NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Abba yace”kinfi wadan nan sakarkarun anyi bako basusan sutarbesa dako ruwa ba,murmushi kawai nayi yayin da su kuma sukaci gaba da jefata da mugayen harararsu,

Saida yaci ya koshi sannan aka fara hira,Umma tace”ke me kama da bakar mayya saiki tashi ki bani guri ingana da d’ana,…
????CIKIN WAYE?????

 ❤❤❤❤
      ❤❤
         ❤



   Story
            and
                   Written

By
Fateemah Sunusi Rabee’u
Ummu Affan

????7⃣-8⃣

Bismillahir rahmanir rahim

????Zan tashi Yah Ameen ya riqe hannuwa na,ya kalli Umma yace”Haba Umma har yanzu baki dena wannan abun ba,tace”to uban ‘yan shisshigi da kai nake magana ko da ita,yace”amma me yasa baki kori su Rahma ba sai ita,cikin fushi tace”Al-ameen ka fita idona in rufe kai kanka kasan da kyai banbaci atsakanin su kuma wllh ka dena samin baki a cikin magana ta da wannan shegiyar yarinyar,

Girgiza kai kawai ya ke zuwa cen yace”Allah yabaki hakuri ya huci zuciyarki,tsaki taja mtsuwww sannan ta juyo kaina “ke bada ke nayi magana ba,

Tashi nayi jikina asanyaye ina zubar hawaye,ko da zuwana dakin kan katifa na fada ina kukan bakin ciki,waini mai nayiwa Umma ta fiddani daban cikin ‘yaranta,ina ‘yar cikinta tana nunamin banbanci da sauran ‘yan uwana,sosai nake kuka na tusa kaina cikin fulo,

Banji shugowarsa ba sai ji nayi ya dagoni zaune,yana sharemin hawayena yace”Naanah ke me hakuri ce da juriya ga hankali please kar maganar Umma ta d’aga miki hankali,kallonsa nayi ido cikin ido nace”Yah Ameen abin da Umma ke min ya fara isa ta hakan yasa nike jin shakkar anya Umma ta aifeni?,da saurin yarufemin baki yace”kul karki sake fad’ar haka Umma ita ce ta aifeki ko da wasa kar in sake jin kinyi wannan maganar,da haka yayi ta rarrashi na har na sakko muna hira yana bani labari ina dariya,

Yasa hannu aljihu waya ya ciro k’arama ce kirar TECNO ya bani,mai kyau ce da tsada,yace”ga waya na saya miki,nayi sauri na amsa da akwaini da son waya ko don game don idan na dau wayar Zainab game kawai nake,nace”kai amma tana da kyau,”tayi miki kenan,yace,nace”sosai kuwa nagode Yayah saidai ina tunanin Umma bazata barni da waya ba,yayi murmushi yace”karki da mu saida na nuna mata saboda hakan har Rahma da Sakina na sayawa,

Nace”kai Yayah amma naji dad’i Allah ya kara rufa asiri yasa kafi haka,yace”ameen,yana jin dadin yadda idan yayi mata kyauta take nuna jin dad’inta tare da masa kyawawan addu’o’i,sa6anin su Rahma wani lokacin ma idan yayi musu kyauta cewa suke baiyi musu kyau ba,amma ita ko da bata son abun zata amsa kuma ta masa godiya da addu’a,shiyasa ako da yaushe yake kara sonta,

To tunda yazo gidan su Rahma aka natsu domin inhar yazo to dole ne su natsu ba wacce ke fita daga makaranta sai gida,su daman ba wani da muwa suka yi da makaranta ba,to in fa yazo dole aje shiyasa basu kaunar yazo mugun tsoransa suke don bai wasa da yara,

Yah Ameen cikakken mutum ne mai haiba da kamala matashin saurayi me jini ajika shekarunsa talatin da biyu yanzu fari ne dogo cikakke mai cikar kamala kirarsa ta kar fafan maza ce bai cika fara’a idan kaga yayi ko murmushi to tare yake da iyayensa saiko Naanah da yake tausayawa halin da Umma ta ke mata,

Malam Isma’il wanda aka fisani da malam Sama’ila shine mahaifinsu bafullatanin Adamawa wanda neman halaliya yadawo dashi Kaduna ba wani mai kudi bane saidai rufin asiri sana’ar saida takalma yake a shagon da yakama haya kasuwar barci,ba laifi yana samu don har Lagos yake zuwa sari,Anan kasuwar su ka hadu da Karimatu wato Umma har Allah ya hada auransu ita haifarfar nan ce,

Karimatu tun farko ba dad’in zama da ita yake ba saidai hakuri don yana da hakuri sosai d’ansu na farko Al-ameen wanda ake cewa Ameen sannan Rahma sai Sakina da Karamarsu Naanah Firdausi wadda nike tantamar anya ita ta aifeta(uhmm mudai je zuwa),

Ameen yayi karatun primary har zuwa matakin secondry da ga baya kuma ya shiga jami’ar Ahmadu Ballo da ke Zaria ya karanci Business,duk da temakon Babansa da shi kansa da ke buga bugarsa har Allah ya temake sa yakai matakin digiri,wajen neman aiki ne Allah ya hadasa da Alhaji Salisu Sada babban d’an kasuwa da sunansa ya shahara babban mai arziki ne wanda yatara dukiya mai tarin yawa,kallo daya yawa Ameen yaji yaron ya kwanta masa sosai yaja shi jiki ya nuna masa harkar kasuwarsa,in takaice muku mutane da yawa basusan Ameen ba d’an Alhaji Salisu Sada ba ne,yanda Alhajin ke jin Ameen a ransa ko dan da ya aifa arbarka daman kuma Allah bai basa aihuwa ba duk tarin dukiyar da yatara,

Hajiya Asma’u matar Alhaji Salisu Sada d’a ta dauki Ameen haka shima Alhajin komai yana iya zartarwa kuma yazartu agidan Alhaji Salisu har d’aki garesa a gidan…

Muje zuwa har yanzu ba mu shugo cikin gundarin labarin ba taku Fateenku  

  Ummu Affan

????CIKIN WAYE?????

  ❤❤❤❤
       ❤❤
          ❤


     Story
             and
                   Written

By
Fateemah Sunusi Rabee’u
Ummu Affan

????9⃣-1⃣0⃣

Bismillahir rahmanir rahim

Duk kan ‘yan uwan alhaji Salisu Sada da na Hajiya Asma’u sun san da zaman Ameen kuma dukansu suna kaunarsa,

Idan yazo gida ba wani dad’ewa yake ba kasancewar aikinsa don har kasashen waje Daddy yake turasa akan har kokin kasuwancinsa,

Wannan karon ma satinsa guda ya koma cike da tausayin Naanah,

Mun fara jarabawarmu ta kammala k’aramar secondry wato (JSCE)cikin azumi ne amma Umma bata tausaya min duk kan aikin azumi nice keyi dana dawo skul banda wani lkc,

Ina duk’e ina wankin waken da zan soya kosai anjima Abba ya shugo,dawowarsa sallar la’asar,”Sannu da zuwa Abba,yace”yauwa Naanah,gefen tabarma ya zauna daga gefen inda nake,yace”Naanah yaushe ne zaku kammala jarabawar,nace”Abba sauran kwana biyar ana sauran kwana uku sallah,yace”to Naanah Allah ya nuna mana,na amsa da ameen,

Zuwa cen nace”Abba kana dai sane da saukarmu bayan sallah ko,murmushi yayi yace”kai Naanah kinsa saukar nan aranki Yayanku ma ya turo kud’in shahadar na biya miki,nace”yawwo Abba Allah yasaka sai kuma d’ayar maganar,”ta me?,ya tambaye,turo baki gaba nayi cikin shagwa6a “kai Abba ba dai kamance da maganar ankonmu ba,dariya yasa yace”Naanah iyayen rikici kinsan Yayanku yace zai komai ni ya hutar dani,zum6uro baki nayi,”kai Abba kasan Yah Ameen da mantuwa,”ehye baya saya miki waya ba saiki dunga tuna masa,cike da yarinta nace”eh fa haka ne Abba,gaba daya mukasa ka dariya,

Umma ce ta fito daga farlour,taja tsaki mtsuuww,ta gallamin harara take na dawo hayyacina,tace”aikin banza harara a duhu ayi dai mugani idan tusa zata hura wuta,

Abba ya kalleta ganin yadda tayi masa k’erere a kai,yace”lafiyarki,”qlau ta basa amsa a tsiwace,kafin ta juyo kaina “KE tace min daman mafi akasari tafi kirana da ke,juyowa nayi ina kallonta,tace”mayya da shegen manyan idanuwan ki kamar na aljanu kurwata kurr da ke,

Da sauri na sadda kaina kasa”kiyi hakuri,nace cikin sanyi,”yar kaza kazan nan ai daman haka kike da anyi magana kice ayi hakuri kamar kinfi kowa sanin Allah a fuska musa a zuciya fir auna,

Sake sadda kaina kasa nayi,tace”zan fita ne kan indawo ki tabbatar kin kammala komai na bud’a baki sauran kiyi abinci da yawa ko kiyi kad’an yazo bai isa ba sakarya shashasha,ture ni tayi tai gaba ko tambayar Abba babu daman duk in zata fita bata tambayarsa,

Tashi nayi ina kakka6e jikina Abba ya kalleni ckn raunin murya yace”Naanah kici gaba da hakuri wata rana sai labari nima dai kina kallo hakuri na ke da ita,ajiyar zuciya kawai naja naci gaba da aikina,

Araina ina tunanin irin wannan hali na Umma,Abba yana matukar bani tausayi wani lokacin saidai ina tunani da mamakin mai yasa bai taka mata burki idan tayi wani abun ko da yake gsky yana bakin kokarinsa ina ga gajiya yayi yanzu…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button