MURMUSHIN AJALI COMPPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MURMUSHIN AJALI COMPPLETE HAUSA NOVEL

Miemie tace a’ah tashi kishirya mutafi” nan salma tamike dama olready tayi wanka tasaka kaya suka fito”’

Koda suka iso gdn mommansu na ganinta tai dariya tace su Miemie yan’gdn tsoho anzo ganinmu ne yau”’ ta6e baki tayi sannan tace a’ah ni sallamar yah sultan nazo ‘bawai dawowa nayiva naga kinfara dariya””’

Girgiza kai hafsa tayi tace toh naji ”’nan suka gaisheta ‘sannan Miemie tace INA yah sultan yake? Nan hafsa take fada mata sunfita shida abbansu”’

Zama sukai sunata fira”’ Miemie tadubi hafsa tace momma wai yajikin baban Aysha ne? Ajiyar zuciya hafsa tayi tace da sauki za’ace amma kam babu wani canji”’

Miemie tace Allah yabashi lfy”’ wlh inajin tausayin gwaggo sa’a ”hafsa tace to yaza’ayi haka Allah ya kadartoh”

Suna nan suna fira sultan yashigo”’ yana ganin Miemie yace a’ah my sis harkin iso kenan”’dariya tayi tace eh nacika maka alkawari koh? Amsawa yayi da eh ” yace kutaso muje kutayani gyara kayana”

Nan suka mike suka bishi xuwa d’akinsa ”’ nan suka baje suna fira suna tayashi gyara kayan”, Miemie tadubi sultan tace ynxu yah sultan daga gobe shikenan baran sake ganinka va” sai inna kawo maka ziyara koh’?

Cikin dariya yace eh ”tace aiko kamar yadda nai alkawari baran ta6a yarda nacika sati biyu banganka va”

Salma tace tayaya kenan ”wazai rika kaiki? Tab ke miemien nan ma bakida lfy koh”’
Sultan yace wlh koh ”salma tambayeta” wazai rika kawota?

Shiru tayi kamin tace hmm yah sultan kenan ”nafada maka a abinda zanrika xuwa amma inbaka yarda va shikenan””

????????????????????????????
Da daddare duk ana zaune a falo sai fira akeyi kamar barasu kwanta va”’ Mahmud yadubi sultan yace ynxu fah Dana tafi shikenan saidai innaxo ganinka”’ saikuma ta waya”’

Murmushi sultan yayi yace hakane abba shiyasama nakeji kamar karna tafi wlh ‘sbd ko kusa banason nai missing naku”’

Caraf Miemie tace wlh innice kai fasa tafiyar zanyi domin baran ta6a yarda nai missing d’inka va”’

Hafsa tace aigara da Allah yasa bakece va d’in ”domin ko ankaiki bawani abun kirki zaki tsinana va”’

Cikin zun6uro baki tace nifah shiyasa banason zuwa gdn nan ”bansan meyasa va mommah bakyaso na va ‘duk abinda nayi saikin kusheni ”

Mahmud yace rabuda mommanki aini inasonki my daughter”'””

Ana tare
[08/10 8:33 am] Me Kosai✍: ???? ????
???? ????
????????????????????????????
MURMUSHIN AJALI
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????
Written by Aysha Wakili
Mrs ahmed

naki ba irin nasu bane aunty halilos inatayaki murnar kamallah ingantaccen littafinki ‘kyautar Allah”ya fadakar ya wa’azantar yakuma nishad’antar’gaba dai gaba dai”’saimunji ki a sabon nvl d’inki ‘Allah yakara basira da zak’in hannu

dedicated to friend bee kalbi Miemie

Page2⃣4⃣

Washe gari ”karfe takwas da Rabi nasafe bayan sunyi breakfast ,kowa yashirya cikin sutura mekyau” Mahmud yafito yagansu”’ yace inafata duk kun shirya dan ynxu zamu tafi ‘INA sultan d’in?
Miemie tace yana d’aki’

Mahmud yafita xuwa waje”’wayarsa ya fiddo yashiga kiran numbern gwaggo sa’ah ringing biyu tadauka mahmud yace sa’adatu kefah muke jira kizo Dan Allah kiywa yaron nan sallama ”’cikin rawar murya gwaggo sa’ah tace kayi yaya amma baran samu xuwava” kuma ba dole sainazo va ‘idan kasa masa albarka tamkar baban Aysha ne yasa masa” sannan idan hafsa itama tasa masa tamkar nice” danhaka inmuna daku akusa bamuda sauran damuwa”””” mahmud jiki asanyaye yakatse wayar”’

Nan yace sufito sutafi” Dan karfe goma jirgin zaitashi”” nan suka shiga fita da kayan sultan”” bayan sungama kowa yashige motar ‘hafsa ‘miemie’salma’ abaya sultan da mahmud agaba”’

Nan suka kama hanyar airport””’ haka kowa yazauna jungum jungum babu Wanda yai magana”’ harsuka karaso airport d’in ”

Bayan sunfito a mota mommah tadubi sultan tace toh sultan yau zamu rabu ”rabuwa irin wacce saime Nisan kwana zaiga lokacin sake gamuwa”abinda nakeso dakai karike mutuncin addininka duk Inda kake karka manta matsayin addininka”” nasanka sultan kaid’in me tarbiyya ne danhaka baranyi maka doguwar nasiha va”kaje Allah zaikula mana dakai”

Rungumeta sultan yayi yana cewa nagode mommana kece Uwa tagari Allah yasaka maki da dukkan alkhairi”’. Nan yajuya ya rungume mahmud yana abba zanyi kewarka sosai”

Miemie dake gefe idonta yacika da hawaye sai sharewa takeyi ‘gaba dai tajuya masu baya”’ juyawa sultan yayi yaga baiganta kusava”’
Da Sauri yakarasa Inda take ‘kamo hannunta yayi yace ‘kan’wata meke faruwa kike kuka ko duk kewar nawa ne yafara ta6aki””’ fisge hannunta tayi tace dillah cikani ‘kasa ne yashigen ido”’
Dariya yayi ‘yace ohh my lil sis bansanki da k’arya va” nd ko kinyi baya maki kyau”

Kallonshi tayi ido cike da hawaye tace ynxu fah yah sultan kai naga ko ajikinka ma”kamar Allah Allah ma kake katafi koh?

Girgiza mata kai yayi alamar a’ah ‘sannan yace mezaisa ni murna zanrabu da kan’wata kawai banason nasasu abba damuwa ne shiyasa kikaga ina pretending ”

Dariya tayi tace yauwa yah sultan na ”kayarda narik’a xuwa maka duk bayan 2weeks d’in koh? Cikin dariya da rashin yarda da sakarcinta yace nayarda koh bayan 1week ne kizo”’

Dariya tayi ta rungume shi tana cewa yauwa my swt bro I prms u 1st 2weeks darakayi a skull zankawo maka ziyara ”” kama hancinta yayi yana cewa kincika rigima”’kiyimin alkawari baraki rink’a sa mommah surutu va’ sannan zaki cigaba da zama da best a skull kamar yadda kike”’ sannan zakiyi hankali kamin nadawo”’

Dariya tafashe dashi sannan tace nayi maka alkawari baran dinga sa mommah magana va ‘nd I will olways be d best ”bt ba ukun baranyi maka alkawari va sbd kara haukacewa zanyi ””tana gama fadar haka tafisge hannunta zata wuce Ashe haushi taji””’

Binta sultan yayi yajanyo hannunta yace haba lil sis meye na fushi kuma? Harararshi tayi tace ai Kaine kullum kar’inka cemin banda hankali”’ dariya yayi yace toh am sorry me hankali ”

Mtwe toh kadaiyi Sauri domin anfara shiga jirgi kar atafi amanta dakai”’sultan yamike rataye da jakarsa yana cewa aiko yatashi nasan zaki kaini ataki jirgin me saukar angulu”‘””

Ta6e baki tayi sannan tace sainayi niyya” rungumota sultan yayi suka nufo Inda su mahmud suke””” nan yaimasu sallama ”’xuwa yayi akayi checking nashi sannan yawuce xuwa Inda zasu shiga jirgin””

Miemie koh nan take hawayen daba taso suzubo suka fara kwaranya a idanuwanta ”shikenan yau yayanta mesonta yatafi yabarta ‘ynxu ita kadai zatake rayuwa”’

Suna kallon sultan sanda yazo shiga jirgi cikin” begen juna suke d’aga Mashi hannu shima yana d’aga masu””

Minti shabiyar da shigarsu” jirgi yafara shirin tashi”’ cikin share hawaye Miemie tace Allah sarki yah sultan d’ina zanyi kewarka”’

Basu bar wurin va saida sukaga tashin jirgin ”sannan suka juyo sukayi gun motarsu _”””

Acikin jirgi sultan bayan yazauna yad’aura belt ”’bayan sunfara keta hazo’ sultan gaba dai tunanin iyayensa da Miemie ya addabesa”’ jiyake kamar yatsaida jirgin yasauka””

Girgiza kansa yake ‘yana mebawa kansa kwarin guiwa”’ juyawa gefensa yayi domin ganin na kusa dashi””’

Innalillahi wainna ilahiraji’un ”sultan ke furtawa ganin wacce kezaune kusa dashi ”’ cikeda tsoro bakinsa sai rawa yakeyi ” yad’aga d’an yatsarsa yana nunata ” yana mie___mie_____ duk yadda yaso hada harufan sunanta abun ya gagareshi sbd tsananin rudewa da firgici daya shiga”’

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button