NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Shi kansa Abban hawaye yake yace”Ameenu kai ka aikatawa yarinyarnan haka innalillahi wa’inna ilaihir raju’un Ameenu kanka kacuta kuma inaso kasani daga yau bani baka kum…..bai k’arasa ba yayi shuru saka makon k’arar da Naanah tasaka,

“Wayyo cikina bayana marata wayyo mutuwa zanyi,tasaki k’ara sai kuma ta zube a gurin gaba d’aya akayi kanta,Umma ce farkon isa,

Ameen ya rungumeta yace cikin kuka”Naanah kece rayuwata don Allah ki tashi karki barni ba laifina bane k’addara ce kuma duk mairai bai haurewa k’addararsa kiyi hakuri ki yafemin don Allah Naanahta ki tashi……..

WhatsAPP no 08104335144

Tofah muje zuwa????
Karkumance
Fateenku ce????????

      Ummu Affan✍????✍????✍????

????CIKIN WAYE?????

  ❤❤❤❤
       ❤❤
          ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Am Sorry my fans for my absence some tin came of but am back,Karku damu ana tare ina ji daku my fans,Musamman wad’anda suka biyoni PC da wad’an da suka kirani nagode????

Didicate to Hussaini 80k

Special gift to Anty Hauwa,ina yinki over Antynmu maganin kukanmu,Allah ya k’ara d’aukaka ki????

Gaisuwa gareku d’aukacin members na kungiyarmu me tarin Albarka Arewa writers,’yar gatan arewa na gaishe ku????

Bismillahir rahmanir rahim

????5⃣7⃣-5⃣8⃣

Hankalin kowa yatashi a gurin ganin Naanah ko numfashi batayi,nan fa Ameen ya kinkimeta sai mota akayi asibiti da ita,

Gaskiya sun shiga cikin wani hali musamman Ameen duk yayi wani iri haka Abba da iyayen Naanah,da kawa ta gari Zainab haka su Hajiya da Marwan,

Jini kawai Naanah ke zubdawa ta wahala sosai tunda ta farfad’o sai kuma wani irin nishi tun tanayi da k’arfi har ta galabaita sosai,domin sunce nak’uda take,hankalin kowa fa ya tashi,

Ameen kuka yake kamar wani k’aramin yaro,shi kansa ka kallesa abin tausayi ne,likita yace dole sai an k’arawa Naanah jini leda uku,Na Ameen aka dauka domin jininsa mai k’arfine zai iya bawa kowa jini,leda biyu aka dauka,

Didiy ya kira Sayyeed a waya yace”kana ina,jin yanayin muryar Didiy nasa yace”Didiy lafiya,yace”lfy kalau kana inanace,”ina hanya zan koma gida daga makaranta,

Yace”to kazo asibiti yanzun nan,ya fad’a masa sunan asibitin,”me yafaru Didiy,ya fada a rikice don yanayin da yaji muryar Didiy kuma yace yazo asibiti,baibasa amsa ba ya kashe wayar,

A rikice Sayyeed yayo kwana,yana zuwa ya gansu a Reception,yanayin da ya gansu yasa shi kasa fassara waye ba lafiya tun da yaga iyayensa yaga ‘yan uwansa,Didiy yace”suje a d’ibi jininsa domin jininsu d’aya yake dana Naanah bayan an gwada aka d’iba shidai binsu yake da kallo cike da rud’u don yakasa gane meke faruwa,kuma ba fuska bare yayi tambaya,

Kwanan Naanah biyu a asibitin amma duk mai imani ya ganta saiya tausaya mata abin tausayi duk ta fita haiyacinta abin ba sauk’i,

Ganin tana tashan wahala likitoci sukace gaskiya saidai a mata aiki,a cire abinda ke cikin,haka Didiy yasa hannu cike da tashin hankali aransa yana addu’ar Allah ya sa ayi lafiya,

Cikin ikon Allah da yardarsa har angama shiri za’a tafi da Naanah d’akin Tiyata sai tayi wani nishi mai k’arfi nan take sim6ulelan kyakkyawan yaro sak Ameen ya fad’o kamar yayi kaki ya tofar,Allahu akbar Allah kenan waye zaiyi hakan bayansa,

Bayan an gama gyara yaron Ameen ya amshesa ya k’amk’ame yana kuka sosai daman yana Labour room d’in kusan tare akayi amsar haihuwar dashi,fitowa yayi da yaron yana hawaye,Abba ne ya kar6esa yana hararar Ameen shidai k’asa yayi da kansa sannan ya koma d’akon haihuwar inda ake gyara Naanah,har fad’a akayi da Ameen akan shiga d’akin haihu da yake dole suka rabudashi don yace basu isa sumasa iyaka da Naanahrsa ba,

Kallon yaron kawai suke wanda baida maraba da Ameen,addu’a aka masa sosai inda Abba ya masa huduba da sunan Didiy wato Taheer

08104335144

Amin afuwa da wannan idan na sami lokaci anjima zakujini????

Fateenku ce????

Ummu Affan✍????✍????✍????
????CIKIN WAYE?????

  ❤❤❤❤
       ❤❤
          ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

????5⃣9⃣-6⃣0⃣

Bayan an gama gyara Naanah aka dawo da ita d’akin hutu Alhamdulillah jikin da sauk’i domin cikin ikon Allah tana haihuwa sai ta dawo nomal saidai abinda ba’a rasa ba,

Domin tak’i kallon kowa tunda suka shugo kanta ak’asa yake ta kasa had’a ido da kowa,

Jinta take ta to zarta wai itace da d’a kuma wanda aka haifa batare da aure ba,to CIKIN WAYE?,

Wata k’ara ta saka da ta tuno abinda yah Ameen yace”CIKIN dake jikin Naanah CIKINA NE,

Tak’ara sakin k’ara tare da fashewa da kuka,gaba d’aya sukayo kanta,Abba yace”Naanah lafiya me ya faru,Cikin kuka tace”Abba kace ya fita banasan ganinsa Abba ya fita,

Tun kafin Abba yayi magana Ameen ya fice da sauri,ta kwanta jikin Abba tana kuka yace”Naanah kiyi hak’uri Ameen kansa ya cuta kuma zaiga sakaryar abinda ya miki ai abinda kashuka shi kake girba,

K’amk’ame idona nayi ko photon fuskar yah Ameen banso na hango,

Likitoci sun bamu sallama ganin babu wani abu dake damuna,kai tsaye gidan Daddy aka wuce dani,A bedroom d’in Momy aka saukeni,har zuwa lokacin banga abinda na haifa ba kuma bama nason na ganin,

Zuwa lokacin tuni Sayyeed yasan abinda ke faruwa haka ‘yan uwa duk sunji labari na kusa sai zuwa ganin Naanah suke sunawa juna barka da arzikin ganinta da akayi yayin da na nesa akayi ta waya dasu suma sunce suna hanya zuwa gobe,

Nan Momy ta yimin wanka mai rai da lafiya,ta gyarani fess sannan ta kawomin lafiyayyen tuwan semo da miyar ku6ewa d’anya dataji bushasshen kifi sai kular ferfeson kan rago me romo da yaji tarugu sosai,

Haka na zauna naci sosai na k’oshi,sannan na kwanta kenan saiga Momy ta shugo hannunta da jariri,mik’omin shi tayi tana cewa “amsarsa Naanah yasha yaron ma yana da hakuri wallahi,

Kwanciya nayi tare da zuya mata baya nace”ni Momy bana sonsa don Allah ki fita dashi,sakin baki tayi tana kallona”Naanah meye haka shime yasani don Allah karki d’au hakkinsa,

Kuka tasaki tare da birgima akan gadon tanacewa”ni bana sonsa kuma ba’abinda zan basa,zaunawa Momy tayi bakin bed tare da dafa Naanah cikin sigar rarrashi tace”Naanah wannan yaron da kike gani baisan komai ba karki d’au hakkinsa ba laifinsa bane domin daza atambayesa wallahi zaifi kowa bak’in cikin me yasa yazo ta wannan hanyar amma kaddara ta riga fata,kiyi hakuri wata rana sai labari ki ringumi d’anki daman Allah ya rubuta hakan sai yafaru dake shiyasa kika 6ace har suka tsinceki suka raineki daga baya hakan ta faru meyasa bazakiyi tawakkali ba,

Jikin Naanah yayi sanyi amma ita har ga Allah bata k’aunar yaron nan dashi da ubansa,Momy ta mik’o mata shi,ta amshesa,bayan fitar Momy ta k’ura masa ido yayi kama sosai da yah Ameen,

“Ba tare da aure ba fa kika haifesa Naanah,zuciyarta ce ta fad’a mata hakan da sauri ta sakesa kan gano ta fashe da kuka,shima yaron ya tsandara kuka don yadda ta sakesa abin ba kyau,

Da gudu Momy ta shugo kallon Naanah tayi ta kalli yaron da gudu ta d’agosa,cikin fushi tace”Naana baki da hankali ko?to meye hakan kike?ko kin isa ki cenza ma kanki rayuwa ne haka Allah ya kaddaro miki me zaisa bazaki rungumi k’addararki da hannu biyu ba,haba Naanah wannan wanne irin rashin hankali ne,

Cikin kuka tace”Momy ki yafeni karkiyi fushi dani narasa gane ya zanyi ne amma ina rok’onki????don Allah ku shayar da yaron nan da madara bazan iya basa Nono na ba please Momy????,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button