LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

????????????????????????????
???? ???? ????
???? ????????????????????????????
LAMARIN KADDARAR AURE NA!!!.

     ????     ????     ????

????????????????????????????

Story and writing
by
????
ZAINAB HABIB
{Mom islam}

WRITER OF✍️????

*ZAINABU ABU*

ZAZZAFAR KISHI
LADIDIN KAUYE
NANCY YAR KARYA
JININ ABBANA!!

AND NOW
LAMARIN AURE NA!!

INA MIK’A GODIYATA GA RABIL IZATI DAYA BANI IKON RUBUTO WANAN LITTAFI

BANYI DAN WANI KO WATA BA DUK WANDA YAJI YAZO DAI _DAI DA LABARINSA TO HASASHE NE , BAN YARDA A JUYAMIN LABARI BA DUK WANDA YAYI MIN HAKA SHIDA ALLAH

MARUBUCIYAR????
ZANABU ABU
ZAZZAFAR KISHI
LADIDIN KAUYE
NANCY YAR KARYA
JININ ABBANA

     *AND NOW????*

LAMARIN K’ADDARAR AURE NA

My fans ya zamo free domin farincikin ku????


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com
https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.

BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM

????️ EPISODE 1& 2

Gidane d'an madai daici , baza'a kira masu gidan da talakawa ba ,amma sunada rufin asiri , d'akuna biyar ne , a cikin gidan , da kitchen da d'akin matar gidan dakuma bayin waje sai d'akin bak'i  daga gefe kuma a cikin d'akin matar gidan d'akin mai gidan ne a ciki ,wato mu had'u a parlor sai toilet a gefe , malale gidan yake da fasasun tails ,gefe ga pampo ,wata matashiyar mata na hango tana fitowa daga d'akinta , fara amma ba sol ba sanye take da doguwar riga ta atamfa mai ruwan ganye da kwaliyar flawoyi a jiki , rigar ta zauna a jikinta sosai , ta fito da asalin kyaun ta dakuma kyan diri na cikinta , hannayenta sanye suke a awar waro wuyanta kuwa wata sark'a ce y'ar k'arama , bakinnan yasha pink d'in jan baki , a k'ala zatayi shekara ashirin da biyar 25yrs , kitchen ta nufa , tukunyar dake kan risho ta sauke ta dawo ta   koma d'akinta , ta fito da jug da food flaks , kitchen ta nufa , bud'e tukunyar da ta sauke yanzu tayi , jollof d'in shinkafa ce yaji salad da carrot da albasa , sai k'amshi take zubawa , bud'e kular tayi ta zuba abincin ta rufe , ruwa ta d'ibo a randa ta zuba a cikin jug d'in , ta maida murfin ta rufe , tirai ta d'auko a kwando mai adon falawoyi a jiki ta jera abincin da cokali da plet da kula a ciki , ta nufi parlorn ta dashi , wani d'an madai daicin tebur ta ajiyeshi , kana ta koma bedroom d'inta , ta zauna a gaban stool tana kallon dressing mirror , k'ara shafawa fuskarta powder tayi tare da k'ara feshe jikinta da humra masu k'amshi ."

Daga kanta tayi ta kalli agogon dake manne a jikin bango , k’arfe tara na dare , mik’ewa tayi ta k’arawa d’akin turaren wuta ta ciro wayarta dake , chaji wata number ta danna cikin sa sanyar murya tace ”amincin Allah ya tabbata a gareka mijina , daga cikin wayar wanda takira yace ”Afnan sarauniyar mata afuwan yau nayi dare ,yanayin aiki ne amma insha Allah ganinan , zuwa mekikeso ?”k’ara rage muryarta tayi tace ”banason komai Allah ya dawo dakai lafiya ,amen yace ”daganan suka kashe wayar , bacci ne yake k’ok’arin surarta tana k’in kwanciya , jiyo bugun k’ofa tasata ficewa da gudu , bud’e k’ofar tayi , tana ganinsa ta rungumesa tana dariyar farinciki , d’agata sama yayi yace ”ammata ba kya girma ko da alamu bakici abinci sosai ba ?” naci Afnan tace tana dariya , rik’o mata hannu yayi sukayi bedroom d’inshi , temaka masa tayi da cire kayan jikinsa ,ta rakashi toilet nanma ta temaka masa yayi wanka , wanan ta zamo al’adarsu tun tana amarya yanzu gashi shekararta biyu ,amma babu wanda zai ce tayi wanan shekarun komai nata kamar na budurwa , tare suke wanka sai dai inbabu mutum d’aya hakama cin abinci tare sukeyi abincin rana ko sbda babu organ nata sai lokacin da tayi ra’ayin cinsa .”

Temaka masa tayi da shafa mai , ta dubo masa kayansa a drowa , wando gajere da farar singlet , gado ya hau zai bud’e laptop d’insa , cikin Maria raicewar murya tafara bubuga k’afa tana cewa uhm uhm my Hubby kazo muje kaci abinci , Hankalinshi ya tafi ga laptop d’in da ya bud’e , yace ”jeki ganinan , no bazan wuce ba harsai ka taso ,mik’ewa yayi tana gaba yana biye da ita , teburin data jera masa abincin sa ta nufa , bayan ya zauna ne , ta zubo masa tare da sa nata cokalin tana bashi a baki , shima hakan yake himata , har sai da suka k’oshi sanan kowa yai brush , Afnan na ganin Haisam zai wuce ,bedroom d’inshi ta rik’o masa hannu cikin shagwa6a tace ”yanzu lokacin bacci ne kadinga hutawa rayuwarka , badan Haisam yaso ba ta dawo suka wuce nata bedroom d’in .”

Washe gari ta tashi da shirin zuwa anguwa , bayan Haisam ya fita tagama komai na gidan da yazame mata farillah , misalin sha biyu na rana ,tajiyo ana bubuga k’ofa , mik’ewa tayi ta je gurin mai buga k’ofar , tana bud’ewa gabanta ya fad’i , mama ce sanye da hijabi , tasan lokacin kukanta yazo , cike da masifa mama , ta shige ciki batare da tayi sallama ba ,Afnan ce ta bi yanta ,a parlor maman ta tsaye tana k’arewa gidan kallo , mtsw taja tsaki ,tafara sababi , ga gida har gida ,amma babu y’a y’a nikam Haisamu ya kwaso mana juya , ta fashe da kuka ,

Afnan data mik’e daga durk’uson da tayi tace ”mama itafa aihuwa rabo ce , kee rufemin baki banason kinibibi , wayasani ma ko kafin auran naku kinje kinsha abinan na hana d’aukar ciki , shiru Afnan tayi ta sunkuyar da kai k’asa , inda sabo ta saba da gorin mama , amma ba’a sabo da wulak’anci , yasata fashewa da kuka mai ban tausayi, kitchen mama ta shiga hango gwan gwanin madara yasata Ciro ledar da ta sak’ale a Mara tasa cikali ta d’ibi madarar ta fito , itadai Afnan ta koma d’akinta .”

Mama na fitowa tayi waje ko rufo k’ofar batayi ba , Afnan ce ta mik’e ta fito waje , wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata , tanata zancen zuci ,ace tunda nayi aure banida kwanciyar hankali uwar miji tasani gaba , akan maganar aihuwa , ta kuma fashewa da kuka , tana cikin haka mak’ociyarta ta shigo suna mutunci sosai sunanta Fatima , mamaki ne ya kamata ganin k’ofar gidan a bud’e , shigowa tayi da sallama tace ”Afnan har yanzu baki shirya bane ,ni gashi harna gama komai , kan Afnan a sunkuye bata d’ago ba , Fatima ce ta rik’o hanunta tare da shigewa da ita d’aki suka zauna , Fatima ce tace ”ko baki gayamin ba nasan mama ta shigo amma dan Allah kiyi hak’uri ki cire wanan surutun nata a zuciyarki , Allah ne me bawa kowa aihuwa kemafa bawai baya sanki bane ya hanaki , kuma ko asibiti da kikaje kince likitar tace ”lokacine beyi ba amma zaki biye mata hankalinki yadinga tashi ?”.

Afnan ce a share hawayenta tace ”Fatima kinfi kowa San in halin da nake ciki kuma kinfi kowa na anguwar nan sanin halin mama , takuma share hawayen da suka sake zubo mata race ”aurena da Haisam yin Allah bana mutum ba ,cikin tausayawa Fatima tace ”nasani amma kirage sawa kanki damuwa , tashi ki shirya muyi mu tafi , cikin fushi Afnan tace ”Fatima bazan iya zuwa ba wlh kwai kije zanje wata rana , babu rarrashin da Fatima batayiwa Afnan ba ‘amma furr tak’i , haka Fatima ta wuce gida zuciyarta babu dad’i ko kad’an, bedroom d’inta ta koma ta kifa kanta akan fillo tana kuka , tana cewa ya Allah ka kawomin aihuwa cikin satinan Allah ka duba irin gorin da nakesha a gurin dangin mijina .”

Tana cikin kuka taji wayarta tana ring dubs mai kiran tayi , ganin my husband ,yasata dai daita muryata ,tace ”amincin Allah ya tabbata a gareka mijina ya aikin , dafatan babu wata matsala ko ?”dariya Haisam yayi yace ”wato ni zaki yiwa wayo ko ?”waya saminke kuka ? dariyar yak’e tayi kamar yana ganinta tace ”ba kuka nakeyi ba, kwai kai na ke ciwo , hmm Haisam yace ”badan ya yarda ba yace ”to ki kularmin da kanki , daganan sukayi sallama jiki a sanyaye , sallama taji na muryoyi da dama tasan ko suwaye , hakan yasata mik’ewa ta fito parlor su biyu ne y’ammata ,da Khadija da Aisha , taunar cingom sukeyi cikin isa da wulak’anci , Afnan ce ta k’araso da fara’arta tace ”ah sanunku da zuwa , ko kallo bata ishesu ba bare tasa ran zasu amsa mata , neman guri tayi ta zauna a gefen kujera , Khadija mai shekara goma sha biyar ta mik’e tana yarfe hannu tayi kitchen , Afnan ce ta taso cikin zafin rai tace ”gaskiya yau bazan yarda ba ,kunason wulak’anta min gida , Aisha ce ta mik’e tare da gallawa Afnan harara tace ”gidan yayan mu ne dole muyi abinda ranmu yakeso .”

Zuciya ce ta d’ibi Afnan ta wankawa Aisha mari ,da gudu Khadija ta shigo jin k’arar kukan Aishe ta cakumi wuyan Afnan , Afnan ce ta kaimata mari , dayake k’arfi ba d’aya ba , Afnan ta nad’a musu duka , girkin da basuyi ba kenan suka , wuce gida rai a 6ace , zama Afnan tayi tana girgiza k’afa , tana jiran abinda zai biyo baya, indomie ta dafa dan yunwa ce ta addabeta , tana gama dafawa ta kwashe a plet ta fito kenan ta jiyo tafiyar da bata tunanin ta kowace face ta mama , mama na shigowa ta ka6ar da abincin kana ta murjeshi a k’asa , bala’i tafara yo gidan ubanki ne kokuwa , dan sunzo ziyara gidan yayansu shine zakiyi musu duka , matsiyaciya juya kawai , Afnan ce ta dubi mama ido cike da hawaye tace ”mama menayi dahar kike jifana da wanan mugun kalamin ?”marine ya biyo bayan k’arshen maganar ta , juyawa mama tayi tana dura mata zagi.”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button