CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Bismillahir rahmanir rahim
????3⃣9⃣-4⃣0⃣
????Da sauri Hajiya da Zainab suka kallesa jin abinda yake cewa,Hajiya tace”kana da hankali kuwa Marwan a tunani na kaine mutum na farko da zaka fara tausayawa Naanah amma Marwan kaban kunya ashe ba sonta kake ba,jin abinda Hajiyarsa ta fad’a yasa jikinsa d’anyin sanyi amma zuciyarsa tak’i aminta cewa Naanah batasan CIKIN WAYE?ba yama za’ayi ya yarda da hankan,
Yace”Hajiya ina kaunar Naanah saidai wannan abinda da tayi ya 6atamin rai har tasa zuciyata na shakku akanta ban yarda bata san CIKIN WAYE?,k’arya take wallahi kuma sai na rama abinda tayimin,yafita a fusace,
Hajiya girgiza kai tayi cike da takaicin kalaman Marwan,harga Allah jin Naanah take kamar ‘yarda ta duk’a ta haifa,
“”””””””””””
Naanah gida ta shiga ta kasa zama kuka kawai take,cike dajin takaicin hanata shiga mota da Umma tayi,ko wanne hali yah Ameen yake yanzu?ta tambayi kanta,bata da amsa ta zauna taci gaba da kukanta,saida ta gaji don kanta tayi shuru tunda ma me rarrashi,sai ajiyar zuciya take daga bisani barci 6arawo ya kwasheta a gurin,
“””””
Acen asibiti kuwa bayan isarsu nan take likitoci sukayi kan yah Ameen domin ceton rayuwarsa,suna nan sun kasa zama Umma sai masifa take”Wallahi wannan mayyar yarinyar ta kashemin d’ana namiji tilo bazan yarda ba wannan wacce irin rayuwa ce,an kwaso mana abinda zai cucemu,duk wad’anda zasu wuce sai kallonta ake wasu sun d’aukama ko mahaukaciyace sabon kamu????,
Abba yace”Allah ya shiryeki Karimatu yanzu a cikin asibitinma sai kin nuna halinki,harara ta watsa masa”ai gaskiya na fad’a inhar Al-ameen ya mutu ita sai na kasheta,matsawa yayi cen gefe yace”bari na baki guri kar a d’auka tare muke,tsuwww taja tsaki”aikin banza harara a duhu kai kasani cen ta matse maka,Rahma bata ta6ajin haushin Umman ba irin na yau tace”kai Umma a asibiti fa muke nan ma saikin nuna halin naki,”kinci gidanku Rahma don kaza kazanki nayi ko zaki bugeni ne,
K’unk’unai Rahmar keyi ta koma kusa da Abba tana cewa”kya k’arata ke kad’ai,Umma ta mulmulo mata wata ashar,nan mutane suka hau magana,hakan yasa Umman yin shuru tana na ciki-ciki burinta ta koma gida ta k’are kan Naanah jira take likitocin su fito,
Wayar yah Ameen dake hannun Rahma ta hau ringing,Daddyna haka aka rubuta,ta amsa bayan ta gaishesa yake tambayar me wayar tace”Wallahi munanan asibiti an kawosa babu lafiya ko motsi baiyi,ai salati taji ya dauka ya tambayeta wanne asibiti ta sanar masa ya kashe wayar,
Ba’afi minti sha biyarba sai gasu a rud’e,Momy harda hawaye,nan suka gaggasa dasu Abba da Umma,Rahma ta gaishe su,
Zuwansu Daddy da minti goma likitoci suka fito suna share gumi,nan sukayi kansa gaba d’aya suka had’a baki”likita ya jikin nasa,murmushi yayi”jiki alhamdulillah mun samu ya farfad’o wani abu aka fad’a masa da yatada hankalin ko yagani,shiyasa ya sume amma gaskiya zuciyarsa akwai matsala amma zamu d’aurasa kan magani tun abun ba wani girma yayi ba,sannan da ya farko yana ta kiran ko Naanah yake cewa gaskiya idan tana kusa muna son da ya farko barcin da ya samu ya ganta domin inaga itace yake yawan tunani har yasama zuciyarsa ciwo,
Cikin takaici Umma tace”ai kuwa bazan gantaba idaiko Naanah ce kujimin ta k’adarin yaro au da ya farko bai kirani ko Abbansa ko ‘yan uwansaba sai wata shegiya Naanah,da mamakin likitan yake kallonta haka su Momy,
Abba yace”za’ayi k’ok’arin likita rabu da matarnan mun gode,likitan ya wuce aransa yana tunanin anya matar nan bata da ta6in hankali,
Gaba d’aya suka shiga d’akin da aka kwantar da Ameen barci yake sakamakon allurar barcin da aka masa,Momy ta kira waya gida tacewa mai aikinta Lami ta shiryowa abin abinci mai ruwa-ruwa irin na marasa lafiya,
Wajen biyar na yamma Ameen ya fara bud’e idanuwansa ahankali,lokacin su Momy sun idar da sallah tuni suna zaune a tabarma da Lami tazo da ita da kuma abincin da takawo,Daidai kuma shugowarsu Abba sun dawo sallah danma sun dad’e zaune a masallacin suna addu’o’i,
“Naa”Naan”Naanah!!!,ya fad’i na k’arshen da k’arfi gaba d’aya suka mik’e sukayo kansa,suka rurruk’eshi,Bud’e idansa yayi ya zuba musu,sai kuma ya fara waige-waige,dafe saitin zuciyarsa yayi hawaye na zubar masa”ina Naanah,ya fad’a cikin wata irin murya mai sanyi ta marasa lafiya,
Umma cikin 6acin rai tace”kai wai wanne irin yaro ne,yauni na shiga uka ni Karimatu anya yarinyarnan ba shanye maka kurwa tayiba,Momy tace”Haba Karimatu meye hakan da wanne kikesoyaji ciwon da yake fama dashi ko masifarki,shuru tayi don ba kad’an take girmama Momynba saboda tasan akwai masu gidan rana balle yadda suka rik’e mata Ameen abin na mata dad’i,tace”ai Hajiya ne shi ya fiye cika ciki wallahi,
Daddy yace”Wai wacece Naanahr nan ne,Abba yace”K’anwarsa ce,Momy tace”anya k’anwa kad’ai kodai yana sontane,Umma zatayi magana Abba ya rigata fad’in “eh inaga dai yana sonta ne don komu bai ta6a sanar damuba,Momy tace”gaskiya yana sontane akawo ta yaganta Malam kar wani abu ya samesa,Umma tace”Hajiya ki bari kawai ba wani sonta da yake yarinyar da bata da tarbiyya cikin shegefa tayi,
Momy da Daddy suka kwararo ido????????tare suka furta”CIKIN SHEGE,Umma tace”k’warai kuwa shiyasa bansonshi da ita shine zaisawa zuciyarsa tunanin banza,sukace”gaskiya kam gara ya hakura ya nemo ta gari,
Ameen yasaki wani rikitaccen kuka yace”ba yarda za’ayi Naanah taui cikin shege idanko har hakanne to CIKIN WAYE?,Umma tace”ohoo to wa yasani,kuka yaci gaba dayi kamar wani k’aramin yaro yana girgiza kai,su kuwa Daddy da Momy sai rarrashinsa suke amma yak’i shuru,
Wata tsawa da Umma ta buga masa gaba d’aya gurin suka toshe kunne saboda k’ara,harni dake gefe saida na tushe kunne,cikin fad’a tace……….
Fateenku ce????
Ummu Affan✍????
Share and Comments
????CIKIN WAYE?????
❤❤❤❤
❤❤
❤
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
Bismillahir rahmanir rahim
????4⃣1⃣-4⃣2⃣
Tace”aikin banza kai bari gaji ba kuka ba ko gajijiyar mutuwa kake kabar ganin Naanah,kai bari kaji yau Naanah zata bar mana gida ba sai gobe ba,
Kuka sosai yasaka kai kace ba wannan Ameen d’inba mai taurin zuciya tsayayyen namiji yau shine ke kuka kamar wani k’aramin yaro,yace”Umma inhar kika kori Naanah to daidai yake da kirasani gaba d’aya,ina son kisani Umma Naanah ita ce farin cikin d’anki rasata daidai yake da rasa rayuwar d’anki,
Hannu tasa aka????tace”yau na shiga uku ni Karimatu Al-ameenu ni kake gayawa magana haka,sai takama kukan k’arya tana cewa”amma ba komai duk Malam kaine silah da baka goyawa Ameenu bayan barin yarinyarnan Naanah a gidaba da hakan bai faruba,
Daddy da Momy kallonta suke cike da mamaki Momy tayi k’arfin halincewa”wai Naanahr nan wacece ne haba Karimatu kina abu sai kace wata k’aramar yarinya,Abba yayi saurin cewa “gara dai kimata fad’a Hajiya k’ila idan taga kece kika mata ta d’auka,
Daddy yace”duk ba wannan maganarba yanzu mu bari Ameen yaji sauk’i sai muji komai,hakan yasa kowa yayi shuru,amma zuciyar Ameen cike take da farga ba tunani kala-kala yayi su akan cikin jikin Naanah,
“””””””
Da yamma Umma da suka koma gida ta iske Naanah kwance a k’asa tsakar gida tana barci,wani wawan duka ta buga mata”shegiya ‘yar kaza-kazancen ta danno ashar,taci gaba dacewa”saboda tsabar jin dad’i zaki kashe Ameenu har wani barcin dad’i kike ko kenan ko ajikinki ko tunda kinaso ki nakasa masa zuciya ko,A furgice Naanah ta farka sai hawaye ta duk’a gaban Umma tace”wallahi Umma bansan barci ya kwasheni ba kiyi hakuri ya jikin yah Ameen,”ai dole barci ya kwasheki tunda kina cikin farin ciki,