NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Fateenku ce????????

       Ummu Affan✍️✍️✍️

????CIKIN WAYE?????

   ❤❤❤❤
         ❤❤
            ❤

STORY AND WRITING BY FATEEMAH SUNUSI RABEE’U
(UMMU AFFAN).


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

????️6️⃣9️⃣-7️⃣0️⃣

Harara ta banka masa”kaga malam cika ni meye hakan,kallonta yayi da idanuwansa da suka cenza launi”haba Naanah kefa matata ce yanzun,

Mik’ewa tayi ta kallesa wani shek’ek’e tace”a inda ba matar kenan gara tun wuri ka nemi matarka bani ba,tana gama fad’a tayi ciki,dole ne ta gasa yah Ameen domin yasan tana da ‘yanci gashi ya bata kunya agaban Momy yanzu me zatace don Allah,

Shi kuwa binta yayi da ido har ta 6ace,rumshe rinannun idanuwansa yayi yanajin wani shauk’i,amma shima yasan dole ya bita a hankali har ta gane shi mai k’aunarta da gaske ne,

Zainab ta Sayyeed kuwa tuni suka fara fahimtar juna saidai tace masa inhar yanaso ta sosa dolene karya buk’aci ta tare gidansa sai lokacin da ta kammala karatunta,ya amince don yana matuk’ar sonta,

Marwan kuwa da Salma tundaga ranar Salma bata sake ganinsa ba,itam ma tana gidan Momy nan aka barta tare da Naanah,ita ko ajikinta don don mancewa ma take da wani Marwan,

Cikin ikon Allah Didiy ya nemarwa Naanah Admission a Kaduna State University KASU,Ta fara karatunta cikin sa’a kuma ta sami fannin da take so,Alhamdulillah karatunta na tafiya yadda ya dace domin Muhseen anan gida take barinsa gurin Momy,yaron tubar kalla bazakace watansa shidda alokacinba sai kace ya shekara yaro kyakkyawa kowa kaunarsa yake,daka ta6asa ya wangale baki yana dariya,

Karatun Naanah na tafiya yadda akeso haka ma Zainab dukda ba makaranta d’aya sukeba amma masha Allahu suna yawan had’uwa domin k’awancensu sai abinda yayi gaba balle yanzun sun d’inke sun ma zama ‘yan uwa,

Ta 6angare guda Yah Ameen na damunta da nacinsa,idan zataje makaranta sai yace shi zai kaita,batabin takansa tunda yanzun Didiy ya saya mata mota kuma tuni aka koya mata,dukda dai ba wani iyawa sosai tayi ba????????,

A gajiye yau ta dawo mkrnt,kan kujera ta fad’a tana sauke numfashi saida numfashinta ya daidaita sannan ta mik’e ta bud’e fridg ta d’auko ruwa mai sanyi na gora,

Tuttulawa tayi a cup ta kafa kai saida ta shanye sannan ta aje,bedroom d’inta ta fad’a tashiga toilet wanka tayi tare da d’auro alwara ta zura doguwar riga sannan tagabatar da sallar la’asar,

Mai kawai ta shafa ta fito kitchin ta shiga tasa abinci makroni da miyar kwai,ta d’auko gorar ruwan da tarage da cup,kan carpet ta zauna ta don zatafijin dad’i ta fara cin abincin,

Sallamar yah Ameen taji bata dagi kaiba har ya k’araso,dire Muhseen yayi dake hannunsa hango Naanah da yayi ya fara zillo,

D’ago kai tayi a hankali ta kallesu,d’aure fuska tayi ganin kallon da yah Ameen ke mata”lafiya?ta tambayesa cikin izgilanci,d’an murmushi yayi yace”lafiya kalau my haert❤️

Harara ta banka masa tare da sadda kai k’asa taci gaba dacin abincinta,sakkowa yayi shima yazauna kusa da ita yace”abin ko tayi babu,d’agowa tayi fuskarsu ta had’u da ta juna,ta sake tamke fuska”meye haka,rausayar da kai yayi”a baki nakeso ki bani,

Tashi daga gurin tayi niyyaryi ya funcikota,saigata ta zube a jikinsa,zaro ido tayi ganin ya gad’e bakinta da nashi,wani irin zazzafan kissing yake aika mata yayin da take k’ok’arin turesa ta kasa,

Kukan da Muhseen ya tun tsira yasa ya saketa da sauri,ita kuwa harda hawayenta tace”ban tafeba,niyyar kamota yayi ta ruga a guje,da sauri ya d’auki Muhseen ya kaiwa Momy shi,

Tace”sanake naji uwarsa ta dawo ka kaimata shi nono ya keso,sosa k’eya yayi Momy ki basa madararsa naga kamar ta rufe k’ofar k’ilan tayi barci,girgixa kai kawai Momy tayi aranta tace”Allah dai yashiryaku ‘ya’yan zamani kenan kallo suke sunfi kowa wayau,

Yau gidan Abba Naanah ta shirya zuwa don ta gaji da abinda yah Ameen ke mata tayiwa Momy sallama ta wuce bayan ta sa6a Muhseen kafad’a ta d’au karamin akwatinta da kayansu kala biyu ke ciki,

Saman kujerar gaba ta ajiye Muhseen sannan ta zagaya tashiga ta tada,motar dabar gidan……

Sai mun had’e da yamma insha Allah????

Fateenku ce????

        Ummu Affan✍️✍️✍️

????CIKIN WAYE?????

   ❤❤❤❤
         ❤❤
            ❤

STORY AND WRITING BY FATEEMAH SUNUSI RABEE’U
(UMMU AFFAN).


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

????️7️⃣1️⃣-8️⃣0️⃣

A hankali take tuk’inta har takai badarawa,bayan tayi parking ta fito,gani tayi gidan ya sauya mata kamar bashiba,tunani ta fara aranta ‘anya kuwa gidan ne,gidan da bashi da gate yanzu kuwa naga an fad’ad’ashi,harda wani gida dake kusa da gidan Abba naga bashi da alama an had ‘esu ne,

Ina tsaye ina wasiwasi don ina tunanin ko su Abba sun tashine sai naga,”Sakina mijinta ya sauketa a mota,ya juya ganina yasa ta k’araso da fara’a,

“Naanah kece kice tare muka zo,ta fad’a tare da d’aukar Muhseen,murmushi nayi nace”Ai Anty Sakina na kasa gane gidan ne wallahi inanan ina tunanin Anya gidanne,

Dariya tayi tace”gidan ne mana ai yah Ameen ne ya gyarashi ya koma haka harda gidan malam sallau da yace zai sayar sai yah Ameen ya saya ya had’ewa su Abba,

Murmushi nayi harga Allah naji dad’in abinda yah Ameen yayi nace”ya kyauta,tare muka jera ciki,

Abba zaune akan kujera yasha wata shadda sosai yayi kyau ya k’ara haske da k’ima daman shi farin bafullatini ne,ai ina hangosa da gudu nayi kansa cikin tsartsar farin ciki,

“Oyoyo Abbana,shima rik’eni yayi cikin farin cikin ganina yace”Naanahta Naanahr Abba kece,nace”Abba nice Abbana yakake,Yace”lafiya qalau Naanahta,

Kusa dashi na zauna sannan na gaishesa,

Ya amsa cikin fara’a dajin dad’in ganina,

Sakina ma ta gaishesa,

Amsar Muhseen yayi daketa wangale masa baki yace”abokina dariyar ka arha gareta,

Nan muka fara hirar yaushe gamo,

Umma ta fito daga kitchin ganina yasa ta saki fuska,

“Maraba marhabun yau su Naanah ne a gidan,

Naanah ta d’ago cike da mamaki ta kalli Umma,sai tasaki fara’a taje gabanta ta duk’a,

“Umma ina wuni,d’agota tayi ta rungume,ai Naanah kusan suman tsaye tayi tace”Lafiya qalau ‘yata ya kika baro mutanan gidan,

Ai Naanah saboda tsananin mamaki kasa magana tayi tana kallon Umma,

Umma ta fara hawaye tace”Naanah na cutar da rayuwarki kiyi hak’uri ki yafemin ko nasamu sauk’in abinda ke damuna tabbas na cutar dake amma naga illar cutar da d’an wani,

D’a na kowa ne kuma idan ka rik’i d’an wani tsakani da Allah kaima sai kaga naka basu wulak’anta ba,don bakasan wataran inda zasu fad’a ba

Naanah ki yafemin wallahi naga illar abinda na miki ko yanzun kece a sama,

Wai ashe duk abinda nake miki iyayenki sune ke tallafawa rayuwarmu,

Kuma d’ana shine yamiki ciki,Naanah ki yafe mana nida Ameen don Allah duk kuskure na ne,

Da sauri na rufe mata baki”a’a Umma ba laifinki a ciki k’addara ce kuma daman cen Allah ya rubuto sai hakan ta faru,

Wallahi ban ta6a rik’eki a zuciyata ba na yafe miki Umma Ke uwata ce wallahi har abada bazan dena kallonki a matsayin uwa ba,

Wannan ranar na dad’e ina jira na ganin nima kin d’aukeni ‘ya,to Alhamdulillah Allah na gode maka dakasa Ummata ta gane gaskiya,

Rungumeni Umma tayi tana kuka”nagode Naanah hak’ik’a ke ‘ya ta garice da ko wacce uwa xatayi alfahari da samunki Allah ya miki albarka,gaba d’aya muka amsa da ameen,

Yah Ameen da ya shugo duk yaji abinda akace murmushi yayi cikin jin dad’in abinda ya faru sannan ya juya,bai shugoba don karsu gansa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button