MURMUSHIN AJALI COMPPLETE HAUSA NOVEL

Shiru Miemie tayi tana sauraron momman su”’
Sultan yace kyaleta momma Alan yashiryeta”,
????????????????????????????????
Bayan sati biyu”’ sultan kwance a dakinsa’ransa gaba dai abace yake sbd rashin kunyar da Miemie taimasa”’
Yarasa meke damunta gaba dai tasanja ”’kamar ba ita ba”’
Yana nan kwance har barci yadauke shi”
Cikin barcin ne yayi wani mummunar mafarki” wai gashi shida Miemie suna tafiya suna fira ”yana rike da hannunta”
Sunyi nisa cikin tafiya sai jiyayi Miemie tafisge hannunta acikin nasa” tajuya da baya tana tafiya’ cikin Sauri yasha gabanta yana tambayarta inazata amma bata amsa shi va’
Haka tacigaba da tafiya shikuma yana binta ” saida takai wani bakin katon rami sannan tajuyo tana kallonshi tana wani irin dariya””
Idanunta sun sauya launi zuwa green ‘ hannuwanta duk biyu tadaga sama zata fada cikin ramin sai sultan ya kwalla wani irin kara yana kiran sunanta’ ”
Amma bata juyova” dagudu yatashi zaibita cikin ramin datake shirin afkawa ”yana kokawar janyo hannunta ne’
Yaga wani saurayi kusa da’ita yarike mata hannu”’ cikin firgici sultan yafara kiran sunanta Miemie Miemie””
Amma bata juyova da karfin sa yasa hannu yanajan kafarta amma ena wannan saurayin yariga yajata xuwa cikin wannan katon ramin””
Afirgice sultan yafalka daga barcin’yana salati ga uban gumi daya’ hada”
Dagudu yamike yafita xuwa dakin Miemie baiganta va” yafito da Sauri xuwa falo” nan yahangota xaune ita da baabaa laure suna fira”’
Ajiyar xuciya yasaki” sannan yajuya Yakoma cikin dakinsa,,,
Miemie tashi ki daukon baga’dadin nan nai tilawar karatun da sultan ya koyamin cewar baabaa Laure kenan”’
Miemie data mike kafafunta ko kallon baabaa Lauren bataiva”balle tasa ran zata tashi”’
Hannu baabaa Laure tadaga tadaka mata duka abaya”’ gantsarewa Miemie tayi”’
Sannan tadubi baabaa Laure tace kika dokeni?
Baabaa laure tace andoka din yar’banza ina magana dake amma kinwani shareni saikace ni’din sa’arki CE”’
Cikin yatsina fuska Miemie tace oho duk kiyi kigama nan da gobe wlh baki kara kwana gdn nan”
Baabaa Laure tace toh sannu malam bukar me tsaran yadda zanyi ”’
Dariya Miemie tayi tace ke kika San wani bukar’amma ni nafi malam bukar din’da kike magana akai”’
Kuma dole kibar gdn nan da karfin bala’e”’,
Harara baabaa laure tasakar mata sannan tace toh naji uwata ””’
Miemie tace oho dai nafada making tun muna shaida juna ki tattara komatsanki kibar mana gd’
Cikin isa baabaa Laure tace ‘ubanki ne ai komatsan bani va”’
Harararta Miemie tayi tace Allah baabaa kinacin bashi awurina dayawa amma akwai ranar dazaki biya”
Baabaa laure tace toh bashin uwar was naci maki dazan biya”’
Dariya Miemie tayi tace zakiy bayani idan aka fara motsa maki jiki ””
Cikeda jin haushi baabaa laure tace ke zanci maki mutunci fah”’,shegiya mai siffar kwakwa””
Tashi Miemie tayi tana cewa wlh baabaa ina tausaya maki”’
????????????????washe gari da safe ”’ ana dining anayin break fast”’
Baabaa laure tadubi alh tace mahmuda”,yadago kai yana cewa na’am baabaa”
Tai gyaran murya tace Mahmuda sonake kaimin iyaka da wannan yar’banzar diyar taka’ mekama da ,,,,,,,,,,,,,,,,,batakai ga karasawa ba taji kif abakinta””
Da Sauri tasa hannu tana shafa bakin””mahmuda yace baabaa inajinki”’
Nan tasake yunkurin yin magana”’ tace sonake kaimata kashedi akan,,,,,,,,,,,,,,,,…,,,,nan ma tasakejin kif’ anbuge bakin”’
Still bata saduda ba tasake bude baki zatai magana taji anbige mata ha6a har hakorinta na haduwa da harshenta””
Cikin radadi da azaba tasake kokawar bude bakin””
[08/10 8:33 am] Me Kosai✍: ???? ????
???? ????
???????????????????????????? MURMUSHIN AJALI
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????
Written by Aysha Wakili
Mrs ahmed
♻ EXCLUSIVE WRITER’S FORUM♻
E.W.F
my Phauxy ammani inaji dake wollah ‘Allah yabarmu tare
fan’s kutayani da addu’ah inada damuwa” kuma zai Iya shafar kowani 6angare na rayuwata pls ur prayer’s means a lot ‘do not hesitate to put Aysha Wakili in ur daily prys
”’
dedicated to friend bee kalbi Miemie
Page1⃣1⃣
Yace ina ledar awarar? Cikin jin haushi tace toh ina ruwana ‘ka kar6e Abu da kanka sannan kana wani tambayata’
Cikin faduwar gaba sultan yace ‘waima tukun ubanwa yabaki awarar?
Make kafada tayi tace oho nima bansani va”
Hannunta Yakama yana cewa zomu tafi gd anfasa kallon namun dajin”’
Cikeda haushi Miemie tace kar a kalla din’ saime’,bai bi takanta va ‘yaja hannunta suka fara tafiya””
Harsuka karaso gate din gdnsu babu Wanda yai magana”’ sultan yadubi Miemie yace ‘waike fushin mekikeyi ne? Ko duk akan awarar Dana yar’ne ?
Hararashi tayi tace bansani va’ Allah saika biya ”tana gama furta haka tafisge hannunta tai cikin gd’ binta yaida kallo ”
Tana Shiga bata iske kowa a falon va’ danhaka tawuce dakinsu””
Samun baabaa Laure tayi kishingide tana gyangyadi””’ dariyar mugunta tayi” sannan takoma da baya ta tsaya a dokin kofar”
Cikin wata irin firgitacciyar murya tafara cewa”’ yauwa gwara da Allah yakawo mu yau dole mu motsawa tsohuwar nan jiki domin ga dukkan alamu tsufa yafara kawo mata hari dole mu Kore wannan tsufar””
Ahaukace baabaa Laure tabude idonta tana ihu cewa take wlh kubarni da tsufa na’ basai kun motsa min jiki va”’,dan annabi kui hkr ‘kuke ganinmu bamu ke ganinku ba ya’ku mutanin 6oye””””
Ihuu taji ansaki mata sannan aka kyalkyace a dariya”’ akace yau’dai dole ki motsa jikinki domin bamuson tsufah Yakama ki”””’ cikin karkarwa baabaa Laure tace wlh amotse jikin yake basai nakara motsawa va”
Dariya aka kece dashi akace idan har kinaso mu kyaleki dole musaka maki kida kiy rawa’inko kin ki amincewa toh tabbas zamu motsa maki jiki”’
Da Sauri baabaa Laure tace yasin kome kukace zanyi amma dai kar amotsan jiki”””
Miemie najin haka taja da baya ”ta isa ga socket dake jikin bango takunna”
Nan kida yafara tashi”’ aiko baabaa Laure tazage tafara tikar rawa”miemie nabude labulen tahangota ‘aiko mezatai inba dariya va””
Harkasa takwanta tana kyalkyacewa da dariya” sultan daya shigo yahango ta kwance akas tana birgima ”’da Sauri yakaraso gareta atunaninsa wani abunne yasami miemien ”’
Saidai ga mamakinsa saiyaga dariya kawai ta tike tanayi”tana daga labulen dakin”’
Ahankali yadaga labulen shima”baki bude yarike ha6a yana kallon baabaa Laure data tike sai tikar rawa takeyi ‘and ga dukkan alamu rawar bana dadi bane’ sbd gabadai gumi yarufe mata fuska ”batamasan yashigo va”’
Da Sauri yafita yakashe socket din” sannan yadawo dakin” jiyayi baabaa Laure nacewa ”’na tsaya kodai naci gaba”miemie kuma ta nutsu azaune tana cewa ”kici gaba ko mutaimaka maki ne?
Cikin azaba baabaa Laure tace a’ah Allah yabaku hkr basai kun taimaka min va ‘zanyi
Da hanzari sultan yace baabaa Laure wai mekikeyi hakane?
Juyowa tayi da idanunta dasukai jazur ‘tace kaii sultan kake kowa’ karufawa kanka asiri kafita karka gogamin wata bala’en”
Sultan yace bala’en me? Cikin alamun nagajiya da tambaya tace nakome ma”’
Tsinkayo muryar Miemie sukayi tana cewa ke baabaa zaki cigaba ne kodai saina motsaki ””
Wayyo wlh zancigaba sultan dan annabi katafi ‘wlh ganinka anan zai iya samin damuwa””