NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Naanah kuwa fara ce doguwa mai yalwal gashin kai bak’i wuluk,tana da manyan idanuwa masu haske da kyau,hancinta d’an dogo ya bud’e kadan daga k’asa,la66anta sirara masu kyau kalar pink bakinta k’arami mai kyau zubin hakoranta kwanin ban sha’awa,

Bata cika k’iba ba gaskiya siririya ce amma fa bacen ba don akwai cikar diri da mazaunai ga hifs,shine suke mata gorin sirinta wacce ba k’aramin kyau ta mata ba har kishi suke da irin kyawun da Allah ya bata,

Gaba d’ayansu sukayo kanta harda Umma jin irin maganar da ta fad’awa Rahma nan suka rufar mata da duka,saida sukai mata ligiligi duk sun ji mata ciwo…

Muje zuwa Fateenku ce????????

Ummu Affan
????CIKIN WAYE?????

❤❤❤❤
     ❤❤
        ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)

????Duk sunji mata ciwo ko motsi ta kasa,amma hakan baisa sunji tausayinta sun rabu da ita ba saima ci gaba da sukayi da bugunta,

Bismillahir rahmanir rahim

????1⃣5⃣_1⃣6⃣

“Abba da Yah Ameen suka shugo ganin irin ta Asar da suke yasa suka k’arasa da sauri Yah Ameen ya ture Rahma da Sakina suka fad’i Abba ya d’aga Umma da ke zaune kan Naanah tana bugu,Yah Ameen ya rufe su da bugu suma saida ya bigesu sosai Umma cewa take”karabu da su Ameenu ko so kake ka kashemin yaran naea,hargagin da ta ke baisa ya rabu dasu ba suma saida ya musu dukan tsiya,

Kin kimar Naanah yayi ya fita da gudu,cikin mota yasa sannan Abba ya shiga wanda ya gama zage Umma tas,sannan suka wuce asibiti,lokacin da suka isa Naanah ta gama fita haiyacinta ko numfashinta sama-sama ya ke futa,nan likitoci suka yi kanta don ceton rayuwarta,

Yah Ameen ya kasa zama yayi nan yayi nan a bakin d’akin da aka shiga da ita Abba kuwa xama yai ya buga uban tagumi sosai ya ke tausawa rayuwar Naanah ya rasa me yarinyar ta tarewa Karimatu take mata irin wannan k’iyayyar,

Bayan likita ya fito ya tabbatar musu numfashinta ya daidaita yanzu ta sami barci ne sun d’aura mata k’arin ruwa,

Shiga suka yi d’akin Yah Ameen ya zuba mata ido idanuwansa sunyi jawul saboda tsabar 6acin rai,ji ya ke kamar ya me ransa duk ajagule yake,

Saida aka kira sallah sannan suka fita,masallacin asibitin sukayi sallah suna dawowa suka iske na tashi,ba abinda nake sai kuka,da sauri suka k’araso,Yah Ameen ya tallabo ni jikinsa ya na bubbuga bayana cikin sigar rarrashi yace”Please Naanah kiyi hakuri kukan nan ba abunda zai k’ara miki sai ciwo,

Na d’ago fuskata cikin kuka nace”Yah Ameen me na musu suka tsane ni nima fa jininsu ce meyasa sukemin hakan Umma bata sona bata k’aunata Yah Ameen me yasa please na lura kai da Abba kamar kuna 6oyemin wani abu don Allah ku fadamin idan ba Umma ce ta haifeni ba ku futo kusanar da ni don Allah!????,

Ta k’arashe maganar da sakin wani gigitaccen kuka,gaba d’aya sai suka rud’e,cikin inda inda Abba yace”uhmm Naa..nah ki kwantar da hankalinki Ummarku ita ta haifeku dukanku,girgiza kai ta fara”uhm uhm Abba ina kokonto don ba uwar da zata dingawa ‘yar cikinta haka,

Yah Ameen yace”haba Naanah ki kwantar da hankalinki maganar da Abba ya fad’a miki gaskiya ne,sadda kaina k’asa nayi ina matsar hawaye,Yah Ameen ya d’ago fuskata yana sharemin hawaye,

Da yamma aka sallame mu bayan ruwan da aka samin ya k’are,da sunce kwana zamuyi Yah Ameen ne ya matsa aka bamu sallama aranar,

Saida ya biya da mu wani babban Super Market ya min sayayya mai yawa,sannan muka biya gurin masu sayarda kayan marmari yasaya min muka wuce gida,

Da sallama na shiga farlourn amma ba wanda ya d’ago ya kalleni balle ya amsamin,kaina k’asa na wuce d’akina,inajin lokacin da Umma taja wani dogon tsaki mtsuww,nidai na shige da saurina,kan katifa na fad’a na saki wani sabon kukan ko sai yaushe hawaye zaibar zuba a fuskata Allahu a’a lamu,

Washe gari kuwa tun asubar fari Umma ta tadani,saijin ana maka min bugu nayi a furgice na farko tace”munafuka algunguma shegiya saiki tashi kin wani rashe rashe kina barci kamar kin sami gidan ub…sai kuma tayi shuru,a furgice na d’ago ina kallonta,hawaye ya k’wace min,cikin kuka nace”Umma me kika ce?,

Tace”to munafuka bance komai ba bare ki kaini gaba cewa nayi ki tashi kiyi aiki tunda ba bayi kika bari agidan ba,sannan ta fita fuuuu!sai da naci kukana mai isata sannan na tashi,na fita na fara aikin,wanke-wanke tun najiya da banyi ba ina asibiti sune tule ba wacce tayi duk sun bushe haka na zauna nayi sannan na share gidan na d’aura abinci,

Da rana ‘yan uwan Umma wasu duk sunzo murnar sallah haka naci aikin girka musu abinci,ba godi bare na gode,

Fateenku ce

Ummu Affan✍????
????CIKIN WAYE?????

❤❤❤❤
❤❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)

AREWA WRITERS ASSOCIATION


????(Arewa ginshikin al’ummah)????


Bismillahir rahmanir rahim

????1⃣7⃣-1⃣8⃣

????Ba godi bare na gode,har suka tafi,

‘Da yamma muna zaune tare da Zainab a gidansu nace”Zainab abinda Umma ke min yana matuk’ar da muna,zuciyata na yawan bani cewa ba ita ce ta haifeni ba,Zainab ta share min hawayena tace”nima kaina wannan abu na d’aure min kai kuma ina zargin ke ba ‘yar gidan bace,domin ba uwar da zata haifi d’a ta nuna masa tsana yadda Umma ke miki,

Na kalli Hajiya da ke zaune kusa da mu,kanta na k’asa saboda tausayin da takewa Naanah gaskiya ita kanta abun yana d’aure mata kai,nace”Hajiya daman mutum yana haihuwar d’a ya nuna bai k’aunarsa kamar yadda Umma ke min,

Ta kalleni cikin tausayawa tace”Naanah ba wanda zai haifi yaro yace bai sonsa kodai akwai abinda kike mata ne?,girgiza kai na fara ina hawaye,nace”Hajiya ba’abinda na ke mata a kullum burina in faranta mata ko na samu ta soni amma duk abinda na ke a banza bata gani yanzun ya zanyi da raina Hajiya,na k’arashe maganar ina kuka wiwi????

Hajiya Tace”kin ta6a tambayar Abbanku kuwa?,nace”duk lokacin da abun ya da meni ina tambayarsa kullum maganarsa guda ce ita ta haifeni,Hajiya taja numfashi sannan ta dafa Naanah tace”kici gaba da hakuri Naanah watarana sai labari,share min hawaye kawai Zainab keyi tana kara bani hakuri,

****************

Zaune ya ke shi d’aya a farlour,yana tunanin Naanah matuk’a ya ke jin tausayinta gashi Umma ta musu shamaki tace yadena kula Naanah yarasa ya zaiyi,kimanin wata guda kenan rabunsa da gidan zuciyarsa ta gaza hakuri da rashin ganinta shiyasa yau yazo ya ganta ko zuciyarsa ta masa sanyi,

Da sallama na shugo farlourn sanye nake da uniform na islamiyya,ai kuwa karaf muka had’a idanuwa,muka k’urawa juna ido,ganin bazan iya jure kallonsa ba yasa na sadda kaina k’asa Yah Ameen yana da kwarjini sosai hakan yasa tunda na tsaya ko k’afata na kasa d’agawa daga inda na ke,gaskiya Yah Ameen ya had’u,yana da wata irin baiwa wacce inhar mace zata kallesa dole taji wani abu a jikinta,

Da k’yar na samu na d’anyi tafiya da niyyar in shige d’aki,har na kusan shiga sai naji yace”Naanah tsaya ina son magana da ke,tsayawa nayi chakk!,ni ban juyo ba kuma ban tafi ba,ya k’araso kusa da ni idonsa na kaina,yace”Naanah nasan yanzu kin girma kinsan abinda kikeyi,ina so ki tsaida hankalinki waje d’aya ban son gayyace-gayyacen samarin banza domin ba da kinyi (SSCE)za’amiki aure ba,ina son kici gaba da karatunki,ya d’anyi shuru tare da wani guntun murmushi sannan ya d’aure fuska yace”kinji na rantse miki wallahi na ganki da wani saurayi ko naji labarin kina kula wani sai ranki ya 6aci kina JINA!ya k’arashe maganar da tsoratarwa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button