Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NAFEESAT RETURN COMPLETE HAUSA NOVEL

Ad

_____

[5/21, 9:53 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
FAMILY DOCTORS
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
NAFEESAT RETURN
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL

SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝🏻‍

بسم الله الرحمن الرحيم

PERFECT WRITER’S ASSOCIATION🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

      *P.W.A✍️*

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattpad: UmmuDahirah👈

Thanks be May God bless everyone, peace and blessings be upon our leader Prophet Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, may God bless you and grant me the ability to write this book, may God grant me the ability to write what will benefit the nation ameen.

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY.

LITTAFAN MARUBUCIYAR
NAFEESAT.
BARRISTER IBRAHIM KHALIL.
LABARIN DEEBIZAH.
MALAMA LADI.
JARUMAI
LUBABATU (ƴar ƙwallon ƙafa).

EPISODE One

  Doctor '' Al'ameen Abubakar Khabeer Cindo ''and his wife ''Prof. Nafeesa (Baby) Isma'il Audu, '' as you know in the story of *NAFEESAT* They live in Kaduna, and they still live in the city, owned by their five children.  *1_ DOCTOR NOOR (LAWAL AL'AMEEN ~YARON UMMEE NAFEESA~)* Wanda a yanzu ake kiran sa Big Dady, matar sa ɗaya *Hajiya Asiya (Hajiya) ƴa ga Muhsina,* yaran su uku, Doctor Usman, sai Doctor Zainab ~yanzu haka tayi aure,~ sai kuma Yusra.

2_ HAJIYA RABI’ATU AL’AMEEN (IKRAM) ~WANDA A YANZU TANA AURE A GARIN KATSINA~ tana zaune da iyalan ta acan.

3_ DOCTOR ABUBAKAR AL’AMEEN ~WANDA YANZU AKE KIRAN SA DA ABBA~ matar sa ɗaya Doctor Fatima (Hajja Fatu) ~ƴa ga Abokin Doc. Al’ameen wato Haidar da ƙanwar sa Ihsan,~ yaran su Biyu, Doctor Al’ameen (Baffa), sai ƙanwar sa Shakira.

4_ DOCTOR AL’AMEEN AL’AMEEN (ABBU) Matan sa biyu, ~Bilkisu (Umma) ƴa ga Baseera,~ yaran ta uku Doctor Zulaiha ~tayi aure,~ sai Fadila da autan su Fadil. Sai matar sa ta biyu A’ISHA (AUNTY AMARYA) yarinyan ta ɗaya ”’NAFEESAT”’ suna kiran ta da Ɗahira.

5_ HAJIYA LAILA AL’AMEEN yanzu haka tana aure a Kano, ta auri babban Yaron WALID. Suna zaune da iyalan su can.

  Waɗannan familyn yanzu haka suna zaune ne a gida ɗaya kowa da part ɗin shi, sai dai akwai Babban parlour'n da ya haɗa su, yanzu haka Doc. Al'ameen Wanda a yanzu suke kiran sa da *KAKA* ya kai shekaru 89years. Tuni ya ajiye aikin sa sakamakon yana fama da ciwon ƙafa wanda a halin yanzu yana zaune ne a wheel chair, matar sa Prof. Nafeesa (Baby) Shekaru uku kenan da Allah ya amshi abin sa.

Za kuyi mamaki idan nace muku duk ka familyn Doc. Al’ameen gaba ɗayan su DOCTORS ne, wannan shine burin sa kuma Allah ya cika masa.

  Babban asibitin da ya gina ya ƙara haɓɓaka shi wanda a halin yanzu Five Block ne, kuma sosai asibitin me suna *(AL'AMEEN FAMILY HOSPITAL)* tayi fice a ƙasar Nigeria, gaba ɗaya familyn suna aiki ne a Hospital ɗin.

Yanzu haka a halin yanzu an shirya yin babban Walima don taya Doc. Ɗahira(Nafeesa) Al’ameen Al’ameen, Doc. Shakira Abubakar Al’ameen, Doc. Yusra Noor Al’ameen, da Doc. Fadila Al’ameen Al’ameen. Murnan kammala karatun su na likitanci, wanda za su soma aiki ne a ranan da a kayi musu waliman tare da sabbin ma’aikata da za’a ɗiba a ranan.

KU BIYO NI DON JIN LABARIN WAƊANNAN FAMILYN

   Zaune suke su Huɗu a Babban katafaren parlour'n gidan da ya'amsa sunan sa a haɗuwa da ƙayatarwa, da shigowan ka parlour'n Babban Hoton Prof. Nafeesa (Baby) zaka soma cin karo dashi, wanda tayi sa ne lokacin da ta zama Professor, tana sanye da baƙar abaya me tsananin kyawu da burgewa, wanda duk da kasancewar ta baƙa ba ƙaramin kyau yayi mata ba, sai tayane kanta da Milk Colour ɗin Veil, kyakykyawar fuskarta yalwace take da murmushin da ya ƙara fito da tsantsan kyawun ta tare da Dimpul ɗin ta, a tsaye take ta riƙe ƙugu da hannu biyu tare da ɗan ɗage kanta, da alamun sanda akayi hoton bata san ma za'a yi sa ba. kusa da hoton kuma wani tanƙamemen hoton ne da a cikin sa Al'ameen ne tare da ita Babyn, suna zaune manne da juna sun saka ankon shadda me ruwan powder, gefe da gefen su kuma Noor ne tare da Ikram jingine da jikin su, duk kan su dariya suke yi time ɗin da aka ɗauki hoton, sai gefe kuma sauran hotunan ƴan gidan ne kowa da iyalan sa, sannan sai aka ɗau guda ɗaya wanda su kayi gaba ɗaya familyn, shi wannan ba'a daɗe da yin sa ba, don gab da rasuwan Prof. Baby akayi sa, gaba ɗaya idan ka kalle su sosai suke kamanceceniya da juna, sai dai banbancin launi da ya raba su. 

Doc. Al’ameen wato KAKA tare da yaran sa maza su uku zaune cikin parlour’n suna tattauna yanda za su gudanar da Waliman yaran su kamar yanda suka saba a duk sanda yaran gidan suka gama karatun su na likitanci.

“Kai takwara yaushe matarka zasu dawo ne? Kasan jibi ne walima, ya kamata su dawo don itama Matata (yana nufin Ɗahira kenan) ta sami damar shiryawa yanda Ya kamata”. Kaka dake zaune saman wheel chair yake wannan maganan

ABBU yace, “insha Allahu Dady zasu dawo zan sake tuntuɓan su inji, sabida mahaifin A’isha (matar sa Aunty Amarya) jikin ta yayi tsanani ne shiyasaka suka jin kirta”.

Kaka yace, “to shikenan Allah ya dawo da su lafiya”.

Gaba ɗaya suka amsa da “ameeen”.

Sannan ya kalli Big Dady yace, “Kai kuma da yaushe ne Usman yace “zai dawo?”

Big Dady yace, “Allah ya taimaki Dadyna! na yi masa magana amma yace “in ba ka haƙuri ba zai samu daman zuwa ba sabida aiki sun yi masa yawa”.

Cikin nuna alamun fushi Kaka yace, “wai yaushe Usman yabzama me taurin kai ne? Ko don yana tunanin na ba shi dama ya zauna acan yayi aiki shine yake son ɓata min rai? To, ka gaggauta kiran sa ka faɗa masa umarni nake ba sa; dole ne ya zo wannan taron Waliman da za’a yi, ko me yake yi ya’ajiye sa ya halarci taron nan”.

Gaba ɗayan su su kace “Allah ya huci zuciyar ka Baba”.

“Insha Allahu zan sanar masa Dady kuma zai zo”. Cewar Big Dady kenan

Gyaɗa kansa Kaka yayi kana yace, “za ku iya tafiya na sallame ku, Allah yayi muku Albarka”.

Gaba ɗayan su suka amsa da “ameen” kana suka tashi suka fice.

Shi kuma Kaka janyo Remote yayi ya sauya tasha zuwa African t.v yana sauraron wa’azi

Da sallama Fadil ya shigo parlour’n, wanda ya kasance shine ƙaramin gidan don shekarun sa baza su wuce 14yrs ba. zama yayi kan kujeran da ke kusa da na Kaka ya saka hannu ya ja gemun Kakan da ya kasance fari fat, yana dariya yace, “Kakus kana hutawa ne?”

Kaka bige hannun sa yayi yana faɗin, “Ƙaniyar ka Fadil, kai ma ka koyi jan min gemun ne yanda Matata take min?”

Dariya ya tuntsire da shi yace, “to ai hakan ya fi dace wa da kai Kakus, don me baza ka aske gemun ba ka bar abu sai faman lilo yake yi, wlh watarana kana barci zan silalo in cire maka kowa ya huta”.

Dariya shima Kakan yayi yace, “lallai ka raina ni da yawa amma ina da me maganin ka, ka jira ya dawo zan faɗa masa duk abinda kake min”.

Zumbur Fadil ya miƙe yana waro ido waje yace, “afwan Kakus kaima ka san ba mu haka da kai, wlh yau ne kawai nace bari in ɗana Amma baran sake ba, Kar kasanar masa don Allah kaji Kaka na”. Yaƙarike maganar nasa yana me marairaice fuska kamar zai yi kuka

“Shaƙiyin yaro ashe kana da tsoro har haka?”

Waro idanu Fadil ɗin ya sake yi yace, “iyyee Kaka taya bazan ji tsoro ba bayan kana son ka haɗa ni da Zakin gidan mu? Ni dai ka ga tafiya na don tunda ka’ambato shi bazan iya zama anan ba”. Yana ƙarisa maganar ya ruga aguje yabi hanyar part ɗin su

Da dariya Kaka yabraka shi, kana ya girgiza kan sa aran sa yana cewa, “lallai Usman ka koya ma yaran gidan nan tsoron ka, ba ka a cikin gidan ma shekara da shekaru amma har yanzu tsoron ka be bar cikin ran su ba”.

Ci gaba da kallon sa yayi, sai can kuma ya ɗago kansa yana kallon hoton matar sa Baby, Wanda take ita kaɗai ɗin, murmushi da hawaye ne a haɗe suka taho mishi tunawa da rayuwan su, kullum ranan duniya sai ya zub da hawaye a kan ta, coz Ko wacce rana sai ya kalli hoton ta sama da ashirin, kuma aduk sanda zai kalla ko yayi kuka ko yayi dariya sabida abinda zai tuna na game da rayuwan su a wannan lokacin, gaba ɗaya ɗakin sa idan ka shiga hotunan ta ne birjik, da sanda take tashen ta da sanda ta tsufa, har ta bakin gadon sa inda yake saka kansa akwai hoton ta da ya’ajiye a wajen, mutuwan ta ya bala’in girgiza sa wanda yayi kamar bazai rayu ba, sai daƙyar ya dawo hayyacin sa bayan dogon jinyan da yayi, har yanzu har gobe soyayyar ta tana nan daram a zuciyar sa, domin kamar ƙaddara ne da Allah ya saka masa na tsananin ƙaunarta, kullum fatan sa ace ga ranan da zai bi ta, shima ya koma ga mahaliccin sa kamar yanda ta tafi ta bar sa..

Dafa kafaɗun sa da akayi shi ya dawo dashi hayyacin sa, Yusra ce tsaye kansa tana kallon sa, idan da sabo yaci ace sun saba da ganin Kakan nasu cikin wannan halin, kuma sun san da cewa ba komi yake saka sa a halin nan ba illa tuna Kakar su.

“Kaka har yanzu dai ka ƙi ka dena tuna wannan tsohuwar matar taka, har yaushe ne zaka cire ta arai ne kayi rayuwan ka cikin kwanciyar hankali? Mu nan mun ishe ka rayuwa ba sai ka tuna ta ba, me ake yi da tsohon Zuma bayan ga sabbin zuma? Don Allah ka dena ɓata time ɗin ka a kan ta”.

Hannu ya saka ya share hawayen yana murmushi yace, “Yusra kenan baza ki taɓa gane wa ba, amma kowa ya san da cewa tsohon zuma shi ne wanda ke magani, sannan ba’a iya manta shi ko wani hali mutum ya shiga, Ni Matata ta fiye min ku duk kan ku, idan da za’a bani zaɓi daku da ita in zaɓa, ita zan zaɓa in bar ku”.

Taɓe baki Yusra tayi tace, “to don baka zaɓe mu ba sai me Kaka? Our parents will vote for us because they love us.”

Kaka yace, “to naji ban ce kiyi min rashin kunya ba, said me to my room”.

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button