CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Muna jin Umma lokacin da take fad’in”to ubanwa zai aureta wanne d’an iskarne zai auri wacce tayi cikin shege idan banda ma ta rainawa mutane wayau har tace batasan CIKIN WAYE?ba yo naga dai cikin nan ba’a ruwa ake shaba balle tace a ruwa tasha,
Ba wanda ya kulata daga ni har Abba,samun guri mukayi muka xauna a farlour,”Abba ya kalleni cike da tausayi yace”Naanah kici gaba da hakuri don Allah na rasa gane kan mahaifiyarnan taku kina gani dai nima ba lagamin tayi ba balle ku yaranta,kuka kawai nake ina dafe goshina,shima Abba ya dafe kai cike da damuwa yace”wannan wacce irin k’addara ce,Naanah Allah ya jarabceki da jarabawa iri da iri amma idan kikayi hakuri kikaci jarabawar da Allah ke miki nan gaba nasan zakiji dad’in rayuwarki kiyi hakuri addu’a itace makamin mumini ki dage muma munataya ki,
Kwantawa nayi jikin Abba ina kuka maganar kanta ta gagareni,addu’a yake min yana tofamin,
Hajiya kuwa bayan ta koma gida tasanar da Zainab da Marwan abinda Umma ta mata ko Naanah bata bari ta ganiba,Zainab ta fashe da kuka yayin da Marwan ya hasala yace”Hajiya wannan wacce irin muguwar matace ki bani dama yanzun na kira hukuma ta shiga cikin wannan lamarin,girgiza kai tayi”Marwan mubi abin nan a hankali ni kaina matarnan na bani mamaki da takaici wallahi da k’yar idan ita ce ta haifi Naanah,kuma inaga idan d’iyar ‘yan uwanta ce idan sukaga abinda take mata zasu amshi d’iyarsu k’ila dangin Abbansu ce shiyasa take mata haka,
Cikin kuka Zainab tace”yanzu ko Naanahr bata bari kin gani ba kodai ta kashemin aminiya ne,tace”haba dai duk rashin imaninta ai bata iya kasheta ba,Marwan yace “wannan muguwar matar meye bazata iya ba,kawai ki bari inkira hukuma,Hajiya tace”karka kuskura ka fara duk abinda tayi kanta wata rana sai labari,haka Marwan ya fita cikin 6acin rai,Zainab kuwa ta kwanta jikin Hajiya tana rarrashinta
Yah Ameen ne na hango yana ta harhad’a kayayyakinsa da muhimman takardunsa na aikin da yayi a k’asar,sauri-sauri ya ke komai da alamar ana jiransa ne,rataya jakar yayi ya fito wata Taxi ya fad’a,yana zuwa filin jirgin kuwa yaji ana kiran suna yana jin sunansa ya nufi matattakalar jirgin yashiga,ba a wani d’au lokaciba jirginsu ya cilla sararin samaniya,sukayo kasarsa ta gado wato Nigeria……
Please sharhi nakeso,hakan zaisa na gane kuna gane inda na dosa,
Muje zuwa????
Fateenku ce????
Ummu Affan✍????
????CIKIN WAYE?????
❤❤❤❤
❤❤
❤
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
MAMAN PHATYMAH ZARAH
Uhm Umma akwai ranar kin dillanci ai,ki kara hakuri naanah duk tsanani sauki na nan zuwa,gaskiyarki Hajiya da danginta ne ai bata haka,amma dai muna biye don warware mata zare da abawa mungode MARYAM
Wow luv u littafin CIKIN WAYE?gaskiya kin samoshi sister sosae,tau kenan naanah kinga takanki nidai ina tunanin ba uwarki bace akwai magana amma ba uwar da ta haifeta bace,tau ga yaya Ameen xuwa ko yaya zata kaya idan yaga Naanah a wanga hali muje zuwa Allah ya kara zakin hannu amin muna godiya,
FIRDAUSI JANAIDU
Wayyo Naanah Allah ya baki ikon cinye jarabawarki ya kareki daga sharrin Umma da Rahma.
Gaskiya dad’in sharhin da kukaimin yasa na sakoko cikin page din nan,sannan na sadaukar da shi gareku,ina yinku irin sosai din nan????
Bismillahir rahmanir rahim
????3⃣3⃣-3⃣4⃣
????Misalin karfe biyar na yamma jirginsu yah Ameen ya sauka,Daddy da Momy ne sai direba sukazo tararsa,yana sakkowa ya nufosu sai washe baki yake yana jin dad’in yadda Daddy da Momy suke sonsa ko d’an cikinsu ne shi sai haka,
Jikin Daddy ya fad’a yana murmushi “Daddy na sameku lafiya,yace”lafiya k’alau my son sannu da k’ok’ari,”yauwa,ya amsa ya kalli Momy”Momyna ya kike,”Lfy qlau my son,ta amsa masa cikin nuna kulawa,gaba d’aya suka rugund’uma sai gida,
Abinci kala-kala ya iske Momy ta tanar masa,ya kalleta cike da k’auna irin ta d’a da uwa yace”Momyna sannu da aiki duk ni d’aya,murmushi tayi tare da shafa kansa tace”my son kafi gaban haka,ya rungumeta”ina godiya momyna,gaba daya sukayi dariya,
Bedroom d’insa ya wuce wanka ya fad’a toilet bayan ya fito ya shirya cikin k’ananun kaya jeanse da t-shirt,sosai yayi kyau,fuskarnan tasa sai annuri ke fita,
Farlour ya dawo ya iske su Momy na jiransa,dinning table suka nufa,harda Freeda wacce tazo takanas domin Ameen,d’iyace gurin k’anin Daddy suma nan cikin gari suke Malali GRA,sosai take k’aunar Ameen irin sosai d’innan,budurwace cikakkiya tana kimanin shekaru ashirin da biyar ta mace akansa inda harta kasa 6oye son Ameen dake ranta ta fito fili tasanar da shi haka iyayenta da su Daddy duk sunsan da zance,shi kuwa Ameen ko ajikinsa wai an tsikari kakkausa a salima ya tsani Fareeda saboda rawar kanta yayi yawa,’yar gata ce ta sosai mahaifinta yana da kud’i sosai nakece misali,shi da yayan nasa ma sai karasa gane wanne yafi wani kud’i,Fareeda tana karatunta a jami’ar jahar Kaduna(Kaduna State University)KASU tana karantar fannin jarida MASS COM.su hudu ne gurin mahaifinsu Fareeda ce babba sai Sayyed sannan Fahat sai k’aramarsu Autarsu Firdausi,sun taso cikin gata da soyayyar iyayensu,sun basu ingantacciyar tarbiyya da ilmi saidai Fareeda ta kasance daman ko a gidansu batada mutumci musamman idan kai talakane ta tsani talaka ko ‘yan aikin gidansu hakuri suke da ita amma sam bata da kyirki ga wulak’anci da izgilanci,tun ranar da tafara ganin Ameen taji ya kwanta mata irinsa ne namijin da takeson aure ingarma,
Bata da kunya nan take tace”gaskiya Ameen kayimin irin kane mijin da na dad’e ina jira,mamaki maganarta ta basa ya wani mata kallon baki da hankali ko amsa ya kasa bata kunsan abunku da miskili,nan tacikasa da surutu harda tsara musu irin rayuwar da zasuyi idan sunyi aure(INA RUWAN DAGA GANIN SARKIN FAWA SAI MIYA TAYI ZAK’I),
Ganin zata basa ciwon kai ya tashi yabar mata wajen,tun daga ranar ta tsari zuwa gidan bayan ada sai ta shekara batazo ba,saida ya taka mata burki ta rage zuwa gidan ta matukar tsoron yah Ameen don ko kallonta yayi sai tajia jikinta amma tak’i kiyayarsa acewarta batajin zata iya rabuwa da shi,kuma tayi alk’awarin ko ta halin k’ak’a sai ta auresa,
Itace ta zubawa kowa abinda yakeso,kallon Ameen tayi cikin murmushi,”my luv me kake so,yi yai kamar baiji abinda take cewa ba ya kawar da fuska,Momy ce ta tashi ta zuba masa tana hararar Fareeda don Allah ya gani ba k’aunar halayen nan na Fareedar take ba,ita bama ta k’aunar Ameen yace ya auri Fareedar yarinyar da bata da kunya ko kad’an,hakan da Momy tayi ba k’aramin k’onawa Fareeda rai yayi ba,
Bayan sun gama suka dawo kan kujeru,Daddy fita yayi yacewa Ameen anjima yasamesa suyi magana,ba haka yaso ba yaso yanzu suyi maganar don yana son zuwa gida a yau yaga Naanahrsa amma ya ya’iya haka ya daure amma zuciyarsa na masa zafi,MOmy ciki ta shige,Fareeda na ganin haka ta dawo kujerar da Ameen yake,hannunsa ta kamo”Ameen nayi kewarka wallahi bansan ina sonka sosai ba sai da kayi wannan tafiyar gaskiya ka dad’e kusan wata biyar,fincike hannunsa yayi sai kyakkyawan mari da ya kifa mata,
Tadafe kumatunta da sauri tana kallonsa cike da mamaki,gyara zama yayi ya mayar da hankalinsa a TV,miskilancin ya 6otsa”ka mareni,Fareeda ta fad’a tana hawaye,kallonta yayi a wulak’ance yace”duk ranar da kika kwatanta irin haka wanda zan miki sai yafi na yanzu,