NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Zaman da Naanah keyi a gidan Abbanta tanajin dad’inta Umma sai nan nan take da ita,ita da tayi niyyar kwana biyu sai gata har tafi sati daman suna hutu ne,koda suka koma,d’auko abubuwan karatunta tayi taci gaba da zuwa anan,

Momy harda mata tsiya tace”kin gujemu ko?,tace”a’a zan dawo ne momy,

Suna kitchin da Umma suna had’a abincin dare,saiga Rahma ta shugo a bige take tana tafe tana layi,tare da surutai burkitai,

Da sauri suka fito jin k’arar abu ya fad’i,ganin Rahna ce ke karo da kaya yasa Umma sakin kuka,

Tace”Naanah kin gani ko rashin tarbiyyar danawa yarana duk k’ok’arin da Abbanku keyi amma nid’in bana ta tasa a lokacin sai nake gani kamar baison yarana nane yau nayi da nasanin abinda na aikata,

Nace”Umma tabbas kece silar lalacewar Anty Rahma amma Allah gafurur rahimu ne tunda kinyi nadama saikiyi ta istigifari,sannan Rahma addu’arki take nema Allah dai yashirya ta,ta amsa da amin sannan muka koma kitchin mukaci gaba da aikinmu,Rahma kuwa anan ta zube barci mai nauyi ya kwasheta,

Zainab ta shugo da yamma muka fara hira tace”uhmm Naanah naga sai wani kyau na musamman kike k’arawa wa zai kalleki yace kekika haifi Muhseen,

Hararar wasa na buga mata nace”to uwar iya ya son ranki,tace”a’a haka nakeso amma meye sirrin ne,nace”na me?,

Dariya tayi “na kyawun mana ko duk yah Ameen d’inne,ai wani duka na kai mata ta goce”amma Zainab baki da kyirki wallahi,

Tace”to meye a ciki mijinki ne fa,harara ta na mata tace”uhm ni bari in kira my man wallahi yau abin dad’i nake so yasaya min,

IDo Naanah ta zaro????kafin tayi magana har Sayyeed ya amsa kiran Zainab kashe murya taga Zainab tayi tace”Babyna kana inane,yace”ina wajen liyafar da muke kinsan mun kammala karatunmu,Tace”Alhamdulillah Babyna na tayaka murna amma inason ganinka,yace”karki damu Honey yanzun kuwa zanzo,sake kashe murya tayi”Babyna kazomin da abu me dad’i,

“Me kike so honey?”ai kasan duk abinda nake so,yace haka ne my honey sai nazo,suka yanke kiran,

Da yake speaker Zainab tasa hakan yasa duk Naanah taji hirarsu,

Tace”ehye Zainab yaushe kika kile haka,tace”tun ranar da na rabbatar na zama matar yah Sayyeed,

“Kai amma baki da kyirki haka kika lalata min d’an uwa,

Zainab ta kwashe da dariya”na lalatasa ko ya lalata ni,kedai wallahi Naanah ina sanar da ke kar ki tsaya kallon ruwa kwad’o ya hau miki k’afa idan zaki farka gara ki farka mijinki yah Ameen special ne samun kamarsa wallahi sa kamar wuya ni dai ina sanar miki ki mance komai ki rungumi mijinki

Kallon ta nayi nace…….
????CIKIN WAYE?????

   ❤❤❤❤
         ❤❤
            ❤

STORY AND WRITING BY FATEEMAH SUNUSI RABEE’U
(UMMU AFFAN).


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

????️8️⃣1️⃣-9️⃣0️⃣

Nace”Amma baki da kyirki Zainab har kina cewa na mance da abinda yah Ameen yamin taya kike so na mance,nan hawaye ya fara zubar min,

Kusa dani ta matso tace”kiyi hakuri Naanah tabbas yah Ameen ba kyauta miki ba,amma kinsan k’addara tunda tun farko Allah ya rubuta miki hakan to dole ta same ki kiyi hakuri ki mance da komai ki ringumi mijinki da d’anki,

Dogon numfashi naja uhmmmm nace”shikenan zanyi tunani akan maganarki,tace”yauwa ‘yar uwats,

Watar Zainab ce tayi k’ara tana dubawa ta mik’e”Sis bari inje Babyna ya iso,

Da sauri ta wuce,Naanah murmushi tayi aranta tace Zainab kenan,

Yau bata da Darasi hakan yasa tashirya tawa su Umma sallama cewa zataje gidan Didiy,

Tashirya kayanta har wajen mota Abba da Umma suka rakata,

Sannan ta wuce,tana isa da Fareeda taci karo da sauri ta amshi Muhseen tace”my son oyoyo,

Suka zube kan kujera,Naanah ta gaisheta ta amsa sannan tace”daga ina haka naganki harda akwati,

“Daga gidan Abba nake wallahi ina su Mameen ne,kan Fareeda tayi magana saiga Mameen na sakkowa daga bene,tace”ehye yau bak’i mukayi,

Murmushi Naanah tayi tace”ai kuwa Mamee,Fareeda tace”k’irik’iri kin guji gidan nan ko,nace”haba dai ya zan guji gudan nan,

Mamee tace”to ko tana nan kwana nawa ne tunda da auranta ko zatayi ta zama ne,

Tashi nayi jin wannan maganar don banso ayita na nufi d’akina dake gidan saman bed na fad’a ina sauke ajiyar zuciya,

Alhamdulillahi lokaci na ta tafiya,yayin da karatun mu keta zurfi sosai,

Shekarun Muhseen uku kenan yaro tubarkalla,kamarsa sak da Abbansa,kowa kaunarsa yake,yau yana wannan gida gobe yana wancen,

Daddy ne yace bazai yuwu ace muna da aure amma muna zaune gida ba,

Kasancewar Saura sati guda bikin Anty Fareeda Daddy yace duka tare za ayi hidimar biki harda tarewarmu,nayi kuka kamar raina zai fita don bana son tarewar nan,

Didiy da Mamee suka zaunar dani suksmin nasiha mai shiga jiki,

Didiy yace”haba Naanah Firdausi kiyi hakuri ki mayar da lamarinki ga Allah sai kiga komai yazo cikin sauk’i meyasa bazaki ya fewa Ameenu ba karki mance irin soyayyar da yaron nan yanuna miki,tabbas bai kyauta ba muma mun sani amma yazamuyi da hukun cin Allah ki zama mai tawakkali Naanah da mayar da Al Amuranki ga Allah,

Mamee tace”inda ke me tunani ce,baki ganin abunda yayi ta faruwa Allah yayi fa sai Ameen ya miki ciki idan ba hukuncin Allah ba babu yadda za’ayi ki 6ace harshi ya takurawa mahaifinsa sai sun d’auke ki kuma kiyi tunani bada son ransa ya aikata hakan gareki ba kuma sannan kiyi duba da yadda mahaifiyarsa taso zubda cikin tayi iya yinta akan sai cikin ya zube amma da yake ba’awa Allah wayau saida CIKIN yazo duniya,(K’alubale gareku iyayen da yaransu sukayi ciki suce dole sai an zubda ko yaran dake k’ok’ari wajen zubar da ciki kusani duk wanda Allah yasa yana da rabon zuwa duniya dole ne yaxo)don ba’awa Allah wayau ko dabara,

Mamee taci gaba dacewa”kiyi hakuri insha Allahu nan gaba nasan zakiyi farin ciki da had’in nan saikin yi Alfahari da samun Al-ameen a matsayin miji,

Jikin Naanah nayi sanyi sosai tabbas maganar iyayenta gaskiya ce,don haka tasawa ranta salama,amma tasan zuciyarta nA mata zafi,

Haka akayi ta shirin auran Fareeda tare da tarewar su Naanah,Fareeda wani attaji zata aura Alh Babale,matarsa daya yara uku,ba laifi yana kaunar Fareeda sosai itama tana sonsa kuma matarsa bata da matsala don tuni sukasan juna,

Momy ta mayar da Naanah wajenta inda take mata wani gyara da musamman da yake ‘yar maiduguri ce Momyn tasan sirrin magungunan Mata dana K’amshi,

Wani irin kyau Naanah ta k’ara don sosai Momy ke gyaran d’iyar tata,

Marwan tuni suka daidaita da Salmarsa don yalura kusan irin halinsu d’aya da Naanah dukansu shirye shiryen tarewa kawai ake,

TUni Ameen ya idasa tambatsetsan gidansa da yake gidana,sosai gidan ya had’u sai yabawa ake,

Lokacin da aka zubawa Naanah jeran kayanta kuzo kuga kyau,uhmm wani abun sai manya fad’ama 6ata baki,Aini da nashiga K’auyanci na fara,uhmmm aljannar duniya kenan gaskiya fa ya had’u,

Shima Marwan ba laifi gidansa yayi kyau sosai hakama Sayyeed kasancewar yanzun zai fara aiki yasa Didiy ne ya mallaka masa gida babba mai kyau da tsari,

Dukansu an musu jere har Fareeda ita ma tare suke da uwar gidanta saidai kowa part dinsa da ban,

Akwatina goma sha biyu Ameen ya had’awa Naanah da kayan alfarma aciki na nunawa sa’a,shima MARWAN haka Sayyeed ma,abindai gaba d’aya sai son barka,

Tun saura kwana biyu biki ake shagulgula tuni bak’i na nesa dana kusa suka fara zuwa,ana abubuwa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button