MURMUSHIN AJALI COMPPLETE HAUSA NOVEL

Awaje su baabaa asabe sunyi ta jiran baabaa laure amma shiru basu ganta ganin har karfe tara da rabi yayi yasa baabaa asabe tace sutafi idan baabaa lauren tafito tabiyo su’
Haka baabaa laure takaraci mitarta amma babu cigaba ‘harta fara gyangyadi,miemie nabude ido taga sai gyangyadi baabaa laure keyi danhaka tai dariya tasa hannu tahankad’ata kan gadon :’
Bayan shigowar mahmud da abokansa guda biyu dasuka rakoshi d’akin amarya ‘sun sayi baki sannan sukayi addu’ar samun zaman lfy da zuri’a day’yiba daga nan suka tafi ‘ nan mahmud yakirawo hafsa tazo ,bayan taimasa sannu da dawowa ‘dubanta yayi yace toh hafsa ga yar’uwarki nan dan allah ina rok’on ki dakui zaman lfy banda tada tarzoma da husuma duk da dai nasan ba halinki bane amma kuma banida tabbas akan ko kin sanja sabon hali,
Shiru hafsa tayi tana ssuraren shi waisaikace ba mahmud ba wanda ko bak’ar magana adaha bata ta6a shiga tsakaninsu ba amma gashi ynxu ya takarkare yana gaya mata magana,
Ganin hafsa batace komeva yasa shi cewa toh kitashi kitafi saida safe, ba musu hafsa tamike zata fita ,amaryar ko ganin hafsan xata fita tai caraf tace inada magana hafsa bata juyova illa tsayawa datayi tana sauraren mezatace,
Nan tafara cewa ni inada doka dazansa maki duk ranar girkina ko sannu banyarda yahadaki da mijina ba sannan ban lamunci kishiga kitchen ba sai abinda nakawo nabaki zakiy amfani dashi keda ya’yanki inafata kina fahimta?
Murmushi hafsa tayi sannan tace naji amma tunda ba zamanki nakeyi va wannan dokar taki bazatayi aiki ba harsai wanda nake zaman shi ya aminta da haka’
Kallon mahmud baraka tayi taiwani far da ido nan take mahmud ya daburce yashiga cewa kinga hafsa zaman lfy yafi kome ki amince da abinda tace kawai sbd ni duk abinda baraka tafada daidai ne agareni’
Da mamaki hafsa tadubeshi tace haka kace shikenan tai ficewarta,
Nan suka zauna shida amaryar sa ,yabude kazar dayaxo daita suka fara ci cikin nishadi irin na sabbin ma’aurata,
Bayan kome ya kammala ne suka wuce suka kwanta batare da sun gabatar da sallar da annabi yakoyar da kowasu ma’aurata dayiva ‘nan suka shige duniyar ma’aurata ,mahmud jin kansa yake kamar yana duniyar sama sbd wani irin yanayin dad’i daya shiga jiyake duk duniya babu macen datakai baraka niema da dad’i
”
Basu bar junava sai wuraren karfe biyu ‘shidinma sbd barakan ne data fara nuna alamun gajiya tafara yimai kukan shagwa6a badan yasova ya kyaleta”
Yana sauka yashige bayi Yayi tsarki sannan yafito yaja bargo ya kwanta cikin minti biyar bacci yadauke shi baraka da dama tunda yabarta take kwance tai lamo kamar me bacci ,tabude idanunta ganin bacci yariga yad’auke sa yasata mik’ewa a hankali tasuako daga kan gadon tasa hannu karkashin gado tadauko wani leda baki tamike tsaye tafito xuwa falo sadaf sadaf take tafiya harta fito kofar dazai sadata da waje tana xuwa tamurda kofar tabude’
Yana budewa tafita xuwa farfajiyar gdn ,bayan wani bishiryar fruit tanufa tana xuwa batare da 6ata tym ba tashiga haka rami agurin” bayan tagama haka ramin tabude ledar tadauko wani ruwa a leda tasaka acikin ramin sannan tabude wani kullin tafito dawani farin kyalle jikinshi duk madubi sai d’aukar ido yakeyi gawani gashi da’aka kulla ajikin madubin touch na wayarta ta kunna ta haska fuskarta dashi tana murmushi tafara cewa mahmud kazamtoh nawa nikad’ai kazam me biyayya ga dukkan umarni na karka bijiremin ,hafsa dake da ya’yanki kunzama bayina daga yau saina lalata rayuwarku hahaha,tana gamawa tajefa acikin ramin sannan tarufe,,
Waige waige tashiga yi sannan tamike takoma cikin gdn tarufo k’ofar ,,
Miemie dake kwance sai dariya takeyi ita kad’ai tace haba dai baraka kinyi kuskure wlh ,da sauri tabude k’ofar tafito cikin falon ,saida tak’arewa koena kallo a falon sannan tabude kofar fita’
Inda baraka ta binne wannan tsubbun tanufa tana xuwa tashiga hak’on ramin nan tafito da duk abunda baraka tasaka aciki sannan tanufi bayan gdnsu .tana xuwa tafasa wannan ruwan tazubar sannan tasa ashana ta k’ona wannan farin kyallen da gashi da madubin dake hade ,bata bar wurin ba saida ta tabbatar kome yak’one sannan tajuya takoma cikin gd’
Koda shigarta d’aki ganin baabaa laure tayi zaune tana rarraba ido ,murmushi miemie tayi tace mekika tashi yine da wannan daren ?
Harararta baabaa laurr tayi tace ubanki natashi yi ‘ina kikaje da wannan daren?
Rausayar dakai miemie tayi tace aina fad’a maki akwai aikin dazanyi a daren nan shine naje na aiwatar nadawo,,ido waje baabaa laure tace dan annabi kifadan gsky kodai kinshiga maitan da ake bada labarinsa ne ?
Dariya miemie tayi tace eh mana ya akai kika sani? Baabaa laure tace ai gani nayi baki nan shine nake tunanin ko meeting kika tafi”’
Tsaki miemie tayi sannan tabuga k’afa tana cewa ohh shit ,da sauri baabaa laure tace meyafaru? 6ata fuska tayi tace Allah oganmu ne nagun meeting yabani haushi wai saidai nakawo babana asha jininsa shine na roke shi akan abarmin babana zanbada tsoho amma fir mutumin nan yak’i wai saidai nakawo wanda nafiso .nikuma nayi tunanin duk duniya babu wanda nake so sama dake amma baran iya bada keba’ sbd ina matukar k’aunarki, ynxu haka fada mukayi da sauran yan’meeting d’in sunce koma kawoki su sha jininki kosu manna maki hauka da bara’a iya maganinta ba ,ynxu nakasa samun mafita dan Allah baabaa kifad’an mafita”
Subhanallahi wal’hamdulillah Allahu akbar shine kalmar da baabaa laure ke furtawa bayan fitsari datakeyi ,da sauri miemie tadubeta tace lah baabaa meyafaru kike fitsari?
Kallon miemie tayi idonta face face da hawaye ????
Tace ynxu dan annabi kirasa wacce zakiso saini ? Narokeki dan k’aunarki da annabi ki koma kifada masu kin tsaneni kuma duk duniya ba wacce kika tsana kamar ni kinji?
Miemie cikin hawaye tace baabaa saidai muyi hkr domin aikin gama yariga yagama dan sunriga sun yanke shawarar xuwa d’aukar ki ,shiyasa ma nashiga matsanancin damuwa lallai baabaa zanyi kewarki sosai wlh”’
????????ido baabaa laure tabude tace haba mutuniyata dan annabi kidenamin irin wannan wasan hawan jini zai iya kamani’ hade fuska miemie tayi tace aw kindauka wasa nake maki kenan ‘to bara kiga gsky” nan tadaga hannunta sama tana wani irin surkulle .kan wani lokaci saiga kwarya yafad’o saman hannunta ,habawa Baabaa laure Naganin haka tayi bakin kofa tana kokawar bud’e kofar amma anriga andatse, cikin gwalo ido take duban miemie tace
Wlh nayarda amma dan annabi kiymin rai wlh banason mutuwa ynxu haba ke kuwa meyayi zafi haka daga shigarki saiki badani ‘mika mata kwaryar miemie takeyi amma ita kuma sai matsawa takeyi .harta hadu da bango ,miemie tadube ta tace baabaa inkina so kirayu toh ki kar6i jinin nan kisha domin shikaidai ne zai iya tseratar dake daga hukunci oga ,jinhaka yasa da sauri tasa hannun takar6i kwaryar zatakai bakinta sai miemie ta dakatar da ita tana cewa wannan jinin dazaki sha jinin mutani dari ba d’aya ne aciki danhaka kina shanyewa kema kinzama irinmu’
Wayyo nan take baabaa laure tayarsa da kwaryan tana kuka ,,cewa take wannan ai bala’e ne yaza’ay nazama mayya ,kekam miemie zama dake bakomi aciki sai tarin tsiya , tsofai tsofai dani ace ina maita wlh gara na haukace yafi,,