NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Kallonta Momy tayi cike da takaici kafin tace”Naanah meke damunki ne amma bari na kira iyayenki tunda ni ban isa dake ba,zata fita na ruk’ota “kiyi hak’uri bazan sake ba,

Mikomin yaron tayi “to kar6i ki basa ina gani,amsarsa nayi tare da rintse idona ta fara basa,

Ai wani zafi da naji yasa na cire masa da sauri nace”wayyo Momy da zafi,kiyi hak’uri da sannu zaki saba,batabar d’akinba saida ta tabbatar yaron yanasha sannan tafita,

‘Yan Igabi san iso washe gari yayun Didiy da matansu da yaransu nan gidan Daddy suka sauka haka akayi ta murnar gani na,lokaci guda muka saba da Salma d’iyar Baba Auwalu da kuma Hafsat d’iyar Baba Sani,domin mu sa’anni ne,muka hadu da Zainab akayi ta hirar zuminci,

Yau kwana shida da haihuwata,kullum sai Momy ta tsareni nikebawa yaron nono,tun tanamin fad’a yanzun ta dawo rarrashi,

Zaune muke,inajinsu yadda suke tashirin abinda za’ayi gobe suna,abin yabani mamaki araina,ganin shege kuma harda wani suna za’ayi,nidai na zama yar kallo,

Sayyeed yace”amma fa Naanah ya kamata musawa yaronmu wani sunan daban tunda sunan Didiy yaci,ta6e baki nayi bance komaiba,Zainab tace”rabu da ita kawai aini tuni nawa d’ana suna,yace”yauwa my zeey me kikasa masa,tace”Muhsin nasan Naanah tanason wannan sunan,Salma tace”wow gaskiya sunan yayi dad’i Muhseen,Hafsat tace”daga yau sunan yaronmu Muhseen,

Da gudu Fahat ya fita yana fad’awa mutane da Muhseen za a dunga kiran yaron,

Washe gari Mutane sosai aka taru a masallaci wajen rad’in suna sosai Daddy da Didiy sukayi gayyata don masallacin ya cika sosai,

Ameen da Marwan duk sunzo Abba yana kusa da Didiy,bayan gama rad’in sunan sai kuma sukaji wata maganar da ban,

????????????kasa kunne nayi don naji kamar aure akeson d’aurawa ????????????nidai banji sosaiba ban ganiba mu had’u page na gaba donji me za’ayi a masallacin bayan rad’in suna da akayi,

Fateenku ce????????

    Ummu Affan????????

????CIKIN WAYE?????

  ❤❤❤❤
       ❤❤
          ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

????6⃣1⃣-6⃣2⃣

Bayan gama rad’in sunan aka fara d’aura aure,kan kowa ya kwance a gurin mamaki ne fal ran wasu daga cikin jama’ar dake wajen ciki,harda Abba,Ameen,Marwan,

Aure ne aka d’aura tsakanin Al-ameen Isma’il Muhammad,da Naanah Firdausi Taheer Sada,sai Marwan Ibrahim da Salma Auwal Sada sannan Sayyeed Taheer Sada da Zainab Ibrahim,

Gaba d’aya kallon kallo suke musamman Ameen da Marwan,hawayen farin ciki kawai Ameen ke zubdawa Allah yajika masa burinsa yau Naanah ta zama mallakinsa,zuciyarsa ta buga da yatuno ya Naanah zata d’au wannan maganar domin yasan kamar yadda baisan da maganarba yasan itama batasan komai ba,

WAITO YA HAKAN TA FARU nifa duk sun sani a duhu????Kufah????,

Abinda ya faru,bayan zuwan yayun su Didiy,Alh Auwalu wanda shine babbansu sai Alh Sani sannan Daddy k’araminsu ne Didiy,kafin muji ya akayi bari muji tarihin ahlin

Alh Sada Igabi shine sunan mahaifinsu,mahaifiyarsu Maryama wacce akafi sani da Baaba Mero,su dukansu haifaffu Igabi ne k’aramar hukumar Kaduna,tun a wancen zamanin Alh Sada mutum ne mai arziki wanda ya riki sana’arsa ta noma da kiwo yana da son karatun boko tun wancen lokacin hakan yasa ya tsaya tsayin daka yaransa duka saida sukayi karatu,duka su hud’un maza ne basu da mace kuma mahaifinsu Baaba mero ce kawai matarsa,

Auwalu shine kawai ya tsaya iya secondry inda yaci gaba da sana’ar mahaifinsa bayan rasuwarsa,ganin burin mahaifin nasu nasan suyi ilmi mai zurfi yasa ya tsayawa k’annansa saida sukayi karatu sosai boko da islama,daman tuni shi yayi aure yana nan zaune gidansu na gado,

Sani ya fara gamawa inda yasami aikin gwamnati anan Igabi,shi kuwa Salis da yake Business ya karanta sai ya bud’e wani k’aramin kamfani a Kaduna cikin ikon Allah lokaci k’ank’ani Campanynsa yayi suna wajen k’era kayan d’aki da na wuta,hakan yasa ya bunk’asa sosai inda yayi wani babban campanyn sosai yayi arziki,

Shi kuwa Taheer babban lawya ne mezaman kansa,ya shahara sosai wajen aikinsa,Allah ya amshi ran mahaifiyarsu sunyi kukan rashi inda suka d’auki Alh Auwal ya zame musu uwa da uba mutum ne na gari,Alh Auwal da Alh Sani a Igabi suke zama,Inda Salis da Taheer suke Kaduna,daman tuni duk kansu sukai aure matan Alh Auwal uku yanzu,su kuma dukansu d’aid’ai sun tara iyali sosai saidai shi Alh Salis Allah bai basa haihuwa ba,daman kunsan wannan tun abaya,

Tarihinsu kenan,cigaba,daman tun zuwansu Alh Salis ya sanar dasu dukkan abunda ya faru sun tausayawa Naanah Alh Auwal yace”k’addararta kenan mu bazamuja da hukuncin Allah ba tabbas Ameenu bai kyauta ba amma sanin da muka masa na yaron kyirki yasa mun yafe masa saidai tabbas zamu had’a auransu tunda yaron na sonta,Fareeda dake zaune gefe tace”nayarda Baba Ameen nason Naanah sosai bai iya kula ko wwacce mace saboda k’aunar da yake mata,

Nan ta basu dukkan labarin abinda yai ta faruwa a tsakaninsu saboda son da yakewa Naanah,Alh Salis yace”kwarai kuwa nima shaudane don yasha bamu labarin ta,nan suka yanke hukuncin ranar suna za’a d’aura auransu amma karwanda yasanar musu,Daddy yace”ko Abbansa bazamu sanarwa ba saboda yad’au fushi dashi sosai idan yaji bazai yarda ba,kowa ya gamsu da hakan,

Sayyeed yace”wallahi saidai a had’a dani nima k’awarta Zainab nakeso don tayimin,gaba d’aya aka d’au salati Didiy yace”mun shigesu zamani yanzu ya sauya Sayyeed mukake fad’awa aure kakeso,

Alh Salis yace”rabu dashi zamani ne ai gara da yasanar damu da yaje yana aikata wani abun fa?zanga Alh Ibrahim ai abokina ne,Fareeda tace”yanzun ni ina matsayin mace amma har k’anina namiji zai aure yabarni ga kuma autarmu,sai kowa ta basa tausai Baba Alh Sani yace”‘yata ki kwantar da hankalinki aure lokaci ne da naki yazo zakiyi,tace”haka ne,

Nan akayi addu’a awashe gari Alh Auwal da Alh Salis suka sami Alh Ibrahim yayi murna don kowa zaiso had’a zuriya da Familynsu Naanah saboda nagartarsu,nan yake sanar dasu ai Marwan ya sanar dashi yanason Naanah,

Hak’uri suka basa cewar ammata miji,Alh Auwal yace”Amma akwai Salma sa’anni suke da Naanah idan yanasonta to,nan take Alh Ibrahim ya amince inda suka tsaida maganar ranar suna xa’a d’aura auran,

To koda yasanar da Hajiya taji dad’i sosai itama tace”karsu sanar da yaran idan an d’aura sai suji,

To kunji yadda abin ya faru,amma ku ya kuke ganin Naanah zata d’auki maganar auran zata yarda da yah Ameen kuma zata amshesa a matsayin miji ko ya?

Marwan kuwa fa shin ya zaiji akan rashin Naanah shin zai amshi Salma yayi auran huce haushi ko ya?

Zainab kuwa fa shin Sayyeed ya ta6ama cewa yana sonta,ga burinta na ganin tayi karatu mai zurfi kuma ga auran Sayyeed ya zataji,

Wai ya batun Umma nifa kwana biyu bana jinta kota gudu ne koya abun yake ne????????

Uhmmm duk amsoshin nan sai kunci gaba da biyo Ummu Affan muje zuwa Ina alfahari daku musamman fans d’ina na Facebook nagode????

Fateenku????

     Ummu Affan????????

????CIKIN WAYE?????

  ❤❤❤❤
       ❤❤
          ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

????6⃣3⃣-6⃣4⃣

Bayan andawo daga masallaci wajen d’aurin aure k’ayatacciyar walimar cin abinci a ka gabatar a harabar gidan Daddy,gaba d’aya nan suka kawo bak’insu,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button