MURMUSHIN AJALI COMPPLETE HAUSA NOVEL

Far tai da ido sannan tace jirgi me tashin angulu”” ysaki sultan yayi yace haukar taki ta motsa shiyasa muntari ya zarge maki jiki ai””’ 6ata rai tayi tace wannan kuma tsautsayi ne yahau kanshi shiyasa yata6a jikina ‘kuma saiya gane kuskurensa”’
Shiru sultan yayi ”kamin yasake kallonta ‘yace Miemie ni kina bani tsoro wasu lokutan sannan saina rik’a gani kamar ba mommace tahaifeki va wlh::::gaba dai abirkice kike ‘meye dalili’?
Dariya tayi tace kai yah sultan nidai wlh karka 6atan rai tashi katafi sainzo goben”’
Tana gama fadar haka tamike dagudu tashige cikin gdn”’ a soro sukai karo da muntari ‘tsawa yadaka mata yace waike mahaukaciyar INA CE? Baki dai bakida nutsuwa ”’ ni mamaki ma nakeyi da kika fito a zuri’ar tsoho wlh””’
Kanta akas tanajin bak’ak’en furucin da muntari yakeyi””cikin tsananin 6acin rai tadago idanunta da baki daya sunjuye kala zuwa bak’i babu ko d’igon fari aciki ‘tadubi muntari tace kai me kararren kwana ne ”nan take wani dogon hannu yafito ajikinta yanufi saitin wuyan muntari””
Yana dago kansa da niyyar yin magana yaga hannun na nufosa cikin in ina ”yajuya zaigudu ”’ wani irin shaka hannun yaimasa ba shiri yadawo da baya”’
Idonsa sun kad’a sunyi jazur ”gasu sun kwalalo kamar zasu fad’o””
Manneshi da jikin bango tayi tana juya cikin kwayar idonta tana murmushi”::: cikin wata irin halitta tabude baki zatayi magana saiga wasu Zara zaran hakora sun bayyana a bakinta ”’,shikam muntari sumewa yayi sbd tsananin rudu daya Shiga’ gawani irin matsa dayasha””
Kusan minti biyar suna nan ahaka ”kamin tafara sauyawa tana dawowa Miemie ta asali”” saidai tana saukeshi kasa wani haske me kama da walkiya yafito ta cikin idonta yashige jikin muntari””
Timm kakeji tasako shi a kasa ””’nan tajuya kamar ba ita va tashige cikin gdn””
Tana shiga gdn sashin baabaa laure tanufa tana shiga ta tadda babu kowa a tsakar gdn danhaka taishigewarta daki takwanta”’
Can cikin barcin dabai Dade da daukarta va ”’taji ana rafka salati ” a sittin tamike tafito tsakar gdn domin taji meke faruwa” jitayi baabaa asabe na salati sauran mutani suna tayata amsawa”’.
Innalillahi wainna ilaihirajiun””’
Kuyi hkr da wannan bayawa
Ana tare????
[08/10 8:33 am] Me Kosai✍: ???? ????
???? ????
????????????????????????????
MURMUSHIN AJALI
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????
Written by Aysha Wakili
Mrs ahmed
dedicated to friend bee kalbi Miemie
Page2⃣3⃣
Tsaki tayi takoma d’akin taci gaba da kwanciyarta”” saidai jin salatin da akeyi yaki saurarawa yasa tamike tanufi soron””
Su baabaa asabe tagani tsaye sunyi cirko cirko ”ga tsoho nan ma shima tsaye sauran yan’uwa duk ansaka muntari a tsakiya ‘masu yimasa firfita yi sukeyi da masu yimasa salati aka duk sunayi””
Kutsawa tayi cikinsu ”’ganinshi tayi kwance kamar gawa”juyowa tayi tadubi baabaa Laure tace baabaa waime yasame shi ne?
Cikin tashin hankali baabaa Laure tace wlh bamu saniva ”kinga dawowarmu kenan muka gansa kwance anan kamar gawa”’ zaro ido Miemie tayi tace toh Ku kaishi asibiti mana”’baabaa asabe tace ke dillah rufe mana baki”’ bagashi yafara farfadowa va””’ tsaki Miemie tayi tajuya taicikin gdn tana cewa aisai kiyi””
Tana shiga gdn tadauko wani Kofi babu kome acikinsa ‘tanufo soron saidai ga mamakina kamin takaraso cikin soron saiga ruwa cike a’kofin”,tana xuwa tasake kutsa kanta ciki tadaga kofin ruwan tana zubawa a fuskar muntari ”’tana gama xubawa baabaa asabe na buge mata hannu tana cewa ke banson iskanci wani irin izgilanci ne wannan””’
Ko kallonta Miemie batayi va ‘tajuya zata wuce kenan sai muntari yamike yazauna”’ duk mutanin wurin akasa ihu yehh yatashi””,da hanzari baabaa asabe tajuyo taga dagaske ne Kodai karyane ganin da gaske ne yasata” riko hannun Miemie da Sauri tana cewa ke’ruwan mekika zuba masa ne” naga duk anzuba masa ruwa amma bai farfado va ”keko daga zuba masaya farfado”’
Harararta Miemie tayi tace irin ruwan da kuka zuba masa ”saidai Ku Baku zuba masa yadda zai farfado va shiyasa”” tana gama furta hakan ta fisge hannunta tai tafiyarta”””
Koda muntari yabude ido kallon mutani yakamayi kamar wani bak’onsu ””can yana cikin raba idon ne yahango salma yar’gurin jibirin yaron baabaa Laure”’ tana tsaye tana kallonsa ”aiko yana mikewa yanufi gurinta ”’ hannunsa yasa yacafko ta da karfi tafada jikinsa ”nan yashiga shashshafata yana sunsunata saikace bunsuru””’ kokarinsa kawai yasamo bakinta yahade danashi””’
Yarinya nan tashiga ihu tana Neman taimako ”’kowa yarude ”nan aka shiga kokawar kwatoh salma ”’Wanda dakyar aka samu aka 6an6arota jikin muntari”’ Wanda yazage yana matsa mata kirji ”” ana kwaceta yana kokawar binta ”’nan aka rirrikeshi ”mazan wurin suka daukeshi zuwa gdnsu ””’
Itako salma ba abinda takeyi banda kuka ‘sbd tunda uwarta tahaifeta ba’a ta6a yimata hakava””’ baki daya jikinta yayi mata wani iri”’ jitake kamar zata mutu”””
Kowa yashigo gd da mamakin muntari ”ansan dai muntari bashida mutunci amma basusan rashin mutuncin nasa harya kai hakava”’ dazai nemi yayi lalata da kan’warsa agaban uban kowa ”
Miemie zaune tsakar gd baabaa Laure tashigo rikeda salma sai faman masifa takeyi tana cewa kagamin lallatacce yaro ”zai lalata yar’mutani agaban iyayenta da kakanninta ”lallai muntari rashin mutuncin nasama yakai intaha”’
Miemie kam kallonta takeyi batace komeva” salma taxo tazauna kusa da ita ”tana kuka mecin rai”’ kallonta Miemie tayi tace kiyi hkr kinji”’ kibarshi da Allah”’ nima d’azun duka yaimin kamar wani ubana”’
Salma tace ainaki da sauki ”’nasan ni da anbarshi lalatamin rayuwa zaiyi””’ Allah saiya sakamin””’
Ranar haka ahalin tsoho suka kwana babu sukuni”kowa abinda muntari yayi mamaki yake bashi”’ koda mahaifinsa sale yadawo aka fada masa karyatawa yayi”’ saida baabaa asabe tafada masa da bakinta sannan ya yarda”’
Xuwa yayi daki yasamu muntari kwance ”idonsa na kallon silin ‘yakira sunansa ‘ya amsa”’ yace wato muntari rashin mutuncin naka haryakai zakaiwa yar’uwarka fyade agaban kowa? Kai wato kar gagari kowa koh?
Toh tunkan raina ya6aci dakai inaso ka kama kanka inko bahaka va ‘xaka fuskanci hukunci na”’
Cikin hawaye muntari yace wlh baba nibansan sanda hakan tafaru ba ”iyaka nabude ido na ganni rirrike ahannun su kawu ado suntaho dani gd amma ni bansan meke faruwa va”
Cikin takaici sale yace dakayi nasarar yimata fyade Aida zaka sani ”’nadai fada maka ka kama kanka”’
gareku iyaye yakamata aduk lokacin da ya’yanku sukai wani Abu ‘Idan kunyi bincike ‘kunji ta bakin yaro ‘toh yanada kyau kuyiwa maganarsa kyakkyawan fahimta’musamman idan kukayi la’akari da muntari shida rashin mutunci ya iya”amma ba’ata6a samunsa da hali makamancin wannan va”’ sannan yafadawa mahaifinsa ‘shibaisan yadda akai hakan yakasance va” yakamata atsaya a tsnanta bincike akan ya’ya musamman idan wani sabon hali ya bayyana ga ya’yanku
Washe gari da safe Miemie ta shirya tsaf kamar yadda tayiwa yah sultan alkawari zatazo” danhaka taceda baabaa laure zataje gdnsu ta sallami yah sultan saigobe zata dawo”’
Salma dake kwance tace Miemie tajira tarakata”’ Miemie tace dah dai kinhuta abinki karna wahal dake”’ salma tace saidai inbaki son rakiyar ””