NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Muna Tudun wada,bayan yayi Mameensa ta masa tsarki suka shugo direbanmu yajamu zuwa gida,ashe rabon ayi tsautsayi ne ya tsayar damu,domin muna zuwa gida aka nemi Firdausi sama ko k’asa aka rasa,nan fa hankalinmu yayi mugun tashi,waya muka farayi Igabi ko mun barota cenne akace’a’a,nan take muka koma gurin da Fahat yayi fitsari amma babu ita babu alamun ma me kama da ita,

Sosai hankalina yatashi nan take na bada sanarwa gidajen Radio da Tv,kai abu fa yayi nisa kwana d’aya biyu uku babu Firdausi hankalin mu yatashi sosai gaba d’ayanmu duka Family domin Firdausi kowa a Family na k’aunarta domin yarinya ce mai saurin shiga rai nashaku sosai da Firdausi ko a cikin yarana ita tadabance Allah ya sani ina k’aunar Firdausi sosai haka Mameenta da sauran ‘yan uwanta,mun shiga tashin hankali sosai na rashinta sanadiyyar hakan na kamu da ciwon zuciya ga hawan jini saboda ya waita tunanin da nake,har zuwa wannan lokacin bamu sake ganin me kala da itaba saiyau,

Gaba d’aya gurin akasa ka kabbara “ALLAHU AKBAR,Abba yace”ni kuwa wata rana mun dawo sallar la’asar ni da Ameen lokacin bai dad’e da kammala secondry ba yana k’ok’arin shiga jami’ar Ahmadu Ballo dake Zaria,shine ya fara ganin yarinya,yace”lah Abba jibi wata yarinya cen sai kuka take,waigowa nayi mukayi ido hud’u da ita nace”kai Aminu ka cika jajibe jajabe ina ruwanka da ita haka kawai daga ganin yarinya kasani ma ko aljanace,jibeta fa,saboda shigar dake jikinta ta wata ‘yar kanti me tsada gashi kanta tasha kitson kala me kyau yarinya kyakkyawa,

Haka muka wuce Aminu sai waigen ta yake najasa muka shiga gida,

Bayan mun fito sallar magrib har zuwa lokacin yarinyar na nan,yace”Abba har yanzu yarinyar cen bata tafiba,harararsa nayi najasa muka wuce,har muka dawo isha’i ta nanan da yake idan mukaje sai mumyi isha’i muke dawowa,

Nan Ameen harda kuka yace”kai Abba yarinyar nan daga gani takasa gane gida ne don Allah mu dauketa mutemaka mata Abba,nace”Ameen kayi shuru yarinyarcen da kake gani k’ilama aljanace ni ban yarda da ita ba,

Haka muka wuce gida,ranar Ameen baiyi barci ba da tunanin yarinyar ya kwana,koda asuba da naje tadasa muje masallaci zaune na iskesa yana kuka”lafiyarka Ameen,na tambayesa,yace”Abba yarinyar nan da ita na kwana araina,naja tsaki”kai kasani wuce muje masallaci,

Haka yabini,mukaje damuka dawo muka iske yarinyarnan kwance a gurin tana kuka sosai,ashe da zamu duhune yasa bamu ganta ba,ai da gudu Ameen yayi kanta ya d’auketa “yi hakuri princess…..

Kuyi hakuri da wannan wallahi kwana biyun nan ina busy ne amma karku damu????

Fateenku ce????????

       Ummu Affan✍????✍????✍????

????CIKIN WAYE?????

❤❤❤❤
❤❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bidmillahir rahmanir rahim

????5⃣3⃣-5⃣4⃣

“Yi hak’uri princess,nan ya fara jijjigata alamar tayi shuru,kallona yayi idanuwansa cike da hawaye”please Abba don Allah mu temaki yarinyar nan,numfashi naja nace”tom shikenan,muka nufi gida da yarinyar wacce ta kwanta kafad’ar Ameen zuwa lokacin tayi shuru,

Da sallama muka shiga,Umma wacce ke kitchin tana had’a abin kari ta fito,shak’ek’e tabi Ameen da kallo kafin tace”meye haka me zan gani haka,Ameen ya aje yarinyar gaban Umma yace”Wallahi Umma abin tausayi haka muka tsinci yarinyar nan sai kuka take,harara ta banka masa”kai dai Ameenu kaciga jajibe-jajiben tsiya daga ganin yarinya kuma saiku d’auka me ruwanku da ita wayasani ma ko aljana ce,

Ganin fad’an da Umma keyi tasa yarinyar run gume Ameen tana cewa “nidai bansonta Yaya kakaini gida,cike da mamaki suka kalli yarinyar jin ta iya magana amma ba sosai ba,

Umma tajawota taja kunnanta nan take tasaki kuka tace”kujimin kinibabbiyar yarinya nice bakiso don ubanki saidai kik’i iyayenki dasuka yarda ke wayasani ma ko shegiya ce,kuka sosai yarinyar take,

Ameen ya amsheta hannun Umma yace”haba Umma yarinyar nan me tasani,rik’e baki tayi”ehye to maza ka kwasheta ka mayar inda ka d’aukota bazan iya ba,Abba yace’yarinyar nan dai tsintarta mukai zataci gaba da zama gidan nan har Allah ya nuna mana ‘yan uwanta,

“Wanne gidan Umma ta fad’a cike da karaji,Abba yace “wannan gidan wallahi Karimatu ki fita idona inason ki dauki yarinyar nan tamkar ‘yar da kika haifa da cikinki banson ko da wasa tasan ba mune iyayenta ba duk ranaar kuwa da kika sanar da ita bamune iyayenta ba to abakin auranki,

Wata kururuwa Umma tayi tace”ikon Allah yau daga k’arfin hali to wallahi bari kaji na tsani yarinyarnan ban sonta ban kaunarta kuma bazan ta6a sonta ba har abada,

Ameen ya rungume yarinyar yana hawaye yace”Umma don Allah kiyi hakuri kiso yarinyarnan karki cutar da ita,tsaki taja ta wuce kitchin tana masifa,

Kallon yarinyar yayi”meye sunanki?shuru tayi kamar ba itace tayi magana d’azunba,Abba yace”kawai mu dunga kiranta Naanah tunda ko wacce mace Nana ce,Ameen yace”haka ne,

Bayan Umma ta gama abin karyawa,duka suka had’u domin karyawa,Rahma da Sakina suka kalli Naanah cike da mamaki,Sakina tace”Umma wannan wacece,tsaki taja kafin tace”shegiya ce iyayenta suka yar amma Abbanku da Yayanku sun kwaso,Shuru sukayi suna hararar Naanah ba halinsuyi magana don sosai suke tsoran yayansu Ameen bai musu da sauki,

Kowa aka sama abin karyawa banda Naanah Ameen ya zaunar da ita jikinsa ya fara bata nasa,sosai taci saida ta k’oshi sannan yaci ragowar,Umma ta rik’e baki”Ameenu kana son in sa6a maka wallahi akan yarinyarna kuma yanzun nan zata bar gidan nan,

Kallon Umma yayi cikin hawaye”Umma idan har kika matsa sai yarinyar nan tabar gidan nan to saidai ki rasani domin zan dauketa mu tafine,duka suka kallesa yace”Umma inhar kina son farin cikina to ki rik’e Naanah don Allah,

Batason ta rasa Ameen don sosai take kaunarsa hakan yasa tace”naji na amince amma kusani har abada bazan ta6a sontaba hakama yarana bazasu sota ba,

Shi baidamu da wannan ba yasan indai Naanah na gidan dole wata rana tasota,

Dakansa ya shiga kitchin yasa ruwan zafi yawa Naanah wanka,hardasu shafa sudai iyayensa na kallonsa,da rana ya amshi kud’i gurin Abba yasayowa Naanah kayan gwanjo don ta dunga cenji,idan an mata wanka,

Sosai Ameen ke kula da Naanah wacce suka saba sosai shine wankanta shine bata abinci a baki saita k’oshi yakeci,komai shike mata wanka wanki wanke bayan gida idan tayi yakaita kitso da kunshi domin Umma ta rantse bazata mata komai ba,

Sosai suka saba,da yasami kud’i nan take zai k’arar dasu akan Naanah saya mata kaya takalma da kayan kwad’ayi su sweet choculate da dai sauransu,Umma na matuk’ar jin haushin wannan abu tayi masifar da bala’in amma abanza,

Suna zaune a barandar gidan suna shan iska Ameen na tsefewa Naanah kitso yace”kan nan naki ya tsufa Naanah kusan sati biyu dayinsa ni inason ki dunga yawan kitso kar gashinki ya lalace,cikin shagwa6a tace”kai yah Ameen nifa banson kitso babu abinda kaina yayi sai ka tsefemin,dariya yayi”ke kuwa kinga yadda kanki ya tsufa,tace”uhmm uhmm kaidai kawai kafison me kitson nan ta matseni ina kuka tamin,

Yace”kai!kai!!badai matsemin princess take ba,dariya ta tuntsere tace”matseni take ni kuma na cijeta,rik’e baki yayi yana murmushi”haba dai princess kidena cizo idan ba haka ba zan dena sayamiki choculate tace”sorry Yayanah na dena,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button