NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Lokaci-lokaci tana duba wayarta ko Marwan ya kira,haka kuma tana yawan kallon K’ofa ko yah Ameen zai shugo,shikansa Abba yaga duk jikinta yau a sanyaye ta tashi yace”Naanah lafiya daiko idan kinajin wani yanayi kisanar fa,murmushin yak’e tayi wanda yafi kuka ciwo tace”Abba ba komai kawai yau na tashi naji ni haka gani nake kamar wani abu zai sameni yau,

Shafa kanta yayi yace”Naanah kiyi ta addu’a insha Allahu alkhairi ne kinji Naanahta,murmushi ta sake “to Abba,sannan ta kallesa”Abba ina so inje gidansu Zainab yanzu,yace”shi kenan saikin dawo,

Hijab na zura dogo har k’asa,daman tunda cikina ya fito dogayen hijabai nake sawa,gidansu Zainab na wuce,ina shiga ta rungumeni har muka kusan fad’uwa,Hajiya tace”waiku yaushe zaku girma Zainab baki ganin cike ne jikints idan kika kadata fa,kan kujera muka zube Zainab nace”ni wallahi mancewa nike da wani ciki,nace”murnar me kike haka,tace”yanzun nake niyar kiranki a waya sai gaki daman zan sanar miki na sami Addmision ne a Poly,hawaye suka zubomin ba wai na bak’in cikiba natayata murna nace”na miki murna Zainab ni kuwa da yin wata makaranta ai saidai ko alahira idan anayi,Zainab ma sai hawaye tace”wallahi naso ace tare zamu fara karatun nan amma ba komai karkicire rai da zarar kin haihu sai ki fara,nace”uhmm kedai bari kawai wanne karatu zanyi ni kuma bayan wannan abun kunyar ni wallahi ko k’ofar gida bansan fitowa tunda Umma ta gama yad’ani a unguwar nan,

Gaba d’ayansu sai kuka suka rungume juna,ita kanta Hajiya sai taji hawaye na gangaro mata,

***************

Ameen ne ke tashiri cikin wata bugaggiyar shadda marun ya feshe jikinsa da turarukansa masu dad’in k’amshi ya taje sumar kansa wacce sai shinning take saboda gyara da take samu,

Wow zo kugansa gaskiya yah Ameen ya had’u ajin farko ne kyakkyawa ne na k’arshe ga kyau ga cikar kamala haiba da annuri ga uwa uba kwarjininsa,

Farlour ya fito ya iske su Momy a dinning table suna breakfast,shima zaunawa yayi Momy ta zuba masa arish falantai sai wainar kwai da bread ta had’a masa tea,sauri-sauri ya ke karyawa,

Daddy yayi murmushi yace”Ameen duk saurin ne haka lallai ka k’osa kaje gida,murmushi yayi yana sosa k’eya,zaiyi magana saiga Didiy Mamee da Fareeda sunyi sallama gabad’aya suka juyo,Daddy ya tashi ya tashi ya taro d’an uwansa suka rungume juna”Mukhtar kaine kuke tafe,Didiy yace”ai kuwa,Momy tace”ku k’araso ku karya,ta fad’a cikin fara’a,Mamee ta k’arasa”kamar kinsan bamu karya ba wannan fitinanniyar ta sakomu gaba,ta fad’a tana nuna Fareeda wacce gaba d’aya hankalinta ke kan Ameen ya gama tafiya da imaninta,

Bayan sun gama karyawa Ameen ya mik’e yace”Daddy ni zan wuce,Kafin Daddy yayi magana Didiy yace”ina zaka,Daddy yace”gida zashi,Didiy yace”yauwa abin yazo gidan sauk’i muma daman gidan nasu mukeson zuwa,

K’walalo ido Ameen yayi????aransa yana tambayar me zasuyi,don kar ace yayi rashin kunya ya kasa tambaya,Daddy yaji nacewa”ina fatan dai lafiya ko?,Didiy yace”Fareeda ta ishemu da ita Ameen take so jiyafa suma ta dungayi kuma duk akan Ameen shine yau da safen nan tasamu gaba wai saimunzo wajen Ameen,du kansu kowa yayi shuru Ameen ya zauna ja6al har ga Allah badan yana son Naanah ba da ya auri Fareeda kodan darajar iyayentas musamman ma Daddy saidai baijin zai iya,Daddy ya kalli Ameen yace”to kai ya kagani ni ina taya d’an uwana neman alfarman ka auri Fareeda,a gigice Ameen ya d’ago dukansu shi suke kallon ya saukar da kansa k’asa yace”Daddy bazan 6oye makaba wallahi akwai wacce nake so yanzun ma gurinta nakeson zuwa,yace”amma kace mana gida zaka,yace”eh gidanmu take k’anwata ce,shuru sukayi nawani lokaci kafin Didiy yace”kai namiji ne mijin mace hud’u inhar ka amince sai ka had’asu biyu,numfashi yaja dukansu yanajin kunyarsu,Daddy yace”idan Abbanka kakeji ku tashi dukanmu muje munemi alfarma,yace”a’a ba komai Daddy bama saikunje ba na amince,Didiy yace”mun gode karkaji komai daman munyi niyya zamuje musami Abbanka,numfashi yaja yace”tom shikenan,

Gaba d’aya suka d’unguma zuwa gidan Abba,Ameen ne kejan motar cike yake da tunani iri-iri ya yain da Fareeda ke kusa dashi cikin murna da farin ciki,

Suna isa yayi parking suka shiga gidan da sallama,Umma tana ganinsu ta hau washe baki”sannunku da zuwa sannunku maraba marhabin,suma cikin fara’a suke amsa mata,anan farlour suka zube ana gaishe-gaishe,Abba yace”sannunku,Rahma da Sakina da tazo itama tsohon ciki gareta suka gaishesu,nan aka kawo musu lemuka da ruwa,

Ameen ganin baiga Naanah ba wayarsa ya ciro yatura mata sak’o kamar haka

 Naanah kina ina gani na k'araso baki gida,

Yana gamawa ya tura,lokacin suna zaune ne da Zainab Hajiya ta shiga ciki,sak’on ya shugo tana dubawa ta mik’e yayin da taji k’irjinta ya buga da k’arfi,innalillahi kawai take nanatawa,tace”Zainab zo muje yah Ameen yazo,mik’ewa tayi itama tasaka hijabinta mukayi waje,karo mukaci da yah Marwan yace”yauwa Naanah daman yanzun zan kiraki,tace”ohkey ina zuwa yanzun,yace”tom,ciki ya shige mu kuma muka fice,gabana bai dena bugawa ba haka muka shiga cikin gidan,

Mutanen dana gani a farlour nike bi da kallo suma ni suke kallo kafin wani mutumi daga cikinsu ya mik’e yana nuna Naanah da hannu????????…….

My WhatsAPP no 08104335144

Muje zuwa Fateenku ce????????

Ummu Affan✍????✍????✍????
????CIKIN WAYE?????

❤❤❤❤
❤❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

????5⃣1⃣-5⃣2⃣

Yana nuna Naanah da hannu,”ke…!ka…Haj…!ya…!,muryarsa rawa take da kyar ya iya cewa”Hajiya duba kiga ikon Allah wannan ba Firdausi bace,gaba d’aya mutanan farlour kallo ya koma gun Naanh,

K’arasowa tayi ta zauna kusa da Abba tana cewa”Abba munyi bak’i ne,gyad’a kai yayi alamar eh don ya shiga rud’u,Mamee tace”babu tantama wannan Firdausi ce,da sauri Didiy ya koma kusa da ita ya rungume hawaye na zubar masa,itama sai takama kukan,kafin tace”wai Abba meke faruwa ne?,

Da sauri Zainab tayi gida ta kira Hajiya da yah Marwan,Daidai shugowarsu Didiy yace”‘Yata Firdausi ta 6ace shekaru goma sha shidda da suka wuce kuma ina kallon wannan ‘yar na tabbatar ‘yata ce,ya d’aga hannunsa sama????”Allah na gode maka da kadawomin da farin cikina,Mamee da Fareeda tuni suka fara kukan farin ciki suka rungume Naanah,

Abba yace”Allahu Akbar Allah me girma da d’auka ikon Allah yana da dama yanzu daman Alhaji Mukhtar Naanah ‘yarka ce,Alh Salis tuni ya fara godewa Allahu yana cewa”Ikon Allah kenan daman Firdausi tana kusa damu Allahu akbar,Momy kuwa itama tuni ta koma gurin Naanah duka suka ruk’umk’umeta,

Abba yace”amma Alh Mukhtar ya’akayi Firdausi ta 6ace daga gidanka,hawaye suka zubo masa wanda daga gani na tsantsar farin ciki ne yace”bak’ar rana agareni wacce bazata ta6a 6acemin ba wato ranar da Firdausi ta 6ace”Munje Igabi bikin yaron babban yayan mu domin asalinmu ‘yan Igabi ne bayan angama biki da komai don satinmu guda acen nida iyalina,muna hanyarmu ta dawowa Fahat yayan Firdaisi ya ishemu fitsari yakeji,banza muka masa bayan maganata da farko da na masa cewa yayi hakuri saimun kai gida amma yaron nan ya dunga kuka bamu kulasaba, ganin da gaske yake kuka yake sosai yana cewa”Didiy don Allah mu tsaya nayi wallahi ya matseni,ganin yaro na niyyar suk’ewa dole nasa direba ya tsaya,Fahat ya sauka yayi fitsari lokacinmma har mun shugo cikin Kaduna,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button