NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Dubu uku Umma ta zaro tace”iya kud’ina kenan idan zaki amma sa to,Asabe ta amsa tana fad’in “k’aro d’aya,harara Umma ta ban ka mata tayi gaba tana cewa”idan basu miki ba saiki dawomin da kud’ina,har ta fita ta dawo”Asabe dame ake shan maganin,tace”jik’a mata zakiyi ta shanye ruwan,”to,tace tare da ficewa tayi gida cike da farin ciki a yau tasan cikin Naanah zai fice,

Tana shiga tasami langa ta juye maganin tass ta zuba ruwa ta rufe tana jiran ya jik’a………

Fateenku ce????

         Ummu Affan✍????✍????

Please Share and Comments.
????CIKIN WAYE?????

  ❤❤❤❤
       ❤❤
          ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

????4⃣7⃣-4⃣8⃣

Da yamma bayan na gama aikina,na idar da sallar la’asarr kenan Umma ta kirani,addu’a na shafa sannan na fito gabanta na duk’a “Umma gani,kallon banza tamin tace”Rahma mik’omin maganincen,Rahma ta kawo,mik’omin tayi tace”kafa kai ki shanye ki bani langar,

Kallon maganin nayi da yayi duhu sosai,runtse idona nayi don ni banson magani ko kad’an,balle wannan dana gansa wani iri sai naji zuciyata na tashi,kafa kai nayi idanuwana a kulle kur6a d’aya nayi na bud’e ido cike da tashin hankali saboda d’acin maganin,sam babu dad’i kamar mad’aci,

Nan na fara hawaye nace”Umma kiyi hakuri maganin d’aci,rik’e baki tayi”ehye ke harkina da za6in maganin da kike so kisha don zan temakeki na rabaki da alak’ak’ai to wallahi saikin shasa ko namiki d’ure,

Runtse ido na sake akaro na ba adadi na sake kaiwa baki,amma ina warin maganin ba kad’ai ya isheka,kuka na fashewa Umma nace”don Allah kiyi hakuri,

Mik’ewa Umma tayi cike da 6acin rai tace”Rahma kamamin yarinyar nan batasan halina ba har yanzu,cike da mugunta Rahma ta murk’ushe Naanah abinku da ban da ita ba kad’an ba sai Naanah ta kasa tashi,

Nan suka had’u suka murk’usheta suna mata d’uren magani,wani ya shiga wani yafita kuka kawai Naanah take tana neman matemaki,

Sakina tun daga waje takejin ihun Naanah da sauri ta shugo gidan,”Subuhanallah Umma, Rahma meye haka,nan tasamu ta ture Rahma taja hannun Umma wacce ta gama juyewa Naanah maganin nan tasss!,

Sakina tayi kan Naanah ta d’agaa”sannu Naanah,take fad’a,wani amai ne yazo mata ai dagudu tayi waje,suma duka suka bita,Umma fad’a take wallahi kika kuskura kikayi amai saikin biyani kud’in magani na bazakisa nayi a sarar banza ba,

Ina ai tuni Naanah ta dunga kwarara amai kamar zata amayar da kayan cikinta,Sakina ce kawai ke mata sannu,ta zuba mata ruwa ta wanke bakinta da jikinta,sannan Sakina ta gyara gurin,

Umma tacika tayi fammm!ta kalli Sakina tace”wallahi iska na wahalar dame kayan kara,ita dai Sakina bata kulata ba,ta kalli Naanah tace “ke kuma idan cikin nan bai zube ba saikin biyani kud’ina mayya kawai,Rahma ta dungureta tace”me halin mayu kindaiji kunya Naanah wai cikin shege,

Kuka Naanah ta saka don taji dungurin,bayan sun wuce Sakina ta zauna kusa da Naanah tace”Naanah kici gaba da hakuri don Allah wata rana sai labari,cikin kuka tace”maganar kenan kullum wata rana sai labari to yaushe labarin zaizo ni na k’osa inga yadda labarin zaizo,ta sake fashewa da kuka,Sakina ta rungumeta tana rarrashi,

******************

Kimanin wata biyu kenan da ciwon Ameen Alhamdulillahi jiki yayi sauk’i sosai saidai abinda ba arasa ba,kallon Momy yayi dake 6are masa lemu yace”Momyna yau ina son zuwa gida,kallonsa tayi”kai Ameen kusan kullum sai kace zaka gida ina hanaka don Allah ka bari jikinka ya k’ara sauk’i mana,yace”nifa Momy naji sauk’i sosai ba abinda ke damuna,girgiza kai tayi”bayan har yanzu my son ba kadena tunani ba,

Murmushi kad’an yayi”kai momy nifa na dena please ki barni naje gida yau badan niba????ya had’a hannayensa guri d’aya alamar rok’o,murmushi tayi shikenan my son,amma ka bari Daddynka ya dawo,

Ba haka yasoba don ya k’osa yaje yaga Naanah da iyayensa akwai wani muhimmin abu da yakeson sanar musu,yace”shikenan Allah ya dawo dashi,ta amsa amin,

Yah Marwan ne zaune a farlournsa wayarsa ya ciro ya kira lambar Naanah yaci sa’a a kunne take,itamma kunna wayarta kenan wai tayi game ko ya d’ebe mata kewa ganin Umma sun fita bakowa gidan sai ita,kiransa ya shugo,gabanta taji ya buga,ta amma ta kara a kunne kasa magana tayi”Hallo Naanah,taji muryar Marwan,a hankali tace”Na’am ina kwana,yace”lafiya lau,sai kuma dukansu sukayi shuru,

Zuwa cen yace”Naanah kiyi hakuri da abinda nayi miki nakasa iya hakuri ne akan abinda kikayi amma nayarda ba laifinki bane,wani sanyi naji ya ratsa jikina jin yayarda dani nace”nagode yah Marwan da ka fahimceni,”ba komai yace,sannan yace”Naanah inason zamuyi wata magana dake mai muhimmanci,gabana naji ya buga da k’arfi nace”to,yanzu ko yaushe,

Yace”yanzu zan fita office amma idan na dawo zan kiraki sai ki futo mu had’u a waje,nace”tom shikenan,yace”nagode Naanah inaso kisa a zuciyarki Marwan yana sonki har yanzun i luv u,kawai naji ya kashe wayar,bin wayar nayi da kallo gabana na dukan uku-uku,

Wani ringing ta sakeyi,da sauri na d’ago YAH AMEEN ya fito 6aro6aro a fuskar wayar gabana yaci gaba da bugu,kamar kar in d’auka har takusan yankewa sai kuma na danna,

“Naanah”ya fad’a cikin muryarsa me dad’a lumshe ido nayi don yadda naji kiran sunan nawa dayayi yana ratsa jikina,cikin sanyi nace”na’am yah Ameen,yace”nagode da bakizo gaisheni ba Naanah meyasa baki damudani ba ko koda mutuwa nayi ko ajikinki ko,Tuni hawaye suka wanke fuskata cikin,muryar kuka nace”ya kakeso nayi yah Ameen nayi duk bakin k’ok’arina na ganin nazo amma Umma ta hana,”ya isa kinsan banson kukanki ko,don kukan nata har cikin zuciyarsa yake jinta,da sauri tayi shuru,tace”yah Ameen yaushe zakazo,

Shuru yayi zuciyarsa na harbawa yace”yau naso nazo amma Daddy har yanzu bai dawo ba ina ganin gobe inan zuwa sannan akwai wata magana mai muhimmanci da nakeson muyi dake a goben,gabanta ya buga da k’arfi,maganar Marwan ta tuna wacce sak babu banbanci data yah Ameen”kona jina kuwa,tace”ina jinka yayanah Allah ya kaimu lafiya”Ameen ya amsa sannan sukayi sallama,

Wayar take kallo bayan ya kashe yanzun gabanta tara tara yake bugu,tace Allah yasa duk alkhairi zasu sanar dani,haka ta wuni duk jikinta yayi sanyi,ta kira Zainab ta sanar mata tace”to Allah yasa duk alkhairi ne,ta amsa da ameen,sannan ta kashe wayar tana ta tunani ta k’osa goben tayi taji me zasu fad’a mata…….

TOFAH Fans nima saidai mu had’e goben donjin abinda Ameen da Marwan zasuwa da Naanah amma ku atunaninku me dukansu suke son sanar mata?

Uhmmm nidai ko……

To idan abinda nake tunani ne ko kuke tunani a cikinsu CIKIN WAYE?

Yah Ameen ko Marwan
Muje zuwa
Fateenku ce????

      Ummu Affan

????CIKIN WAYE?????

  ❤❤❤❤
       ❤❤
          ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Gaskiya masoya ina yinku oba jiya kawai da ba kuji littafin nan ba jiya wasu harta pc suna tambaya ko lafiya wasu harda kira,gaskiya nad’i dole ma yau namuku typing ko banso ana tare????I luv u masoyan Ummu Affan❤Ina sonku a duk inda kuke????.

Bismillahir rahmanir rahim

????4⃣9⃣-5⃣0⃣

Haka ta kwana jiki duk a sanyaye sai takejin kamar wani abu ne zai sameta,tun asuba ta tashi kamar ko da yaushe aiyukanta tayi bayan ta idar da sallah,wajajen takwas na safe ta kammala komai,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button