CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Ummu Affan
????CIKIN WAYE?????
❤❤❤❤
❤❤
❤
Story
and
Written
By
Fateemah Sunusi Rabee’u
Ummu Affan
????1⃣1⃣-1⃣2⃣
????Koma dai menene addu’a ta kullum ita ce Allah ya shiryata,
A kwana atashi ba wuya a gurin Allah,mun kammala jarabawarmu lfy har Allah ya kawomu gobe sallah ranar wuni nayi aiki kamar me na gaji sosai,
Washe gari sallah da wuri na tashi nashirya cikin wata atamfa riga da siket sosai ta amsheni kamar dama ajikina aka tsarata nayi make-up d’ina simple sosai nayi kyau Yayah Ameen ne ya aiko mana da kayan sallah kala biyar biyar masu kyau da tsada,k’awata Zainab na biya mawa muka wuce salar idi,sai yabani take wai nayi kyau,bayan an idar muka dawo,
Abba da Yah Ameen suka shugo sun dawo sallar idi ne,Yah Ameen yana cikin wata d’anyar shadda da akayiwa d’inkin da samari ke yayi,gaskiya yayi kyau ainun,
Tunda ya shugo idanunsa na kan k’anwar tasa da yake matukar kauna a zuciyarsa,kusa da ita ya samu ya zauna,sannan ya rad’a mata a kunne,”gaskiya kinyi kyau kanwata sosai,murmushi tayi har sai da dimple d’inta suka lotsa,ita ma ahankali yadda shi daya kawai zaiji tace”ai Yayah ka fini kyau ka ga yadda ka had’u kuwa,ido ya d’an kura mata na wani lokaci sannan yace”ke kanki kinsan ba zaki had’a ni dake ba ke me k’ira irin ta indiawa,dariya tayi sosai har Abba nacewa “yau kuma me yasami Naanahr Abba ta ke irin wannan dariyar,tace”Abba kamanta yau take sallah dole inyi farin ciki,yace”haka ne,sannan ya maida hankalinsa gurin abinda ya ke yi,
Ta k’ara cewa a hankali”Yah Ameen ai gwamma kai kasan da Abba kake kama su Aunty Rahma kuma da Umma ni kuwa da wa nake kama,ta fad’i hakan cikin damuwa,ya d’anyi shuru na wani lokaci sannan yace”ai kema da Abba kike kama ko baki ta6a jin wanda yace muna kama ba,
Tasan wasa yake mata sai kawai tayi murmushi ba tare da tace komai ba,Ashe duk abun da suke Umma na kallonsu abinda suke cewa ne kawai ba taji,tace”waiku k’wusk’wus d’in me kuke,Yah Ameen yace”Umma ba komai,sai kuma batace komai ba,
Bayan sun fita ne Umma ta kamamin kunne taja sosai,zafin da naji yasa na saki ‘yar k’ara tace”wallahi kinji ni inhar baki fita idona na rufe ba sai na sa6a miki sau nawa ina gargad’inki da ki dena shigewa yaron nan meyasa bakiji halinki ya ke irin na mayu ne iye to ina sanar dake wannan yaron yafi k’arfinki kurwarmu kurrr da ke me bak’in hali,
Nace”don Allah Umma kiyi hakuri bazan k’ara ba,ta k’ara jan kunnen tare da sakinsa kuka na saka saboda zafin da naji yana min,ta buga min tsawa,”tashi ki fita cen waje kiyi kukanki ba zakiyi mana shi anan ba,tashi nayi na d’auko mayafina nayi waje kai tsaye gidansu Zainab na nufa,
Ina shiga harabar gidan naga motoci da yawa,duk da cewa in nazo gidan ina ganin motoci a ajiye amma na yau sunfi yawa,sai nayi tunanin ko don sallah ne kila ‘yan uwana sukazo gaishe su,Ina shiga farlour cike yake da ‘yan uwa,gaishe su nayi suka amsa cikin fara’a da sakin fuska,Zainab ta taso ta kama hannuna tana cewa”Naanah zo ki gaishe da Yayana Marwan ya dawo daga karatunsa,da yake tana bani labarin yayanta Marwan dake karatun likita a kasar Egypt,sai faman jana take har gabansa sannan ta ajeni kusa dashi ita ma ta zauna,tace”Yah Marwan ga Naanah wacce nake baka labarinta a waya aminiyata,d’ago kansa yayi daidai da d’ago nawa kan muka kalli juna lokaci guda,take naji gabana ya buga kamar yadda naga alamar shima abinda naji yaji,gaishesa nayi ya amsa a hankali,ganin yayimin banza na juya gurin Hajiya nace”Hajiya ina wuni anyi sallah lafiya,ta amsa min tana me fara’a,da ya ke haka yaranta ke kiranta da Hajiya nima hakan nake kiranta,
Na zauna kusa da Zainab anata hira kamar nima daman ‘yar gidan ce,na lura da kallon da Yah Marwan ke min hakan yasa na kasa sakewa,na d’ago ido kenan sai kawai muka had’a ido dashi na kallesa sosai,bak’i ne shi duk da a zaune yake zaka iya ga ne yana da tsayi ba laifi kyakkyawa ne,fatar jikinsa daga gani kasan akwai hutu,sanye yake cikin k’ananun kaya jeanse da t-shirt,
Ganin ba zan iya jure kallonsa ba yasa nayi kasa da kaina ina wasa da ya tsun hannayena,…
Fateenku
Ummu Affan
????CIKIN WAYE?????
❤❤❤❤
❤❤
❤
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
Ummu Affan
????1⃣3⃣-1⃣4⃣
Bismillahir rahmanir rahim
????Ganin nayi shuru sai Zainab tace”Naanah na lura yau baki son magana ko anyi miki wani abu ne,Hajiya tace daman cen Naanah ba maison Surutu bace irinki,Zainab tace”uhmm Hajiya ke dai bari don batare kuke da ita ba ne a haka ne kike mata kallon shuru shuru amma idan kika zauna da ita surutu sai ya isheki hakan ta ke kamar Aku,
Na kalleta na d’an harareta sannan nace”Zainab ban son sharri fah,
Hajiya tace”rabu da ita kawai nasan sharri ta ke miki,haka mu kai ta hirar mu har na mance abinda Umma ta min,
Wayata naji tayi Ringing ina dubawa lambar Yah Ameen ce 6aro-6aro,hakanne ya tuna min da gargad’in da Umma ta min,na d’au kiran tare da sallama,
KO amsa sallamar beyi ba yace”kina ina ne!,nace “Ina gidan su Zainab,yace”maza kizo ina son ganinki,”toh,na amsa masa,na mik’e Zainab tace”sai ina kuma,nace”Yah Ameen ne ke kirana,
“Tace”shi kenan kinsan halin Umma da nazo munje mun amshi barka da sallah gurin Yah Ameen,nace”kedai idan zaki taso muje!,ta mik’e muka fita zamu shiga gidanmu kenan ta juyo ta kalleni tace”inhar Umma ta ko ro ni ke kika jamin,nace”haba dai Zainab ba ma zata koroki ba,da ya ke da Zainab tana yawan zuwa guri na Umma tayi ta mata habaici daga baya ta dunga korarta data shugo,shine Hajiya tace”ta dena zuwa,
Yana ta safah da marwah a farlour shi kansa bai san me yasa yadamu da Naanah da yawa haka ba,ya da mu da lamarinta yana matuk’ar jinta a jini da tsokar jikinsa,
Da sallama suka shugo ganinsu da yayi tare da Zainab sai yaji hankalinsa ya kwanta tare da sakin sanyaryar ajiyar zuciya,
Zainab ta gaishesa ya amsa fuska sake,tace”Yah Ameen munzo amsar barka da sallah,murmushinsa mai kyau yayi,yace”Zainab kinyi sauri a binda zan baku yanzun na fasa,Naanah cikin shagwa6a tace”kai Yayah yanzun sai ka fasa ba mu,
Yace”k’warai kuwa tunda kun tambaye ni,Zainab tace”Yayah a mana afuwa,yace”shi kenan nayi amma sai gobe zan baku don akwai inda zaku rakani goben saiki tambayi Hajiya,tace”shi kenan ba damuwa Allah ya kaimu,ya amsa da “Ameen,
***************
Ai kuwa washe garin munsha yawo,Yah Ameen ya kaimu gidajen abokansa da ‘yan uwan Umma na nan cikin gari,gaskiya mun samo kyautuka da yawa,gab da magrib muka dawo ya so ya kaimu gidan Daddynsa saidai ganin magrib tayi yace muyi hakuri sai wataran,
Gidan su Zainab muka wuce Hajiya muka bawa kudin da muka samo ajiya,da kayan,sannan na wuce gida,
Ina shiga Umma ta hauni da fad’a,tace”daga ina kike,Anty Sakina tace”ina zata idan ba yawon iskancinta ba,Umma tace”shegiya tana abu kamar me gaskiya nan kuwa iskanci ne cike da ciki figigi da ke kamar a hureki ki fad’i mutum kullum yana cin abinci amma yana yadda ya ke,
Anty Rahma ta kwashe da dariyar mugunta tace”ai wannan yarinyar inaga kome zata ci bazata ta6a k’iba ba,ni kuwa na kada baki nace”wallahi Anty Rahma da nayi irin k’ibarki gara na zauna a haka na,
Da ya ke Rahma a kwai jiki ga ta gajeruwa gab da k’asa ga bud’ad’d’an hanci sai k’aton baki,gara Sakina ta fi Rahma komai don ita da tsayinta irin na Abba,ba dai wani kyawun aje agani gareta ba don duk Umma suka kwaso,