CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Aslm Yah Marwan ykk?,bawai bansonka ba ne a’a ina sonka amma ina so kayi hakuri domin Yayana yayi min gargad’i da kar in kula samari domin karatu zanyi,in har zaka iya jirana toh,bye daga Naanah Firdausi,
Tana gamawa ta tura masa,sai da ta tabbatar ya shiga sannan ta kashe wayar don karr ya kirata,shima da ya gama karantawa yaji dad’in sak’onta domin shi kansa mutum ne maison ilmi,ya d’aga wayar ya kirata yaji a kashe yasan kashewa tayi don kar ya ne meta,murmushi yayi yana bala’in son mace mai kunya,gashi Allah ya had’a shi da Naanah yarinya kyakkyawa ga hankali da nutsuwa uwa uba kunya da hakuri,Naanah duk ta had’a wannan a bubuwan,shiyasa yake bala’in sonta,
Zaune suke da Zainab a skul bayan sun futo Break fast,Zainab tace”waini Naanah meya tsakaninku da Yah Marwan sai naga kamar akwai wani abu,murmushi na d’anyi nace”uhm ke dai bari na mance ban sanar da ke ba,wai Yah Marwan sona ya ke,dariya tayi sosai tace”aini naga alama irin wannan zumud’in da yake akanki abun yayi yawa nasan da wata a k’asa,kallonta nayi”to ke yanzu ya kika gani,tace”wallahi nayi murna Allah yasa ayi damu,nace”Amin to,ta kaimin dukan wasa,tace”ashe dai ana so,nace”ke kanki kinsan Yah Marwan ya kai a so shi,tace”kin fasa karatun kenan sai aure,nace”a’a zanyi karatuna mana,gaba d’aya mukasa dariya,
Wata irin soyayya da shak’uwa ce tsakanina da Yah Marwan yanzu,sun shak’u sosai cikin k’ank’anin lokaci,saidai a kullum Naanah tana tsoran kar Yah Ameen yazo ya ganta da Marwan,ita kanta Hajiyarsu Marwan da taji abin ya mata dad’i don tana matuk’ar k’aunar Naanah da tausayin halin da take ciki a gidansu,
Marwan yana k’aunar Naanah bilhakki da gaskiya,yanzu haka ma suna tare,sak’on soyayya kawai suke aikawa zuna don ita ma Naanah yanzu ta cire kunya tana furta masa kalamon so don tana sonsa,sun shagala sosai suna hirarsu cikin nishad’i da begen juna,a haka motar yah Ameen tazo gurin basu sani ba,
Shi kuwa da ke cikin motar yana hangensu,ji yayi zuciyarsa na barazanar bugawa,wani irin abu yaji yana kaiwa da komowa a zuciyarsa,idanuwansa nan take sukayi wani jawur zuface kawai ke kwarara a fuskarsa……
Muje zuwa dai????
Karku manta Fateenku ce????
Ummu Affan✍????
????CIKIN WAYE?????
❤❤❤❤
❤❤
❤
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
Masoya nima ina yunku,kamar yadda kuke yi da wannan littafin,ina sonku fiye da yadda kuke son CIKIN WAYE?,Fatana kuci gaba da suburbud’omin Comments d’inku yana k’aramin k’warin gwiwa,Ina yinku sosai,One luv????
Bismillahir rahmanir rahim
????2⃣3⃣-2⃣4⃣
????Zuface kawai ke kwarara a fuskarsa,
Aransa yace”lallai nayi mugun sake amma…bai k’arasa ba ya fita a fusace,ya doshi inda suke zaune,basu ga taho warsa ba,saiji tayi an funcukota,kyakkyawar marin da taji Afuskarta yasa ta gigita jinta da ganinta suka d’auke na wucin gadi,wasu fararan taurari take gani saboda tsabar shigarta da marin yayi,cikin 6acin rai yace”Naanah yaushe kika koyi rashin ji,kenan maganar da na fad’a miki ta shiga ta kunnen dama ne sannan ta fita ta hagu,aijin muryar Yah Ameen yasa ta mik’e da sauri tayi ciki a gigice,
Ya kalli Marwan cikin izgili tare da ta6e baki yace”kai kuma a suwa don Allah ko kunya bakaji ba kazo k’ofar gidan mutane wai da sunan hira duka ya Naanah ta ke da zaka zo wai hira,to bari kaji daga rana irin ta yau banson sake ganinka da Naanah,Marwan ransa yayi mugun 6aci yace”Al-ameen kai baka isa ka rabani da Naanah ba don tana sona,nima kuma ina k’aunarta,kallon raini ya masa miskilanci ya 6otsa,k’ala bece masa ba yayi gaba abinsa,har zai shiga gida sai kima ya juyo cikin muryarsa ta isa yace”Ok muzuba mugani ni dakai,yana gama fad’a yayi shigewarsa,
Marwan ransa ya 6aci aransa ya fara shakku anya Al-ameen da Naanah ciki d’aya suka fito,don a maganganunsa tsantsar kishne ke tashi,d’an guntun tsaki yaja mtsuuww!ya wuce,
Ita kuwa Naanah a rud’e ta shiga cikin gidan tana zuwa ta fad’a jikin Abba tana kuka,Umma ta daka mata tsawa”ke da uban waye zaki shugo mana kina kuka,kan ta bata amsa sai ga Yah Ameen ya shugo rai a 6ace,yayo kanta zai duketa da gudu ta ruga bayan Abba tana ba shi hakuri,
“Don Allah Yah Ameen kayi hakuri bazan sake kulashi ba,ya dank’ota yace”idan kika sake kulashi fa,da sauri tace”ka kasheni kawai,tsaki yaja”ba zan kasheki ba amma sai jikinki ya gaya miki,cikin kuka tace”nayarda,nayarda wallahi nayarda,kunsan Naanah da shegen tsoron bugu,
Sakinta yayi tare da cewa “zabuwa kawai sai shegen tsoro,zaunawa yayi tare da gaishe da iyayensa,Umma aranta sai dad’i ta ke ji wai yau Al-ameen ne da bugun Naanah shi da baison a daketa ko k’uda inda da hali baiso ya ta6ata,,Abba yace”yau me ya had’aka da mutuniyar taka ne,yace”Abba rabu da ita kawai yanzu Naanah ta koyi rashin jin magana,Abba yace”Naanah har yanzu yarinya k’arama ce sai ana binta a hankali,Umma tace”haba dai ai Naanah ta wuce yarinya k’arama wacce ke SS2 aji biyar a secondry ai ta wuce a kirata yarinya,don da tasami miji aurar da ita za’ayi mu huta,
Da sauri ya kalli Umma yace”a’a Umma tunda Naanah tana son karatu to zamu bata wannan damar Rahma da Sakina sune zasu fiddo mazaje tunda sunk’i karatun kulum shekarunsu k’aruwa suke,yanzu Rahma shekarunta 26 Sakina ce me 23 ita kuwa Naanah sai wannan shekarar ta cika 17,
Harararsa tayi tace”to uban iya mace ake kira uwar iya amma kaima yau kazama uban iya kai ka haifarmin ‘ya’yan to nida na haifi a bina ban gaji da ganinsu ba,Sakina tace”nidai Yah Ameen a kwai wani saurayina da yacemin zai turo,yace”to masha Allahu,ke kuma Rahma fa?,kai ta fara sosawa,kafin tace”babu,Umma tace”nifa karka takuramin yara kabarsu idan ta samu namaka magana,ke kuma basai kin takura kanki ba idan wanda kike so yazo saiki magana,tace”toh,
Abba tashi yayi yana girgiza kai cike da takaicin irin wannan hali na Umma,ya nufi d’akinsa,Umma ta kama Rahma suka wuce ciki,Ita ma Sakina tabi bayansu,
Daga ni saishi a farlour,ya maida kallonsa gareni,k’asa nayi da kaina na kasa had’a ido da shi,hakan yasa ya sami damar k’aremin kallo,Naanah kyakkyawa ce ajin farko balle yanzu da ta zama budurwa tana da cikar zati ko a cikin mata samun kamarta sai an tona,dole duk namiji mai hankali yaso ace ya sami kamar Naanah don ta tara komai da akeso,
A hankali ya tashi daga inda ya ke ya dawo kujerar da take zaune,ya ruk’o hannayenta suka had’a ido,tare suka saki a jiyar zuciya,yace”Naanah me yasa kika mance gargad’in da na miki,tace”don Allah kayi hakuri Yah Ameen bazan sake ba,kallonta yayi yace”Naanah kina sona kuwa?,da sauri ta kallesa jin abinda ya fad’a tace”me kace Yah Ameen,yayi saurin dawowa duniyar da ya fad’a tare da gyara furucinsa yace”cewa nayi kina son karatun nan kuwa?,ajiyar zuciya tayi,tare da gyad’a kanta alamar”eh,yace”to kar in sake ganinki da Marwan idan ba haka ba kuma sai mu aurar dake yadda Umma tace,yana gama fad’ar haka ya mik’e ya fita,
D’akina na shiga na fad’a kan katifa ina numfashi,wayata ce naji ta fara k’ara na jawo wayar,lambar Marwan ce kamar karta d’aga,sai kuma ta d’aga asanyaye,”hallo yace,a hankali tace”ina jinka Yah Marwan,yace”Naanah abinda kika yi kin kyauta kenan,tace”kayi hakuri yah Marwan kasan dama na sanar dakai tun farko Yah Ameen ya hanani kula kowa,kuma kaga dai yadda ransa ya 6aci gaskiya ni bana son ransa ya 6aci,yace”ok ni kike so raina ya 6aci kenan,”a’a ba haka na ke nufiba,”to me kike nifi Naanah amma ba komai,kawai ya kashe wayar,d’aga kafad’a tayi sannan ta gyara kwanciyarta nan take kuwa barci ya kwasheta.