya d’an yi sai kuma yayi kasa da kai yace “Sai na dau excuse gun aiki idan Allah ya yrda” Kai kawai sarkin ya gyada masa, Satan kallon Zahrah yayi ya juya ya fice, kamar warce aka tsikara ta mike ta bi bayansa da sauri.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button