MURMUSHIN AJALI COMPPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MURMUSHIN AJALI COMPPLETE HAUSA NOVEL

Baabaa asabe tajuyo tadubi Mahmud tace mahmuda anya ko musa ba gamo yayi da autan aljanu va’kaduba kaga yadda halittarsa ta sauya lokaci guda?

Cikin shariya Mahmud yace toh baabaa ni inazan SANI tunda ba agurin nakeva lokacin da abin yafaru”’

Jinjina kai baabaa asabe tayi tace ‘akwai ayar tambaya akan musa kod’ai yaci masu bashi ne bai biyava””’sultan ne yadubeta yace haka yafada maki?

Cikin hassala tace toh isasshe dakai nayi?

Shiru sultan yayi baikara cewa komeva””” hakan baisa baabaa asabe tai shiru da bakinta va””

Miemie na shigowa taji abinda baabaa asabe ke cewa nan take taji ranta na suya”””cikin dak’ikai dabasu gomava ‘idonta yajuye amma babu Wanda yalura””’

Kallon gadon da baban Aysha yake kwance Miemie tafarayi”’nan take hannun shi yafara motsi yana d’aga ”’amma babu Wanda yagani”’.

Ahankali hannun yafara mikewa yana kara tsayi’,sosai hannun yake kara tsayi”” daidai lokacin baabaa asabe na dago kanta’ aiko tahango hannu sai mikewa yakeyi yana kara tsawo”

Da Sauri taja da baya tabar wurin gadon”’ kusa da sultan takoma” ta tsaya’,amma ga mamakinta saitaga kamar hannun na nufota”’.

Da Sauri takoma bayan sultan ta tsaya tana yi masa rad’a a kunni”’ sultan kalli gun gadon can kaga menene awurin”’

Sultan cikin quluwa yace nibanga komeva””ido taruntse Takara budewa ‘ganin dai hannun sai nufota yakeyi”” dagudu taje Inda gwaggo sa’a ke zaune tace sa’a wlh hannun mijinki tsayi yake krawa duba kigani””

Cikeda mamaki gwaggo sa’a tadubeta tace haba baabaa kibarni naji da abinda ke damuna mana”’ wani hannu ne kuma yake kara tsawo bayan ‘ga baban Aysha kwance da hannuwan sa kina kallo””

Afirgice baabaa asabe ta matsa tana cewa wai me kuke nufi ne””’
Jin hannu ya damke mata wuya ‘ihu takeson yi amma takasa ”sai ido data shiga zarewa tafara tarin dole””””””

am so sorry masoya wannan littafi ina ganin sak’on Ku ”da masu cewa wulakanci nakeyi dan naga anason littafina ‘da masu cewa banason amsa su inasunyi magana duk ina Baku hkr”kuma kunsan dan Adam ajizi ne”’. Sannan inaso kusan saida cikakkiyar lfy zan Iya typing ”danhaka banida ita ‘inakan hanyar Neman magani ‘kuma inasamun sauki da ikon Allah ”kuci gaba da bibiyata ‘nikuma insha Allah Dana samu karfi sosai zaku fara jina akaikai ngd

maman ma’aruf naga sak’onki kuma ga cigaban nan inafata zaki kasance tare dani akoda yaushe ngd””””husnah da khady kuma duk naga sak’onku ”amma inakuka 6atan rai saina shekara banyi typing va ehe????????

one love ”ana tare????
[08/10 8:33 am] Me Kosai✍: ???? ????
???? ????
????????????????????????????
MURMUSHIN AJALI
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????
Written by Aysha Wakili
Mrs ahmed

yawan magana akan abinda bai shafeka va yana haifar da bak’in jini”’ka fuskanci abinda kasa agaba shiyafi alkhairi””rayuwa babu tabbas

happy sallah to oll Muslim’s ‘aci ahankali kar ashake

dedicated to friend bee kalbi Miemie

Page1⃣9⃣

Sultan ne yajuyo yana dubanta ‘yace wai baabaa lfy kike tari haka?

Ganin yadda idonta suka firfito gashi tarike wuyanta da hannu sai kokawa take dashi” yasa sultan firgita ”’cikin karaji yace abba kalli kaga””

Da Sauri Mahmud da sauran mutanin d’akin suka juyo ga baabaa asabe”’, Mahmud ne yakarasa yarike hannunta yana cewa baabaa lfy meyafaru””

Cikin fisge hannunta take nunawa Mahmud wuyanta” ba shiri Mahmud yajata xuwa waje” baabaa Laure dake tsaye agu duk ta rude tarasa mezatayi”” sai raba ido takeyi””

Suna fita hannun yasaketa ”’yana sakinta tasaki jiki tazube akasa ”tana maida wani waha lallen numfashi””””

Mahmud ya kalleta yace baabaa waimeke faruwa dakene? Cikin alamun jin jiki ”tadubi mahmud ”tari tafarayi”’ kamin tadubi mahmud tace ””’

Kaga mahmud wlh shaken wuya akayi” na tabbata mutuwa akaso nayi ”badan kafiddoni a d’akin va ” saidai a fiddo gawata” dan’haka ”’ni baran Iya komawa cikin d’akin nan va”’

Dan na tabbatar idan nakoma toh ajali ne ke kirana””'” ka koma nizanyi zamana anan ””’

Mahmud yace haba baabaa aibare yuwuva kawai kitashi mukoma”” cikin quluwa tace eh aidole kace natashi mukoma dashike bakason ganin ina numfashi a doron k’asa”’

Girgiza kai mahmud yayi yace Allah yahuci zuciyarki baabaa ”barin koma”””””””yana wucewa tabi bayanshi da kallo tana maganganu””’

Bayan kwana biyu ‘bayan an sallamo baban Aysha daga asibiti””’ sunkoma gd’ mahmud sai zirga zirgar tafiyar sultan yakeyi sbd saura kwana ukku tafiyarsa””

Sannan yanaso yagama da tafiyar sultan farko kamin yafara Neman maganin baban Aysha””

????????????????????????????
Sultan zaune a d’akinsa sai harhada kayansa yakeyi cikin jaka ”Miemie ta turo k’ofa tashigo”’ kallonta sultan yayi yace ke baki Iya sallama bane?

Cikin yatsina fuska tace baka koyamin ba ai”””girgiza kai yayi yace shikenan kije makaranta akoya maki”

Zama tayi tadube shi tace ynxu yah sultan kai baraka hkr da wannan tafiyar va”? Nifa wlh inka tafi baranji dadiva”””kuma saidai nakoma gdn tsoho meran karfe””

Cikin dariya sultan yace oho ke kika SANI’ karkiji dad’in mana ”lokacin da ilimin dazanyi zaimaki amfani lokacinne zakiji dadi”’ ni karki dameni ‘inba tayani had’a kaya zakiy va”””’

Cikin jin haushi tace tab lallaima yah sultan d’in nan ”amma dai kome zakace I will nt miss u again” saikaje kaci karatun ”

Murmushi yayi yace huh Miemie kedai yadda kikasan murd’adden kan keke haka kike”baki daya bakida saiti”””’

Cikin 6ata rai tace aiko zakaga rashin saiti ””’fuu tafice a dakin”’

Girgiza kai sultan yayi yana cewa Allah kashirya wannan baiwa taka””””

D’akin mommansu tashige tana kwalla mata ”’hafsa tadubeta tace waike yaushe zakiy hankali ne kirinka kwallawa mutm kira saikace wacce ta 6ace hanya””

Cikin zumbura baki ‘Miemie tace mommah kinga yah sultan koh”” hafsa tace meyai maki”?

Cewa fah yayi wai banida Sauri saikace kan keke””””

Dariya hafsa tayi tace toh karya yayi? Kallonta Miemie tayi tace kema hardake mommah ?

Gyada mata kai hafsa tayi tace ai inbara kiyi hankali va ‘to nima baran goyi bayanki va””’

Cikin jin haushi Miemie tace aidama nasan kun tsaneni amma daga yau baraku kara ganina a gdnku ba””’. Tattara kayana zanyi nakoma gdn tsoho meran karfe ”nasan shi yana sona””’

Dariya hafsa tayi tace kije da kafarki zaki dawo”’miemie tace wlh baran dawova ”””’nan tawuce d’akinta tafara had’a kayanta cikin akwati””

Bayan tagama tafito ta leka falo babu kowa danhaka” tasa kai tafita”’ adaidaita ta tare tashiga ”””

Malam bukar zaune kor gdnsa” yahango Miemie da akwati da Sauri yamike yana takawa ahankali ya isa gareta ”yace mairo INA zuwa haka da akwati?

Dariya tayi tace tsoho nadawo gdnka ne da zama ”acan gdn duk sun tsaneni ”shiyasa nadawo gdnka nasan kai kana sona koh?

Dariyar manya malam bukar yayi yana cewa yaro yaro ne””””’

Duban Miemie yayi yace kwarai mairo ina sonki sosai”’ tashi mushiga ciki toh””””’

Sashinsu baabaa Laure yanufa da ita” suna shiga ”tahango baabaa Laure zaune tana gyaran shinkafa””, dagudu Miemie taje tashake mata wuya tana cewa ”Allah yakamaki saimun motsa maki jiki yau”’

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button