NOVELS

CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Kuka nake kamar raina zai fita ina bata hakuri”wallahi Umma bansan CIKIN WAYE ba a jikina kimin rai kiyi hakuri,Abba ne ya taso ya ture Umma wuk’ar ta fad’i yace”kee!wacce irin mahaukaciya ce,ita ma a fusace ta tashi ta sake yowa kaina”ai gara in kasheta kowa ya huta taya zamu had’a shegu har biyu a gida,muna so murabu da k’aya za’a k’aro mana wani to bazai yuwuba,

Ganin ta tun karoni,nayi gurin Abba da gudu ina kuka na k’amk’amesa,jana yayi bayansa yace”Karimatu karki kuskura ki ta6ata,kallonsa tayi a wulak’ance ta juya ciki a matuk’ar fusace,

Zaunar da ni Abba yayi gefe dare da dafe kansa,duk’awa nayi gabansa cikin matsanan cin kuka nace”Abba ka yarda dani wallahi tallahi bazan CIKIN WAYE ba,bansan yadda akayi na sami wannan cikin ba,yau ni na shiga uku ya zanyi da rayuwata ya Allah ina rok’onka ka d’auki rayuwa ko na huta da wannan kuncin na duniya,

Da sauri Abba ya rufemin baki yana girgiza kai”Ki dena fad’in haka Naanah na yarda da k’addara nasan ke bazakiyi hakan ba Allah shine mafi sanin abinda ya faru da ke,ke kuma taki k’addarar kenan,

Wani matsanan cin kuka na saki tare da zubewa jikin Abba nace”nagode Abba da ka fahimce ni daman nasan kai mai fahimta ne

****************

Tun daga wannan rana rayuwata ta sake jagulewa,ina matuk’ar jin tasko gurin Umma da Anty Rahma,magungunan gargajiya kala-kala Umma ke d’uramin don cikin ya zube amma kamar ana k’ara masa ban ruwa fon beda alamar zubewa,

Gaba d’aya wankin gidan ni ke yinsa haka wanke-wanke,shara goga kai da duk wani aikin wahala har ruwa Umma ke aikena d’auka duk da yah Ameen ya mana bohol,amma Umma tace saidai inje waje in dauko,duk da k’udirinta na cikin ya zube amma ya k’i,

Yau kimanin watanni biyu kenan da faruwar hakan zuwa lokacin tuni nayi wata irin muguwar rama,k’ashin wuya ya fito sosai nayi duhu duk haskena amma na koma bak’a,saboda aikin wahala ga bugu ko ishasshen abinci ban samu a fad’ar Umma idan ina cin abinci da yawa cikon dole zaik’i fita,ko wayata ban takanta tun ranar da naji cewa wai ina da ciki wanda bansan CIKIN WAYE ba,na kashe wayar daman Yah Ameen yayi tafiya England a kan harkar kasuwancinsu,tun kan wannan abun ya sameta,

Tana kwance a d’aki bayan ta gama cin uban wankin da Umma ta sata,sai numfashi take yunwa takeji kamar zata mutu amma Umma tace yau sai na dare zata bata tun safe ba abinda taci,kuka take tana bugun cikinta da k’arfi,cikin kukan take cewa”ciki don Allah kafita yau na shiga uku ya zanyi da rayuwata shikenan burina na karatu bazai cikaba shi kenan nasan na rasa Marwan dan nasan bazai auri wacce tayi ciki ba shi kenan nasan Yah Ameen ya dawo kasheni kawai zaiyi,yau nashiga uku me yasa rayuwa kikazo min da haka meyasa hakan ya faru dani bayan ban ta6a aikata zina ba meyasa rayuwa ta take a haka ni bansan wani farin cikiba tunda na ke sai akasin hakan,me yasa…me yasa…Wayyo Allah kad’au raina kawai na huta da wannan mummunar rayuwar,ta kife taci gaba da kuka mai cin rai,

Sakina da tun d’azu tazo d’akin,sai jin hawaye tayi na tsiyayar mata,tunda tayi aure tayi hankali balle da ta had’u da muguwar kishiya me gasata son ranta,sai ta dawo tausayin Naanah da tausayawa rayuwarta sosai yanzu take jin Naanah cikin ranta,

k’arasawa tayi tare da dafata Naanah na juyowa ta rungume Sakina tace cikin kuka”don Allah Anty Sakina ki kaini inda za’a kasheni na huta wallahi na gaji da wannan rayuwar,da sauri Sakina ta rufe mata baki tace”A’a Naanah kar bak’in cikin da kike ciki yasa kiyi sa6o ki zamu me ta wakkali a duk kan halin da kika sami kanki Umma ta sanarmin ko mai Naanah na tausaya miki nasan halinki bazaki aikata hakan ba,amma ina mamakin taya hakan ya faru da ke,cikin kuka fuskarta har ta kumbura saboda kuka tace”bansani ba wallahi bansan taya hakan ya faru dani ba bansan CIKIN WAYE ba,

Sakina ta jinjina kai cike da tausayin Naanah tace”to ya isa kidena kukan haka,komai daran dad’ewa gaskiya zatayi halinta,nan taci gaba da sharemin hawaye……

Wasa farin girki,muje dai zuwa fans,plsss sharhi nike buk’ata ba wani tnx ba,da fatan angane????Lol ana tare,kar ku mance,

Fateenku ce????

          Ummu Affan✍????

????CIKIN WAYE?????

  ❤❤❤❤
       ❤❤
          ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

Fans I luv u,wujiga-wujiga,Farin ciki kune masu baiwa Fateemah,bak’in ciki in nai kusakani dariya,da na ganeku sai inji nazam sarauniya????comments d’inku na jiya yasani farinki,
Wow jiya nayi tsalle da murna kunsani farin ciki da ina karanta Comments d’inku,aci gaba da gashi ina yunku irin sosai d’in nan❤???? nagode????

Bismillahir rahmanir rahim

????2⃣9⃣-3⃣0⃣

????Sakina tana sharemin hawaye,sai ganin Umma muka yi ta fad’o d’akin kamar an turota,

Cikin fad’a ta kalli Sakina tace”Ehye yamiki kyau in zauna in sanar da ke abinda shegiyar yarinyar nan tayi shine kika zo kina rarrashinta kamar wata k’aramar yarinya,

Sakina ta kalli Umma tace”haba Umma ki kalli yadda Naanah ta koma ai abin a tausaya mata ne,cikin rage murya taci gaba da cewa”Umma ina rok’onki da Allah ki tausayawa halin da Naanah take ciki kiyi tunanin inda mune muke cikin wannan halin ya zakiji ki duba wulak’anci da cin kashin da abokiyar xamana take min nasan bakijin dad’i kuma…,

“Ya isa haka Umma ta katse Anty Sakina cikin tsawa da fad’a,tace cikin masifarta”ke kika so kuma ke kika k’yale kishiyarki da baki maganinta wallahi masifa da bala’i kawai idan kika rufar mata sai ki kori kafirar amma kin zama wata shashasha sakarya tunda kikayi aure sai kace kanki farau,Sakina ta kalli Umma cike da takaici wai uwarta ce ke fad’a mata sbinda ko k’awayenta bazata so su gayamata ba Umma ta gama cutarsu,

Tace”haba Umma don Allah kiwa kanki fad’a wallahi abinda kikeyi sam bai dacewa,wata ashariya da Umma ta saki ni kaina saida na toshe kunnuwana tace”to dan ubanki saiki zo ke kimin kujimin ja’irar yarinya ni kike gayawa magana Sakina saboda kinyi aure,tace”Umma don Allah kiyi hakuri ni wallahi yanzun na tuba duk wani abu mara kyau na dena na dama danayi ina roko Allah ya yafemin,ta kalli Naanah tace”kema ki yafeni Naanah ko na sami sassauci don yanzu nasan mugunta bata dad’i fitsarin fako ce,Umma taja tsaki”ke yadama ni babu ruwana,ta fita tana masifa,na jawo Anty Sakina nace”kiyi shuru ni ban ta6a ruk’arki a rainaba Allah ya yafemana baki d’aya,haka suka rungume juna suna kuka sosai,

Marwan ne sai safa da marwa yake a farlour,danna waya yake yana karawa a kunne alamar kira yakeso yayi yayi hakan yafi sau goma da alama wayarce bata shiga,sai guntun tsaki yakeja,Zainab ce ta sakko matattakalar bene,itamma cike take da damuwa,zaunawa tayi kan kujera tace”yah Marwan lafiya kuwa,mtsuuww yaja tsaki”wai Zainab lafiya naga ban ganin Naanah wallahi duk hankalina atashe yake gashi sai gwada kiran wayarta nake tak’i shiga,

cike da damuwa Zainab tace”nima ina cikin damuwar rashin Naanah kusan wata uku rabona da ita kasan halin Ummarsu kwanaki na shiga muka had’u a zaure wallahi idan kaga cin mutumcin da tamin sai kayi mamaki tace karna k’ara shugo musu gida,

Marwan yace”jikina na bani Naanahta babu lafiya ya zanyi Zainab wallahi inason in ganta,

Zainab tace”nima inason ganinta bansan yadda zamuyi ba lambarta bata shiga kullum sai nakirata fiye da sau ashirin,Hajiya ta k’araso wacce duk taji hirar da suke ta zauna sannan tace”Allah yasa dai tana lafiya fonni kaina abin na damuna Naanah bata ta6a kwana uku bata shugo gidan nan ba,bare wata uku,ta jinjina kai “uhmmm ni abin wallahi har tsoro yake bani Allah dai yasa lafiya,dukkansu suka amsa da amin cike da juyayi da tashin hankali,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button