CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Haka suka koma tare da Sakina,ta kasa koda had’a ido da Abba,sai zubewa da tayi gabansa tana basa hakuri”kayafe ni Malam nasan nayi kuskure amma in Allah ya yarda daga yau zan fara gyara kuskurena,yace”nagode Allah da kika gane kuskuranki amma ke don Allah yanzu ba’abin kunyarki bane da kikaji ko CIKIN WAYE?CIKI nad’anki ne to yanzu wanne irin hukunci kika tanada dazaki tunda kin dad’e kina son jin CIKIN WAYE?Umma ta fashe da kuka tace”nayi nadama nayi da na sani wacce akecewa k’eyace,
Nan dai yafita yabarta tana kuka,Rahma dake taunar chingam ci kake k’as!k’ass!!tace”ke Umma kece da d’aurawa kai shiga uku kika sani ko yah Ameen d’in k’arya yake don ya kareta kinsan fa yarda yake sonta meye bazai mata ba,
“Dolla cen rufemin baki shashasha,Umma ta fad’a cikin tsawa,Rahma ta gallawa Ummar harara tace”a’a ni karki cikamin kunne da tsawarki wallahi banso kika dawo gidan nan ba ke Sakina dad’i uwa kinje kin kwasota,Umma tasaka kuka tace”nashiga uku Rahma nikoke gayawa irin wannan maganar,tsaki Rahmar taja tabar gidan jikinta shigar da ba mutumci,
Sakina tace”Allah na gode maka da ka shiryani tunda wuri kuma ka aurar dani,Umma ga irinta nan bazanga laifin Rahma ba don irin tarbiyyar dakika bamu kiken,ni kinga tafiyata zan koma d’akin mijina idan kin lalla6a Abba kun zauna lafiya ke kika sani idan kuma zakici gaba da abinda kike tom ga fili nan ga mai doki,tana gama fad’a tayi waje abinta,
Umma tasa kuka tana fad’in kaichona yau ga abinda na shuka ‘ya’yana na cikina ke gayamin irin wannan maganganun,ya Allah ka shiryu masu irin halina kabamu damar yiwa mazajenmu biyayyar aure kabamu ikon tarbiyyar yaranmu,
Haka ta dunga lalla6a Abba har ta samu ya d’an sakko sosai yanzu take girmamasa da masa biyayya Rahma kuwa sai abinda yaci gaba yanzu ta d’aura k’awance da duniya,
Sakina ta riga Naanah haihuwa ta sami yarta mace Sakinatu,akasha suna,batayi arba’inba Naanah ta haifi Muhseen,tun Naanah na asibiti Umma taso zuwa Abba ya hanata,haka da takoma gida taso zuwa Abba yace ta bari,gashi tanason ganin jikan nata amma da Abba ya hanata saita hakura,shi kuwa yana sake gwada tane yaga da gasken ta gyara ko kuwa,
Ranar sunan da al’ajabi ya dawo gida yake sanar da UMMA abinda ya faru”hawaye suka zubo mata tace”lallai iyayen Naanah sun nuna mana halacci naji dad’in wannan had’in Allah ya basu zaman lafiya,Abba ya amsa da amin domin tabbas yaji dad’i amma duk da haka sai ya nunawa Ameen kuskuransa,
To kunji abinda ya faru da Umma kenan,cigaba,
Babban farlourn bak’i na Alh Salisu Sada cike yake da ahlin wannan gida kowa yazo haka 6angaransu Ameen su Abba da Umma sunzo harda Sakina,haka wajensu Marwan mahaifinsa Alh Ibrahim da Hajiya sai Zainab,tarone da Alh Auwalu yace yana neman kowa don sanar dasu wata muhimmiyar magana,
GYaran muryayi bayan an bud’e taro da addu’a sannan ya fara dacewa”…….
Saimun had’u a page na gaba karku manta
Fateenku ce????????
Ummu Affan????????
????CIKIN WAYE?????
❤❤❤❤
❤❤
❤
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
Kwana biyu ba kujini ba amin afuwa,na gode da nuna kulawa,
Didicated to my Fans
Bismillahir rahmanir rahim
????6️⃣7️⃣-6️⃣8️⃣
Ya fara dacewa”Alhamdulillahi mun gode da irin ni’imomin da Allah ya mana,yaci gabadacewa,”Mun yanke hukunci ba tare damun shawarce kuma domin munsan komai muka fad’a muku baza ku bamu kunya ba,musammanke Naanah Firdausi da fatan zaki kar6i za6in da muka miki kuma ki rik’e hannu biyu bamuyi hakan da nufin cutarki ba sai gani da mukayi hakan shine mafi daidai agareki,
Tuni gabanta ya buga da k’arfi tun kafin asanar mata meke faruwa ta fara hawaye,tayi k’asa da kai k’irjinta na bugawa da k’arfi,
Alh Salisu yace”ba kuka zakiyi ba Naanah ni nasan zakiyi alfahari da za6inmu anan gaba,ya kalli Ameen yace”kai kuma karkaga mun baka ita kaga kanar wani abu muke nufi cancanta da mukaga kunyi yasa muka yanke wannan hukuncin,yace”Daddy karkayi haufi akaina ni mai kaunar Naanah ne wani naga zaiwa Naanah wani abu sai inda k’arfina ya k’are bare ni da kaina,
Naanah ta d’ago kai ta cilla masa harara domin tuni ta gane inda maganarsu ta dosa so suke su had’a auranta da Ameen to bazata yarda ba,jin abinda Alh Sani kecewa yasa ta d’ago kai cike da tashin hankali,
A wajen rad’in suna aka daura auran Ameen da Naanah,Marwan da Salma,sai Sayyeed da Zainab,ai kusan lokaci guda duk kansu suka d’ago kai,Ameen da Marwan suka zubawa Naanah ido,yayin da Sayyeed da Zainab suke kallon juna cike da mamaki,
Hawaye kwance akan idanuwan Naanah,a hankali tayi k’asa da kanta hawaye na tsiyaya,nan dai akayi musu fad’a sosai sannan taro yatashi,
Da gudu Naanah tashiga bedroom d’in Ameen sakamakon Hankalinta da yatashi ta d’auka nata tashiga saman gadonsa ta fad’a tana kuka,cike da mamaki shugowarta ya shiga,kallonta yayi yanajin tausayin Naanah saboda abinda ya aikata mata amma yanaso ta basa dama domin kankare abinda ya mata,
Zaunawa yayi bakin bed ya d’agota tasha Fareeda ce saita k’amk’amesa tana kuka,fad’i take “ni bana sonsa bazan iya zama tare da shiba,da k’arfi ya runtse idonsa don yaji zafin kalmar bata sonsa,
Naanah jin shurun yayi yawa sai bubbuga mata baya da ake alamar rarrashi yasa tasha jinin jikinta,jin sanyayyen k’amshin turaren yah Ameen da kulum take ji atare dashi yasa ta d’ago kanta dake kan faffad’an k’irjinsa,
Ai da sauri ta fara k’iriniyar kwace jikinta amma ya rik’eta katamau,Wata harara ya banka mata yace cikin muryarsa mai dad’i da sanyi”lokacin da kika rik’eni wa yasaki?sannan me ma yakawoki d’akina alamu ya nuna kinason ki tare gidan mijinki ko?,
Da sauri na sake kallonsa idanuwansu suka sark’e da juna,dukansu kowa najin bugun numfashin kowa,masifar da zata masa sai tanemata ta rasa nan kuma muryarta ta fara rawa”ni…ni…ni dai yah Ameen ka cikani na wuce”ank’i,ya fad’a yana kashe mata ido d’aya????,
Da sauri tasake k’asa dakai”me yah Ameen d’in nan yake nufi?,ta fad’a aranta ashe maganar ta fito fili yace”komai ma nake nufi,hannunsa yasa saitin la66anta yana zagayawa dasu,cikin sanyi murya yace”Naanah ina sonki da yawa,
Da sauri ta ture hannunsa ta turo baki gaba cikin shagwa6ar da batasan tayi ba tace”nidai banso ka sakeni na wuce,
Shima yayi kamar yadda tayin”ni kuma inaso,
Kallonsa tayi sai kuma ya bata dariya”kai yah Ameen sai kace wani yaro,murmushi yayi cikin jin dad’in dariyar da yaga tayi yace”ai ni nafi yaro yarinta ko Muhseen albarka,gaba d’aya sukasa dariya,
Rik’e hannunta yayi”to muje na rakaki ciki ko?,tace”a’a nagode bari naje,girgiza kai yayi ya zuba mata manyan idanuwansa yace”a’a sai na rakaki,
Zatayi magana saijinta tati sama yah Ameen ya sun gumeta,zaro ido tayi????”kai yah Ameen,nan ta fara tsalle tsalle ajikinsa tana bugun k’irjinsa”nidai ka saukeni banso,bai kulata ba yayi waje da ita,
Suna fitowa Momy na sakkowa kan bene,ido ta zaro cike da mamaki,yayinda Naanah taji wata muguwar kunya ji take kamar k’asa ta tsake ta shige ciki,sai ta tusa kanta cikin k’irjinsa tana goga fuskarta,ai tuni Ameen yaji wani irin yarr!,amma ganin Momy ya share tare da direta akan kujera,yana sosa k’eya,ai ganin haka momy ta wuce batabi ta kansu ba yana ganin ta wuce da sauri ya zauna kusa da Naanah tare da rik’o hannayenta……..