NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Cikin gida kuwa Fahat ne ya shiga ya tsegunta abinda ya faru,mutane da yawa sunyi mamaki domin basusan da zancen ba,Momy tace”kayi shuru kar Naanah taji zancen nan daman da k’yar ta yarda aka shiryata don haka kowa yayi shuru nasan akwai abinda suka taka da kansu zasu sanar mata,

Hakan yasa kowa yayi shuru,ita kuwa daman Naanah tun safe tana cikin bedroom da k’yar ta yarda aka mata kwalliya tasa kayan da Ameen ya mata akwati guda na suna babynsa ma nasa daban,

Bataso saka kayan Ameen ba amma Momy ta dage dole ta hakura akan yasa tace”bazata fito farlour ba,tunda kowa ya tsaneta komai suce Ameen,

*****************

Kwana yau biyar da sunan Muhseen yaro kyakkyawa,idan Naanah tana kallonsa kuka kawai take,yauma hakan ta kasance zaune take kan bed ta gama karyawa da had’in da Momy ke mata,yaron ya tuntsere da kuka,

Ahankali ta juyo ta kallesa,ganin yadda yake kuka sai kawai itama tasaka kukan ta kasa d’aukarsa hannunta rawa kawai yake,

Sosai ta saki kuka tanacewa “me yasa?meyasa kazo ta wannan hanyar?meyasa baka jiraci zuwanka ba sai lokacin da yadace?meyasa kayi gaggawar zuwa lokacin da bana maraba dakai,

Ameen da yashugo tun farkon jin irin kukan da yaron yake don ko kad’an baison yaji yana kuka,tsayawa yayi yana kallonta dajin kalamanta wani irin so da tausayinta yacika masa zuciya,ya k’araso gurin da take tare da dafa bayanta,

Da sauri ta juyo don ta tsorata tayi tunanin ko Momy ce ganin Ameen yasa tayi saurin ture hannunsa a jikinta tare da wata muguwar harara da ta banka masa,

“yace”duk abinda zakimin Naanah nasan na cencenci haka amma inason kisan wani abu guda ni Ameen mai k’aunarki ne a ko wanne irin hali kika tsinci kanki,sannan kiyi hakuri da abinda ya faru k’addara ce wacce ta riga fata kimin afuwa Naanah nima ba ason raina na aikata miki hakanba,

Hawaye ne ya gangaro akan fuskarta ta kallesa cike da tsana tace “Ameen na tsane ka bana kaunarka kuma bazan ta6a k’aunarka ba ka cuceni ka 6atamin rayuwa Ameen ka cutar da zuciyata kamin abinda bazan ta6a ya fe maka ba,

“Kiyarda da k’addara mana Naanah meyasa kike abu kamar wacce batace islamiyya ba,mik’ewa tayi cike da takaici tace”tunda ka cuceni dole kace haka mana to banjeba kuma bazan yarda da kaddarar ba NA TSANEKA YAH AMEEN banson ganinka please kafitarmin daga d’aki,

Da sauri ya toshe kunnensa kalma kenan mafi muni agaresa,da sauri ya juya ya koma nasa d’akin”NA TSANEKA YAH AMEEN,kalmar dake ta yawo a dodon kunnansa,saiga yawaye yana bin kuncinsa,

A fili ya furta”haba Naanah me yasa bazaki yarda da k’addara ba ni me sonki ne har abada,

Fareeda ta shugo wacce duk taji abinda ya faru,kallon Naanah tayi tace”wallahi Naanah baki da wayau,yanzu miji kamar Ameen ya k’ask’antar da kansa yace yana kaunarki har kidinga ya6a masa irin wadannan mugayen kalaman haba Naanah,

Kuka ya saki tace”me yasa duk abinda nayi sai adunga ganin laifina ku bakwa duba abinda yayimin,Fareeda ta k’araso tare da rungume ‘yar uwarta cikin sigar rarrashi tace”tabbas bai kyauta ba amma idan zakiyi tunani ba halinsa bane kaddarace wacce duk kan wani mumini dole yayarda da ita Naanah Ameen me kaunarki ne ki duba irin halin da kika shiga a gidansu amma ki duba jajircewarsa Allah ne ya rubuta hakan zai sameku shiyasa kika 6ata har kika fad’a hannunsa AMEEN yacika dukkan wani abu da za’aso na nagarta,bayan nan kuma shi me kaunarki ne da be kaunarki wallahi don ya miki wannan abun ko kallo baki ishesa ba,kiduba fa Naanah maza da yawa idan sun sami abinda sukeso gurin mace shi kenan sai su rabu da ita ko wanne hali zata shiga babu ruwansu indai sun sami biyan buk’atarsu amma ke jibi yadda ya jajirce akan ke yake kauna kuma babu namijin da zaki aura kisami kwanciyar hankali irin Ameen,

Da sauri ta d’ago ta kalleta tace “me yasa kikace haka Anty Fareeda,murmushi Fareeda tayi tace……

Fateenku ce????

   Ummu Affan????????

????CIKIN WAYE?????

    ❤❤❤❤
          ❤❤
             ❤

Story and written by FATEEMAH SUNUSI RABEE’U
(UMMU AFFAN).


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

????6⃣5⃣-6⃣6⃣

Tace”Saboda shine ya fara saninki a mace,shin kina tunanin zaki auri wani ya sameki ba cikakkiyar budurwa ba har kusami zaman lafiya da kwanciyar hankali,AMEEN shine yadace dake domin bazai ta6a wulak’antaki ba domin yasan shine silar komai kuma bada saninki ya aikata miki hakanba kinga dole ya girmamaki kuyi zamanku lafiya koda ba dan wannan ba d’anku da kuka haifa kurik’e abunku kubashi tarbiyya bazai ta6a tunanin bada aure kuka haifesa ba,

Kuka sosai ya k’wacewa Naanah tace”Anty Fareeda Marwan duk yasan da wannan yasan duk abinda yasameni ni nasan idan na auresa zan sami kwanciyar hankali zai bani duk kulawar da tadace,

Fareeda tace”Naanah ke har yanzun yarinya k’arama ce amma nan gaba zaki fahimci abinda nake nufi nidai inason kimance da komai ki rungumi k’addararki hakan zaisa ki sami kyakkyawan rabo nan duniya da ranar gobe k’iyama,

Tana gama fad’ar haka tayi waje,Naanah ta tura kanta tsakankanin cinyoyinta tana kuka sosai daman Fareeda ta fita tare da Muhseen,

Baku tambayeni ina Umma ba?,

Ai Umma Karimatu tun ranar da abin ya faru taji ko wacece Naanah sai taji duk ta muzanta,haka tayi kai da k’asa sai kace bak’ar munafuka,bayan sun tafi kai Naanah asibiti lokacin da ta fad’i,ita ma ta had’a yanata nata sai gidansu Rahma dama cewa tayi bazata ba,da Sakina tazo ta sanar mata abinda ya faru tabi bayan Umma inda ta sameta duk ta rame ta zama wani iri,saboda daman iyayenta tuni duka suka rasu sai Kawunta agurinsa ma ta girma shiya aurar da ita,to zaman gidan dai ba dad’i Matansa sun sa mata ido ba halin tayi abu yanzun za’a fara mata gori abincima basa bata,nan fa hankalints ya tashi duk kud’in da Ameen yake bata adashi takeyi taje gurin me adashin amsar kud’in suka hau tsiya domin ta cinye kud’i,Umma tayi kuka kamar me tayi da nasanin abinda tawa Naanah yau ga ranar k’in dillaci,duk ta zama wata irin sanyi kamar ba Umma ba,

Ranar da Sakina tazo wankau ta iske Ummar nayi,ta gaishe da matan gidan suka shiga d’an akurkin d’akin da Ummar take wanda shirgine ciki don acikinsa matan gidan ke ajiyarsu ta kayan abinci da duk wasu tsummokaransu,

Cikin hawaye Umma tace”Sakina nayi takaicin abinda na aikatawa Naanah yanzun taya zan fuskanceta ashe daman Ameenu ne ya mata ciki nayi takaici duk wannan abun da nake ashe CIKIN NA D’ANA NE,jikana ne nayi da nasani kaicona ni Karimatu ashe duk dukiyar da mukeci duk ta iyayen Naanah da wanne ido zan kallesu,

Sakina taja numfashi uhmm tace”ai duk irin abinda nake gaya miki ne Umma amma kika k’iji yanzun ga irinta nan amma me yasa kike wankau,tace”dole ne tasa Sakina idan banyiba wa zai ciyar dani abinci ni ke saya,

“Amma me yasa baki sanar damu ba,Umma duk lalacewarki ke uwarmu ce babu yadda zamuyi dake yanzu idan yah Ameen yaji wannan abun zaiji dad’i ne,tace”ya kikeso inyi Sakina dolene fa tasa,tace”to meyaraboki da gida sanake ko lokacin da Abba yasakeki baki bar gidanba har ya mayar dake sai yanzu haka kawai kibar gida,

“Wallahi Sakina kunya nakeji da wanne idon zan kalli Abbanku da yayanku balle iyayen Naanah,Sakina tace”ai duk abinda ya faru ya riga ya faru ki had’a kayanki mukoma yanzu don bazan bari ki kuma kwana a gidan nan ba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button