NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Fareeda tayi kan Fahat zata daka,nan yayi ta wahalar da ita suna kewaye farlour,kan kujera ta fad’a tana kuka,Sayyeed yasa dariya”Anty Fareeda ba k’arfi sai tonon fad’a,kamar jira take ta sake sakin kuka shima tayi kansa,amma shima wanata yayi suna ta mata dariya jikin Didiy ta zube tana kuka,yace”Rabu dasu kai Sayyeed na fasa siya maka motar da kace kanaso kai kuma Fahat karatun da kace k’asar Misira zaka na masa kaika sai in gani,ai tuni suka dawo k’asan Fareeda suna bata hakuri,ita kuwa ta saki dariyar mugunta tace”yauwa Didiyna haka nakeso,

Sayyeed yace”haba dai my Antynmu kinsan bamu haka dake,Fahat yace”Anty Fareedarmu kiyi hakuri bamu sakewa,Mamee me zatayi ba dariya ba tace”kai Didiy gaskiya a ma yarana afuwa,kalon Fareeda yayi tace”tunda Mamee tasa baki to a musu,

Gaba daya suka rungume juna tare da addu’ar Allah ya nuna musu ‘yar uwarsu,sannan suka shiga mota,Sayyeed yajasu sai hosbital…….

Fateenku ce????

        Ummu Affan ✍????

Please Share and comments
????CIKIN WAYE?????

  ❤❤❤❤
       ❤❤
          ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

????4⃣5⃣-4⃣6⃣

Suna isa suka iske Abba,Daddy,Momy,Umma sai Rahma,sosai suka tarbesu cikin fara’a da girmama juna,da gudu Fareeda ta k’arasa gadon da Ameen yake kwance,an jingins masa filow a bayansa,ya rame sosai sai haske da ya k’ara,

“Sannu yah Ameen ya jikin naka,”da sauk’i,ya fad’a a hankali donshi yanzu ko magana baisonyi burinsa bai wuce yayi ido biyu da Naanahrsa,Su Didiy suka masa ya jiki,Sayyeed ya zauna kusa dashi yana gaishesa,shima Fahat haka,

Didiy yace”me ke damunsa ne,naga lokaci guda ya zube haka,Daddy yace”kadai bari yasawa zuciyarsa tunani gashi har ta kamu da ciwo,subuhanallah suka k’walalo ido gaba daya????Mamee tace”ciwon zuciya kai kuwa Ameen wanne irin tunani ne wannan,Umma tace”haka kawai yasawa zuciyarsa tunanin yarinyar da bazai ta6a samunta ba,kallonta sukai yayin da Fareeda da sauri ta k’araso gabanta,tace”wacce yarinya don Allah karkice bani bace taya Ameen ya fad’a ciwon son wata ni yabarni????kuka sosai Fareeda take,

Duka gurin suka bita da kallon Mamaki,Umma kuwa ta saki baki da hanci tana kallon Fareeda aranta tana fad’in wannan kyakkyawar yarinyar badai son Ameenu take ba amma indai ko haka ne duk yadda zanyi sai nayi ya aureta yaro arziki na binsa yanason kwaso tsiya,d’aga Fareeda tayi daga durk’usan da tatyi tace”kwantar da hankalinki ‘yan mata kina son Ameenu ne,da sauri Fareeda ta d’aga kanta alamar eh,Umma tayi wani murmushi mai manufofi da dama,tasa hannu tana sharewa Fareeda hawaye tace”kisa aranki tamkar kin auri Ameenu share hawayenki ‘yata,(Su Umma ba’a abu don Allah),

Gaba d’aya kowa kallonta yake cike da mamaki shi kuwa Abba murmushin takaici yayi don tuni ya gama gano manufarta nayin hakan,Didiy da Mamee sai sukaji dad’in abinda Umma tawa Fareeda kunsan mai d’a wawa,

Ameen kuwa aransa yasa har abada bazai iya auran Fareeda ba bawai don bata kaiba a’a shikawai Naanahrsa yake so kuma bayajin zai iya had’ata da wata,kai shifa a zuciyarsa babu sauran gurin da wata ma zata samu muhalli,

Sunci sa’a a ranar aka basa sallama badan yaji sauk’i ba sai takurar likitan da Ameen yayi akan ya sallamesa koshi ya sallami kansa,sosai Umma ta fara fad’a amma Daddy tace karta damu tunda baisan asibitin su koma gidan akwai likitan da zai dunga dubasa,

Koda suka kama hanya ya d’auka gidansu za’a kaisa amma sai yaga sun nufi gidan Daddy kamar yayi magana sai kuma yayi shuru ganin k’ok’arin da suke tayi kansa idan yace wani abu sai yake ganin kamar bai musu adalci ba,

Nan gidan Fareeda ta tare sosai take kula da Ameen,duk da Momy ke masa komai amma ita ma tana bakin k’ok’arin ganin ta faran ta masa,

Yana zaune a bedroom shi d’aya tunani kawai yake CIKIN WAYE?jikin Naanah wasu hawaye suka zubo masa yasa gefen hannu ya goge,

Wayarsa ya jawo ya nemo numberta ya danna kira,akashe take buturiyar nan ta cikin waya ta sanar masa,lumshe idanuwansa yayi tare da sakin wayar kan bed,Fareeda da ta dad’e da shugowa ta k’araso zaunawa tayi kusa dashi tare da sakin a jiyar zuciya,”Ameen”ta kira sunansa cikin sanyi murya,a hankali ya bud’e idanuwansa ya kalleta baice mata komaiba,ta kallesa ido cikin ido,tsigar jikinta taji na tashi tayi saurin kallon gefe,ta6e baki yayi,yasake lumtse idanuwansa kamar maijin barci,

Tace”Ameen me yasa baka sona?,bai tankamata ba taci gaba dacewa”nidai nasan nakai macen da kowa zaiso tu meye narasa,mud’e ido yayi yana kallonta,ta mik’e tana jujjuya baya tace”kalleni sama na k’asa nasan ko agasar kyau idan banzo ta d’aya ba to dole nazo ta biyu,mutane da yawa suna sona ‘yayan manya da manyan attajirai amma nak’i bawa kowa dama saikai haba Ameen me yasa kake wulak’antani koni bankai macen da zaka kalla bane,

Cikin tsawa yace”ke!,sosai ta furgita,yace”baki kaiba kuma har abada bazaki kai macen danake soba,gara tun wuri kiba maneman naki dama su fito kafin damarki ta ku6uce,yana gama fad’ar haka ya juya mata baya,kuka ta saka me ciwo tafita da gudu,tsaki yaja tare da sake lumshe idanuwansa,wani abucen da ya faru wani lokaci yake tunowa,bai fad’a a filiba balle ni ‘yar rahoto na ruwaito muku shi????,

********************

Umma na gani bakin k’ofar gida tana ta surfa bala’i,”Malam kazo ka bud’emin k’ofa,banza yayi da ita yayin da ni da Rahma mukayi shuru musamman ni da nayi zuru-zuru,bugun k’ofar take sosai,

Na kalli Abba cikin fuskar ban tausai na had’e hannayena waje d’aya na d’aga a lamar ban hak’uri????nace”Please Abba don Allah ka bud’ewa Umma k’ofa kayi hakuri ta koma gidan nan,kallonta yayi”yace”rabu da ita Naanah sai kace bata da dangi wannan masifar har ina,

Nace”kayi hakuri Abba Umma addu’a take nema,Rahma tace”Abba in bud’e mata don Allah kayi hakuri,bai magana ba,nasake rok’onsa “shike nan Naanah taci albarka cinki ki bud’e mata,cike da murna na bud’e mata k’ofar ko ba komai yah Ameen idan yaji Abba yasaki Umma bazaiji dad’i ba shiyasa tun kafin yaji gara ta kome,me zai faru?ai ina bud’ewa Umma k’ofa ta wani ban gajeni saida na bige da bango na wuntsila,harara ta bankamin tace”sanadinki Malam ya kwance igiya d’aya ta auranmu abinda tun muna yara bai minba to zaki gane kuranki wallahi,tayi ciki fuuuw!!,kakka6e jikina nayi tare dabin bayanta don zuwa yanzu yaci ace nasaba da halin Umma,

Zaune nake ina wanke-wanke,sai na dungajin motsi acikina sosai na tsorata na mik’e zunbur nasha wani abunne,ganin banga komai ba nasake zaunawa,wani motsin na sakeji wanda yafi na d’azun sake mik’ewa nayi na d’aga rigata,sainaga cikina ne ke motsi har wani harbawa yake,nan take hawaye suka gangaromin,Allahu akhbar duk wahalar nan danakesha ashe cikin nan shi lafiya ma yake k’arawa,ganin cikin bai girma sai na d’auka ko ya fucene saboda wahala ashe yanan,watansa biyarfa kenan,zaman da 6aro nayi ak’asa ina kuka ina bugun cikin,

Umma ta fito bina tayi da kallo kafin taja tsaki,sa6ar mayafinta tayi sai gidan k’awarta Asabe da tace ta samo mata wani magani mai k’arfi na zubar da ciki tace mata saidai Naanah bata shaba amma tanasha zai fita fittt!,

Cike da farin ciki na isa gidan bayan sun gaisa tace”Asabe naganar maganin nan nazo,tace”ai ina ganinki nasan da hakan,d’aki ta shiga ta fito da wani k’ullin magani tace”gashi saidai dubu biyar ne,saida Umma ta amshi maganin ta k’ulle a ha6ar zani tace”a’a Asabe bazamuyi haka dake ba dubu biyu zan baki,Asabe tace”wallahi bazan yarda ba kinsan atar da nasha kafin nasamo miki maganin na kibada hud’u da d’aribiyar,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button