NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

A k’ofar gidansu yayi parking kamar kullum idan yazo gidan,sannan ya fito cikin takun k’asaitarsa ya nufi cikin gidan…….

Muje zuwa????
Fateenku ce????

           Ummu Affan

????CIKIN WAYE?????

  ❤❤❤❤
       ❤❤
          ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

????3⃣7⃣-3⃣8⃣

Da sallama ya shiga ba kowa tsakar gidan,kai tsaye ya shiga farloun,”Assalamu alaikum,Umma dake zaune ita da Abba suka amsa masa,guri ya samu ya zauna,yana gaishe su,

Umma tace”mutanan waccen kasa meyema sunanta engula take kome,Ameen yasa dariya “kai Umma England ne,tace”to sannu da zuwa,Abba yace”ka dawo lafiya ya kabaro iyayen naka,yace”suna lafiya Abba suna ma gaisheku”tom muna amsawa,

Rahma ce ta shugo”lah yah Ameen sannu da zuwa”yauwa sarakan yawo daga ina haka?,sosa k’eya ta fara”uhmmm uhmmm Umma ce ta aikeni,Umma tace”kin dawo,”eh tace ta gode tana gaisheki,

Uhmmm Abba yaja ajiyar zuciya tare da girgiza kai nan take sun hada k’aramin film kai ka d’auka da gaske aiken nata tayi Allah ya kauta ya fad’a a fili,Umma ta zuba masa harara,

Yah Ameen ya mik’awa Rahma key d’in motarsa yace”ki bud’e but akwai kaya kisami almajirai su shugo dasu,ta amsa sannan ta fita,

Uban kayayyaki ne ake shugo dasu fannin na masarufi,buhun Shinkafa garin semo,katan-katan d’in taliya dana makroni jarkar mai da manja su maguna sai kayan lambu su kayan miya dasu kabeji,d’anyen nama da kaji yankakku,daman duk wata ne yake musu irin wad’an nan siyayyar shiyasa ya hana Abba fita kasuwa,amma duk da hakan yakan fita ya motsa jiki,

Sai kuma tsarabar England da yazo dasu akwatina hudune cike da kayayyaki na sawa dana kwalliya,Ya mik’awa Abba nasa”shaddoji ne d’in kakkaku da yaduka sai turaruka da takalma,yayi godiya yana samasa albarka,Umma kuma atamfofi da shadda itama takalma da hijabai dasu turare,Tayi godiya,ya ware d’aya yace”wannan na Naanah ne ke kuma Rahma kid’au wannan keda Sakina,

Umma ta yatsina fuska tace”ita Naanahr fin su Rahman tayi kome,dazaka bata d’aya su kuma d’aya su biyuh,cikin ladabi yace”Umma ita Sakina batana gidan mijinta ba,ita kuma Rahma naga tafi Naanah kaya,tsaki taja”kaiwai dai kace kafi sonta fiye dasu to wallahi barama kaji idan akwai wani abu a zuciyarka gami da wannan yarinyar gara tun wuri kacireshi aranka don bamai yuwuwa ba ne atoh nama fad’a maka,a gigice ya d’ago ya kalleta,

Abba yashafa kan Ameen yana murmushi yace”kwantar da hankalinka Aminullahi karka biye maganar Umman nan taku da bata da tunani,tace”ko mahaukaciya zaka kirani ka kirani amma ba zan bar d’ana ya auri wacce ta gama gantalinta a titiba ta gama sayar da mutuncinta a banza harda cikin shege munafukar wai batasan CIKIN WAYE?ba,

Ai yadda naga Ameen ya zaro ido????ya mik’e tsaye da saurin cikin kid’ima yasani gyara zama don ganin abinda zai faru ni ‘yar rahoto LOL

Hawaye ne ke zuba a fuskarsa cikin tsananin damuwa da al’ajabi yakecewa”ciki,ciki,ciki kuma Umma badai Naanahta ba don Allah Umma kice bada gaske kikeba,kallon banza Ummar ta masa tana wani hura uban hanci tace”to nayi k’arya don ubanka kujimin yaro ohww wo yanzu nagane inda kadosa kana nufin sonta kake to wallahi idan barci kake gara ka farka tsakaninka da Naanah ba aure,

Dafe kansa yayi dake barazanar tarwatsewa,nan ya fara ganin hazo-hazo,juwa ta kwashesa nan take ya zube k’asa,gaba d’aya sukayi kansa,

Naanah dake cikin d’aki tun zuwan yah Ameen tana la6e a window tana kallon duk abinda ya faru,jin Umma nacewa yah Ameen badai sonta yake ba kuma bazai aureta ba yasa zuciyarta ta fara rawa shin daman ita da yah Ameen ba ciki d’aya suka fitoba,to idanma hakan ne ita dashi waye ba d’an gidanba,sai tambaya takewa kanta bata da amsa,

Ganin tashin hankalin da yah Ameen ya shiga da akace ciki gareta ta sadak’ar yau sai gawarta tasan garin bugunsa dazai mata yau ita sai lahira,amma sai gani tayi ya fad’i ya sume,ai ta riga kowa dura gurinsa,

k’amk’amesa tayi tana wani irin kuka,”yah Ameen don Allah ka tashi karka mutu wayyo na shiga uku yah Ameen d’ina karka mutu kabarni,Wata irin funcika Umma tawa Naanah ta mayar da ita gefe cikin masifa tace”munafuka tunda kin saba chakumar maza dole ki chakume min yaro to rabu dashi tun kafin in kasheki in kashe banza,

Ai Naanah bama tasan abinda Umma kecewa ba tuni takoma jikin yah Ameen ta sake k’amk’ameshi tana kuka,Nan Umma ta hau bala’i,Abba fita yayi yasami wani yaro nan makota ya basa key motar Ameen saida ya kira matasa suka kama Ameen akasa shi moto suka nufi asibiti,Naanah zata shiga Umma tace”wucecen munafuka wallahi d’ana ya mutu ta silarki kema sai na kasheki algunguma kawai,

Agurin Naanah ta duk’e tana kuka mai cin rai,sauran mutanan gurin sai hakuri suke bata amma ta kasa tashi,Yah Marwan ne ya fito daga gida a mota ya hango wata duk’e a kasa tana kuka kamar Naanarsa da sauri yayi parking ya k’araso gurin,duk’awa yayi saitinta,”Naanah ya kira sunanta,da sauri ta d’ago ido hawaye na zuba fuskarta,shima kasa jurewa yayi sai hawaye cikin sanyin murya yace”Naanah lafiya meke faruwa dake?me kike a wannan gurin?,wani sabon kukan ta fashe masa dashi,da sauri ya d’agata daga gurin ya kama hannunta suka nufi gidansu,

Suna shiga ta fad’a jikin Hajiya ta saki kuka,bubbuga bayanta Hajiya ta fara tasa Zainab ta kawo ruwa mai sanyi ta tasha,bayan tasha sai ajiyar zuciya take”Hajiya tace”Naanah komai yayyi zafi maganinsa Allah sannan dukkan tsanani yana tare da sauk’i,kwantar da kanta tayi jikin Hajiya tace”Yah Ameen ne ya dawo Umma na sanar dashi abinda ya faru dani ya fad’i ko numfashi bayayi,ta k’arashe maganar tana hawaye,

Hajiya tace”kiyi hakuri Naanah Allah zai basa sauk’i,Marwan yaji zafin maganarta daman akan Ameen ne ta zauna atiti kamar wata mahaukaciya sabon kamu tana kuka,ha d’aure damuwarsa yace”menene ya faru dake?naga kin rame kinyi duhu kamar bakeba,lafiya kika dena shugowa gidan nan yanzu badan naganki waje na shugo dake ba da bazaki shugoba?,

Da sauri ta tashi zaune daga jikin Hajiya “ba kasan abunda ya sameni ba?,sai ta kalli Hajiya da Zainab duksnsu sukayi shuru,Hajiya cendai tace”Naanah wannan maganar ba abar ayi ta terere da ita bace,hawaye suka xubomin da gudu na fita don banson ina nan ma Marwan yaji abinda ya sameni,

Zai bini Hajiya ta kirasa,nan take sanar dashi komai,ai a gigice ya mik’e “ciki kuma amma Naanah ta cuceni saida ta gama sawa sonta ya shiga cikin zuciyata sannan ta yaudareni amma ba komai kanta ta cuta wallahi sai ta gane ni tawa wannan babban wulak’ancin sai ta d’and’ani zafi da azaba kamar yadda nima tasawa zuciyata……..

Fateenku ce????????

       Ummu Affan✍????

Yawan comments yawan typing,Muje zuwa.
????CIKIN WAYE?????

  ❤❤❤❤
       ❤❤
          ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)

    ????'YAR GATAN AREWA????


             ????????????

AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Alhamdulillah Alakulli halin????Allah ina k’ara gode maka daka bani ikon kammala littafina me suna UWANIN QAUYE,kamar yadda kasa na gamasa lafiya Allah ka bani ikon kammala wannan lafiya????Abin alkhairan dake cikinsa Allah yasa a amma fana dashi akasinsa Allah ya tsaremu dashi,wannan page d’in sadaukarwa na ga ‘yan UWANIN QAUYE fans NAGODE da sayayyar da kuka nunawa littafin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button