NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Da sauri nayi baya ina kallonsa,shi kuwa yana gama fad’a yayi juyawarsa ya fuce,na dad’e a tsaye cike da mamakin jin kalaman Yah Ameen na shiga jujjuya kalaman a raina,”toh me ya ke nufi wa yagayar mai ina kula wasu samari,ni banma kaina kallon wata budurwa tunda kwanan nan muka shiga (SS1)d’aga kafad’a nayi alamar ko ajikina,ni daman me son karatu ce ina da burin ganin nayi ilmi mai zurfi,

Washe gari ina zaune a farlour sai ga Abba ya shugo hannayensa d’auke da manyan ledoji,ya zauna kusa da ni yana murmushi,nace “Abba sannu da zuwa,”yauwa ‘yar albarka,Umma ta kaida kai tare da ta6e baki tace”sauran ka kira su da ‘yan tsiya tunda kai ke bada albarkar,ba wanda ya kulata cikin mu Abba ya mik’omin ledar da yashugo da ita yace……

Fateenku ce????

      Ummu Affan

????CIKIN WAYE?????

❤❤❤❤
❤❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

????1⃣9⃣-2⃣0⃣

????Abba ya mik’o min ledar da ya shugo da ita,yace”ga d’inkin nan da kayan saukar na amso miki,na kar6a ina dariya nace”kai Abba da kanka me makon tunda Yah Ameen ya sanar da ni gurin d’inki da ka barni na amso,

Yace”naga na biyo ta wajen ne shine da yace ya gama na kar6o miki,nace”nagode Abba ina k’okarin bud’e ledar,d’inki yayi kyau sosai daman kala uku ne Atamfa sai Shadda da Leshi kuma anyi min d’inkuna masu kyau,nace”gaskiya Abba sunyi kyau Allah ya saka da alkhairi,ya amsa da “Ameen,

Umma ta mik’e tsaye tare da buga wani uban tsaki mtssuuw!!,”Ayi dai mugani idan tusa zata hura wuta kuma ai k’arshen alewa k’asa,ta galla min harara tayi gaba,Abba yace”karki damu da wannan abun da tayi kinji,nace”ni Abba na rigama na saba da halin Umma,yace”kici gaba da hakuri har Allah ya kaimu lokacin da zata gano gaskiya,nace”toh,Abba Allah ya ganar da ita,ya amsa da “Ameen,

Na kwashe kayan na nufi gidansu Zainab don in nuna mata,ina shiga na iske ita ma murnar take an amso mata nata d’unkunan,nan na zube mata nawa,tana dubawa tace”kai Naanah kinga naki har sunfi nawa kyau,Yah Marwan yace”toh ya son ranki ita fa ‘yar gatan Abba ce ke kuma ‘yar gatan waye?,jikin Hajiya ta fad’a cikin shagwa6a tace”Hajiya kinga Yah Marwan ko!daman na lura yafi son Naanah a kaina,Hajiya tace”rabu da shi zanyi maganinsa,gaba d’aya muka kwashe da dariya,nace”amma ke Zainab d’innan ‘yar shagwa6a ce,Yah Marwan yace”rabu da ita kawai Naanah ta girma ita bata san ta girma ba ai kuna gama secondry zamu mata aure,

Zainab sai kawai ta saki kukan shagwa6a,tace”ni wallahi ba wanda zai aurar da ni sai na zama cikakkiyar lauya don burina kenan,nace”da gaskiyarki Zainab ina goyan bayanki,Yah Marwan yace”Ok ni zaku had’awa kai,to ke Naanah me kike so ki zama,nace”ni yah Marwan burina in zama (Pediatric)likitar yara,yace”da kyau gaskiya kun burgeni Allah ya cika muku burunku,muka amsa “Ameen,

*** *** *** ***

Daman masu salon iya magana sunce Rana bata k’arya sai dai uwar d’iya taji kunya,yau makarantar tasu cike ta ke da manyan mutane,sakamakon gayyatar da a kayi ta yaye d’aliban makarantar,manyan malamai da attajirai ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa duk sun cika wajen ga dandazon d’alibai,

Tuni aka fara gabatar da duk abinda ya dace,inda aka fara kiran ‘yan sharar fage,daga bisani ‘yan sauka suka fara,lokacin da a kazo kan Naanah zo kuji k’ira’a tana ba ko wanne harafi hakkinsa cikin karatunda sai kai tunanin muryar wata Balarabiyyar ce saboda tsak’in murya,

Bayan an kammala karatun ne sai a ka kira Naanah Firdausi Isma’il a matsayin wacce zata bada tarihin makarantar cikin harshen larabci,”uhmmm humm humm zo kuji murya,turk’ashi ai kowa gurin shuru yayi sai zazzak’ar muryarta da ke tashi,kowa zuciyarsa tayi sanyi sai sauraronta suke,

Wanda bai san Naanah sai ya d’auka ko Balarabiya ce,kai zo kuga kyaututtuka da Naanah ta samu domin ita ce tazo ta d’aya cikin jerin wad’anda sukayi saukar,Yah Ameen wani irin kallo yake mata wanda ita kanta ta kasa fassara irin wannan kallo,

Sun sha hotuna da ‘yan uwa da abokan arziki da malamai abin dai gwanin ban sha’awa,sannan suka tafi da k’awayensu gidansu Zainab a nan zasuyi walimarsu,

An dai yi taro cikin jin dad’i da walwala sai fatan alkhairi

*****

Zaune ya ke a katafaran farlour wanda ke d’auke da kujeru na alfarma,wanda ke d’auke da kayan alatu na zamani,idan ka ga gidan sai ka d’auka wani shugaba ne ko me babban muk’ami a Nigeria,yana zaune ne d’aya daga cikin jerin kujerun falon wanda set biyu ne,zuciyarsa ji ya ke kamar zata buga,kwarai da gaske mahaifiyarsa ta kafa masa abinda ya ke ganin zuciyarsa ba zata iya d’auka ba,shi kansa yarasa wanne irin so ya kewa Naanah kuma son aure ya ke mata,yasan inhar hakan ta kasance yana da babban rikici nan gaba,kuma yad’au burin ko wanne irin rikici ne zai dauke sa indai a kan Naanah ne,

Domin rasa Naanah tamkar barazana ne da rayuwarsa

Tofah,shin wanene wannan ma da ya ke wannan maganar????

Kudaici gaba da biyoni har yanzu bamu tsunduma ciki ba,

Fateenku ce????

      Ummu Affan

????CIKIN WAYE?????

  ❤❤❤❤
       ❤❤
          ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)

Didicated to Hussaini 80k

Kina raina Anty Hauwa,I luv u wujiga-wujiga


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

????2⃣1⃣-2⃣2⃣

????Domin rasa Naanah tamkar barazana ne a rayuwarsa

Wata farar mace wacce baza ta wuce shekaru hamsin a duniya ba,ta sakko daga kan matattakalar benen da ke farlour,har tazo kusa da shi bai sani ba,ganinsa cikin irin wannan halin sai taji hankalinta ya tashi,

A hankali ta zauna kusa da shi tare da dafa kafad’arsa,yayi firgigit ya kalleta,d’an guntun murmushi yai yace”Momy kin fito,cikin a lamun damuwa tace”me ke damunka Al-ameem ka kasa sanar da ni?,yace”ba komai Momy kawai ina d’anyin wani tunani ne,kallonsa tayi cike da rashin gamsuwa amma ganin ya saki ransa sai tace”to banson kana irin wannan dogon tunanin,yace”nadena Momyna bazan sake ba,duka sukayi murmushi,

Al-haji ne ya sakko cikin shadda da a kawa d’inkin babbar riga,ya kalli Ameen yace”My Son ya ka kwana,yace”lafiya k’alau Daddy,yace”yanzu zan fita zamuyi wani meeting ne idan mun gama kasame ni Office,cikin ladabi yace”sai ka dawo,sannan ya wuce,Su kuma sukaci gaba da hira,

*******

Muna zaune ni da Yah Marwan a kan wasu kujerun roba da ke harabar gidansu,ya kirani ne wai yanason magana da ni,gaba d’aya munyi shuru saida baya ya kalleni sosai yace”Naanah nasan baki da saurayi,ko ince duk wanda yazo gurinki baki sauraronsa balle kuyi wata maganar soyayya,hakan da kike yi yana matuk’ar burgeni,amma ni na kasa daurewa saboda gaskiya Naanah tun kafin kikai haka nake k’aunarki tun ranar da na dawo karatuna naganki sai naji kin kwanta min,ina sonki kuma ina burin ki zama uwar yarana,

Kunya naji duk ta kamani,sai na duk’ar da kaina k’asa ina murmushi,ganin haka sai ya d’ago da fuskata muna kallon juna,yace”me kika ce?,

Na k’wace fuskata sannan na mik’e na ruga cikin gida,ikon Allah yace,sai kuma yayi murmushi,

Tun daga ranar sai na dunga wasan 6uya da Yah Marwan,ba wai don bansonsa ba kawai kunya na keji nace masa “na amince,kunsan abunku da saurayin fari shiga rai,

Duk ranar da kuwa yaci sa’a muka had’u,sai ya da meni da tambayar in basa amsarsa,ganin ba zan iya ba sai na tura masa test message,kamar haka,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button