MURMUSHIN AJALI COMPPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MURMUSHIN AJALI COMPPLETE HAUSA NOVEL

[08/10 8:33 am] Me Kosai✍: ???? ????
???? ????
???????????????????????????? MURMUSHIN AJALI
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????
Written by Aysha Wakili
Mrs ahmed

duk wanda yajuyan labari ko yai editing Allah ya isa banyafe va ”labarina ne dakaina nakago shi danhaka aguji juyamin shi takowace iron siga

EXCLUSIVE WRITER’S FORUM
E.W.F

gaisuwa gareku oll member’s of exclusive ina alfahari daku
ummiey zee
amnoor
ruksad
ummu khamal
jamila k Mashi
neenah cool
action baby
hummy luv
habeebty bieboh
serdy barsh
queen memue
biebie
nabilancy luv
aunty halilos
Aishat A Muh’d
pharteemah
queen habiba
phauzzy ammani
billyz
aishan umma
goshh kunada yawa hannuna bare Iya rubutoku dukava ‘amma kusani kuna raina

dedicated to friend bee kalbi Miemie

Page1⃣

Alh zoka gani wlh idon yarinyar nan tsoro yake bani”sannan cikin dare saina juya baran ganta a Inda na kwantar daita va ”gsky alh yakamata kaduba wannan lamarin ‘tun kan yayi nisa”’

Kinga hafsa ni banason irin wannan zargin naki yarinyar dako’ kwana arba’in batai da haihuwa va” zaki sakata gaba kina cewa waitana wani abubuwa toni gsky banason haka”’

Kebaki godeba ma da Allah ya azurtaki da yarinya kyakkyawa kamar yar’larabawa ”” cikin sauri hafsa takatse shi da cewa” alh nagodewa Allah ”’daya bani haihuwa bayan shekaru takwas da aurena”

Nayi farinciki da samun ciki koba komai yan’uwanka dasuka kafamin tarkon kiyayya zasu dena tunda nasamu abinda yasa suke ki’na””

Saidai kash wlh duk farinciki na yakau tundaga ranar Dana fara nakudar Miemie ‘sbd nikadaice nasan barazanar Dana fuskanta a haihuwarta ‘ sannan bayan na haifeta nikadai nasan menake ji cikin dare idan munkwanta””””

Ni kyaun wannan yarinyar tsoro yake bani ‘domin gaba dai batai kama da kowa cikin zuri’armu ba ”’ nikam tafiyimin kama da jesmin wacce muka hadu da ita a misra lokacin damuka je Hutu ””

Tsawa alh yadaka mata yana huci yace karki sake dangantamin diya da waccen jesmin din me tsiffar aljanu inba haka va zakiga 6acin raina”””’

Cikin fushi alh yafice yabar dakin yana huci””””” hafsa koh zama tayi tadafe kanta tana kallon Miemie tana hawaye”’

Cikin rawar murya tafara magana tana cewa narokeki miemie Dan girma Allah Idan ke ba bil’adama bace kifice mana arayuwar mu da kwanciyar hankalinmu””

Karki wahalar dani ”zan Iya jure rashib haihuwa amma baran Iya jurewa va” idan naganki da wannan siffa ”’Miemie kitaimaka kibarni naji da bakin cikin dake zuciya ta””’

Ina kaunarki sosai acikin zuciyata hakan yasa banaso ki fuskanci barazana ”sbd kyawunki yayi yawa baran Iya jurar ganin bakin ciki anan gaba ba”’

Jitayi anshureta da kafa tana juyawa taga Miemie ce tadaga kafa sama tana dariya””’_cikeda fargava hafsa tace Miemie idonta azare????

Kallonta takeyi tana dariya cikin tashin hankali hafsa tashiga karantoh suratul jinn ””’gani tayi Miemie tai lamo tarufe ido kamar me bacci”

Cikeda fargaba hafsa tafito falo tazauna ‘baki daya komai yajagule mata”’ tarasa yazatai da rayuwarta”’

Tana nan zaune alh yafito daga dakinsa zaifita hangota yayi zaune tana sharce hawayen fuskarta ”cikin hanzari yakarasa kusada ita ”

Yace hafsa meke damunki ne wai? Dago kai tayi tana kallon fuskar shi”’tace bakomi alh damuwa tace katafi gun aikinka kawai””

Cikin sanyin jiki yazauna yajanyota jikinsa yana cewa hafsa banaso kina sawa Ranki damuwa akan abinda kike zato”wnda ba gsky bane”

Pls kidena damuwa Miemie yar’ki ce ke kika haifeta baikamata kinayi mata mugayen zatova” pls kidena kinji matata?

Kai ta gyada mass alamar taji ‘sannan ta share hawayen fuskarta tace shikenan alh naji ‘zandena ”

Murmushi yayi yace yauwa matata ”tashi muje kiymin rakiya'”

Cikin murnushi hafsa tamike domin raka alh”’

tuna baya malam bukar wanzam haifaffen garin kano ne a unguwar yakasau yana zaune da iyalansa acan ”mutm ne mai kimanin shekaru saba’en aduniya”’ yanada matan aure uku”’ uwar gida itace bahba Laure ya’yanta biyar ‘kabir,Suleiman,hadiza ,sadiya,murja”

Saita biyu sunanta bahba asabe ya’yanta hudu”_Abdulkadir ,mansura,rashida,sai mansir”’

Ta uku itace inna amarya”ya’yanta biyu Mahmud sai kanwarsa sa’adatu”””’

Gdn malam bukar babban gd ne kasancewar yanada dan’rufin asiri ”sannan ga iyalai dayawa::: danhaka kowace mata da 6arayinta”’

Zaman lfy kam a gdn babu laifi Dan Laure da asabe Kansu ahade yake sunware inna amarya basu cika Hulda daita va”

Itama kuma bata damuva ya’yanta sun isheta rayuwa”

Dukka ya’yan malam bukar matan sunyi aure ‘sbd dazarar sungama secondary yake aurar dasu”’

Danhaka acikin mazanma akwai wayanda sukai aure”

Wayanda suka rage daga mansir sai Mahmud sukadai ne basuyi ””

Mansir bashida niyyar aure ayadda yace saiya ci duniyarsa da tsinke kamin zaiyi aure””

Mahmud ko shekarunsa ashirin da shida yana jami’ar bayero dake kano’ yana shakararsa takarshe Inda yake karantar business administration” yana final yeah dinsa”

Lokacin bikin sa’adatu kanwarsa” yagabato danhaka sai shirye shirye sukeyi ”’abikinne mahmud yahadu da hafsa ‘yar’wan mahaifiyarsa”’ nan suka kulla soyayya maikarfi”’

Inda kowa yasani a danginsu ‘nan aka tsaidah magana akan daya dawo service za’ayi bikinsu ,,

Aiko cikin hukuncin ubangiji mahmud yagama service dinshi lfy”nan akayi bikinsa yatare da matarsa hafsa adaya daga gdjen mahaifin mahmud daya basu””

Haka rayuwa tacigaba da tafiya da mahmud da hafsa cikin so da kulawa”’

Sunada shekara daya da aure sa’adatu kan’war mahmud tahaifo dan’ta namiji kyakkyawa dashi”

Ranar suna yaro yaci sunan ya’yan mejego wato mahmud ”amma zasuna kiranshi da sultan ”” ganin irin wannan karan da akayiwa mahmud yasa daga hafsa harshi mahmud din sunyi rawar gani wurin nuna murnarsu”’

Kaya suka hadawa jariri nagani nafada duk da bawani karfi garesu va ”’
Amma dai sunyi rawar gani”

Wata tara da haihuwar sa’adatu tasake samun wani ciki””’ tashiga damuwa sosai ganin ga yaro ahannunta tana shayarwa ” Ranar da hafsa tazo gdnta ta Tatar da sunata darga itada mijin””

Nan ta tambayi dalili ”musa dakanshi yaiwa hafsa bayani kan cewa waiso take azubar mata da ciki”’

Cikin damuwa hafsa tace haba sa’adatu kiyi hkr karki zub da wannan cikin’ baki ganin mu muna nema da kudinmu ma bamu samuva amma ke kinsamu zaki butulcewa mahaliccinki””

Indai akan sultan ne kihada masa kayansa natafi dashi na yayeshi”” shikenan inbaya gabanki aibaraki samu damuwa va”’

Nan musa yashiga cikin murna yahado kayan sultan yakawo yabawa hafa nan takar6a tagoya sultan ”

Koda mahmud yadawo da daddare yaga hafsa da yaro”cikeda mamaki yace hafsa yaron waye kika samu? Cikin murmushi tace sultan nefah”

Cikin zaro ido mahmud yace ina ita sa’adatun? Cikin damuwa hafsa tabashi’ labarin yadda sukayi”’

Shima mahmud din fada yaitayi yana cewa wasudai basu San baiwa da Allah yaimasu ba saisuita wofantar dashi”

Haka suka Shiga rainon sultan cikin so da kulawa” cikin wata biyu yaro yamurje yazam gwanin sha’awa” yana cika wata shabiyu yafara tafiyarsa koina”

Gashi yaron kyakkyawa dashi ‘fari tas bayada kwarafniya ”kullum cikin kwalliya zaka ganshi sbd hafsa badaga nan ba indai fagen tsafta ne taciri tuta””'””’
[08/10 8:33 am] Me Kosai✍: ???? ????
???? ????
???????????????????????????? MURMUSHIN AJALI
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????
Written by Aysha Wakili
Mrs ahmed

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button