CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

K’asa tayi da kanta tana hawaye ita a ganinta ai tafi kowa damuwa da irin halin da yah Ameen yake ciki,Umma ta tureta ji kake gumm!ta kifa k’asa,cikin d’aure fuska Umma tace”ki tashi ki had’a yanaki naki kibar gidan nan tunda baki da gadonsa,da sauri Naanah ta d’ago kai”Umma ban gane ba?ta tambayeta,tsuww Umman taja tsaki tace”da sannu zaki gane yarinya tunda har kin fara lashewa Ameen kurwa to gara kibar gidan dangin mayu kawai,
Tuni kuka ya 6allewa Naanah,cikin kuka tace”to Umma idan nabar nan ina zani sai ki fad’amin dangina koda mayunne sai naje gurunsu tunda naka nakane kuma hannunka bai ta6a ri6ewa ka yankesa kajefar,wani wawan mari da Umma ta kifawa Naanah saida ta wuntsila ta kifa ta saki wani gigitaccen kuka,Umma ta nunata da yatsa”don ubanki ni zaki gayawa bak’ar magana,to karin maganar naki baiyi daidai ba a yau naka bai zana nakaba tunda inda naka nakane dayau kina cikin ahalinki,idan da kuwa hannunka bai ri6ewa ka yankesa ka jefar da iyayenki basu yankeki sun jefarba ubanmawa yasani ko shegiyace ke saboda kunyar duniya ba atsoron na lahira akayarda ke to wallahi yau sai kinbar gidan nan ba zamuci gaba da zama dakeba anyi cikinki a titi kema kinyi na titi Allah dai wadaran naka ya lalace,
Ai gaba d’aya kukanma nemansa Naanah tayi ta rasa,kallon Umma kawai take,rok’o take Allah yasa mafarki take ba ido biyu ba,Innalillahi wa’inna’ilaihir raju’un kawai take nanatawa a zuciyarta,biyu biyu kawai take kallon Umma da Anty Rahma dake hankad’ata waje,
Daidai tsayawar Abba ya sauka a keke napep,haka nan yaji tunda Umma suka taho yaji zuciyarsa bata amintaba yasan halin Umma sarai zata iyawa Naanah komai tunda bata k’aunarta,cike da tsoro yake kallon Naanah wacce kwata-kwata ma kamar bata cikin haiyacinta k’arasowa yayi da sauri ya tallabeta,Ganin Abban take ya kasu mata wajen biyar cikin rawar murya tace”Ab…Abb…Abba.da..daman baku kuka haifeni ba Umma tace bakune iyayena ba tace ni Tsintacciyace ni shegiyace iyayena suka yarda,
Cikin wani irin fushi dabansan Abba dashiba naga ya d’ago yana kallon Umma kuma daman kunsan ance mai hakuri bai iya fushi ba,Wani kyakkyawan mari ya zubawa Umma a gigice ta d’ago ta kallesa cikin fushi yace”daman Karimatu na fad’a miki duk ranar da kika sanarwa Naanah cewa ita ba ‘yar gidan nan bace a bakin auranki,to kije na sakeki saki d’aya,
Ai wani uban kururuwa Umma tasaka”Wallahi bazan sakuba kuma babu inda zani tsofai-tsofai dani sai inje ince an wani sakeni to ba inda zani,yace”idan gidanki ne sai ingani,
Wata k’ara da Naanah ta saka yasa ya ruga da gudu girinta kafin yakai ta zube gurin a sume……
Fateenku ce????
Ummu Affan✍????
Share and Comments
????CIKIN WAYE?????
❤❤❤❤
❤❤
❤
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
Bismillahir rahmanir rahim
????4⃣3⃣-4⃣4⃣
D’agata yayi yana kiran sunanta,amma ina ko motsi batayi,Umma ko ajikinta wai antsikari kakkausa cewa mata ke”dama zata mutu ai da an rage mugun iri,Abba baibi takanta ruwa ya d’auko me sanyi ya zuba mata,dogon numfashi taja,sai kuma ta tashi a furgice,
Cikin kuka tace”don Allah Abba kace mafarki nake da gaske bakune iyayena,rungumeta yayi yana buga bayanta”Naanah ki natsu ki cire komai aranki k’addara ta riga fata,shiyasa nake yawan ce miki Allah ya jarabce ki da jarobobi masu yawa amma idan kikayi hakuri da ta wakkali sai kiga kin sami kyakkyawan rabo,
Kuka na saki tare da k’amk’ame Abba nace”shi kenan na tabbata shegiya me yasa iyayena suka kasa rik’eni suka jefar,”saboda ke shegiyace abar a guda,Umma ta fad’a,Abba ya mik’e cike da zafin rai,yace”Karimatu zo ki fitar min a gida,
Hannun Rahma taja zasu fice,Rahmar ta kwace hannunta”A’a Umma ba inda zani kedai ki tafi,harara ta bankamata”to nima ba inda zani asibiti zan koma don wallahi bazan bar gidan nan ba,ta fita fuuu!
Girgiza kai Abba yayi cike dajin takaicin Umma wannan wacce irin annobar matace,an sakekima bazaki bar gidan ba,lallai shima Allah ya jarabcesa ta hanyar auran Umma da yayi,
Haka yayi ta lalla6a Naanah akan tayi shuru tayi hakuri amma takasa ranar haka ta kwana kuka,kai tun tanayi da hawaye harma hawayen ya gaza fitowa sai na zuci,
Safiya nayi bayan Abba da Rahma sun tafi asibiti,Naanah ta shiga gidan su Zainab anan take sanar da Hajiya da Zainab komai,Salati Hajiya ta d’auka tace”ni na dad’e ajikina inajin ke ba ‘yarta bace amms kiyi hakuri komai tayi kanta tamawa akwai Allah zakiga danginki nan kusa insha Allahu,jikin Hajiya na kwanta ina kukan zuci don idona tuni ya gama bushewa nace”Hajiya taya zanga dangina?aini kuma nasan a haka rayuwata zata k’are,Zainab tace”ki dena fad’ar hakan Naanah insha Allahu zaki gansu,
Nan suka dunga rarrashina da fad’amin da d’ad’an kalamai amma ina ni kad’ai nasan kunci da bak’in cikin da nake ciki,
Zan fito a harabar gidan mukaci karo da Marwan da sauri nayi k’asa da kaina zan wuce,tare gabana yayi yace”ina zakije munafuka,da sauri na d’ago na kallesa cike da mamakin jin kalamansa,d’aure fuska yayi tare da rungume hannayensa a k’irj yana min wani kallo wanda daga ganinsa na tsana ne yace”da kyau Naanah amma kin bani kunya kinsa naji na tsaneki kuma wallahi yadda kika bak’an tamin kema saina bak’anta miki,
Idanuwana na zubar hawaye na d’ago na kallesa”Yah Marwan idan kace haka bakamin adalci ba,kafi kowa sanin halina me yasa zakamin haka me yasa kakasa fahimta ta me yasa……da sauri ya katseta ta hanyar d’aga mata hannu✋”ya isa haka karki tarwatsani da wad’an nan kalaman naki da zasu cikamin kunne????akan me zan yarda dake bayan kin bari samari sun gama yaudararki har sun k’umsa miki wannan k’umshasshiyar????wallahi tundaga ranar da naji abinda kika aikata naji na tsaneki Naanah kuma sai na rama abinda kikamin,
Zuwa wannan lokacin Naanah ta gama tsurewa da Marwan,kallonsa take tana kuka tarasama da wacce kalma zata fahimtar dashi batasan CIKIN WAYE?ba,muryar Hajiya suka jiyo kamar daga sama tana cewa”Marwan sai yau na yarda damancen ba kaunaR Naanah kake ba duk masoyi na hak’ik’a ba ya gudun masoyinsa a ko wanne irin hali d’aya daga cikinsu ya shiga,ka bani kunya ina ma ace ba kai kad’aine d’ana namiji ba yau da naba d’ayan Naanah amma ba komai ni nasan Naanah bazata tagaiyara ba akwai masoyi na hak’ik’a da gaskiya da zai sameta kai kuwa kayi asarar mace kamila da ko wanne namiji ki muradin samu,wannan cikin na jikinta wata kaddara ce da Allah ya rubuto mata kuma ko wanne bawa bai wuce kaddararsa,
Kama hannuna tayi muka koma ciki sai kuka nake muka barsa nan tsaye kamar ginki,shima part d’insa ya wuce yana shiga bedroom d’insa ya fad’a kan bed tare da rik’e kansa,duk abinda yake fad’a k’arfin hali kawai yake amma soyayya Naanah ba inda taje tanan zaune daram a zuciyarsa amma idan ya tuno ciki gareta sai zuciyarsa tayi k’una yajisa cikin bakin ciki,shifa bai yarda batasan CIKIN WAYE?ba,gashi shi kansa yarasa gane CIKIN WAYE?zaice tunda shidai tunda yake da Naanah bai ta6a ganinta da wani saurayi ba bayanshi,
Alh Mukhtar Salisu Sada da matarsa Hajiya Rabi’atu sai yaransu Fareeda Sayyeed da Fahat ne ke shiri don zuwa asibiti gaishe da Ameen,Fareeda tace”Didi don Allah kuyi ku fito nifa tuni nashirya,Mamee tace”kiyi gaba idan kin gaji bazakizo ba fa kitakura mana ki bimu a sannu,Didi yace”haba Mameen yara garadai kiyi sauri kinga don ita zamu surukinmu ba lafiya,Mamee tace”a’a wallahi ni badan ita zani ba,Sayyeed yace”bare ni kawai don zamu gaishe da Yah Ameen Didi saikace saboda ita,to ita a suwa,tuni Fareeda ta fara cika daman taji haushin maganar Mamme sai kuma ga abinda Sayyeed yace ta zun6uro baki gaba nan ta fara hawaye,Didi ya jawota cikinsa yace”rabu dasu Fareeda dani suke zancen duk bak’in cikinsu saikin auri Ameen,ta rungume Didiy kamar ba itace mai kuka ba tahau dariya”yauwa Didiyna shiyasa nake sonka,Fahat ya ta6e baki “son maso wani dai k’oshin wahala ‘yan mata,Mamee tace”maganarka hakkun Babana,