YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: ???????? YAN ABUJA????????????????

BY HAERMEEBRAERH

Ina farawa da sunan Allah azza wa jal, mai rahama mai jin qai.Allah ka taimaka na isar da saqon alkairi kamar yadda nai niyya. Ameen

Wannan labari qirqirarre ne, ban yi dan cin fuska ko taba mutuncin kowa ba, zan yi domin samun qyara a al’umma musamman ma ma’aurata, dan haka nake roqon duk wanda Allah yasa ya karanta ya daure yai amfani da abinda yaji na alkairi a ciki, kuskuren daya riska , yai qoqarin kauce masa. INA GODIYA DA DIMBIN MASOYAN NOVEL DIN???????? WATA UWAR ???????? BAN FARA WANNAN SABON BA SAI DA ROQO DA
KWARIN GUIWAR KU, INA ROQON KU DA KUCI GABA DA MIN ADDU’A ALLAH YA RABA MU LFY DA MEDIA???? HAERMEEN HAMMAERH LOVE U ALLā¤

Page 1:

Gidan malam Baballiya, gidane mai girma na qasa, a tsakiyar garin kano, wanda ya qunshi mata biyu, Sarai itace uwar gida, sai Bilkisu, itace amarya, malam Baballe yana da yara guda hudu dika mata, wanda yake ta burin Allah ya azurta shi da da namiji, mai albarka, wanda ko bayan ba shi zai kula da wannan zuri’a tashi mai cike da rikici, domin tin yaran nashi mata na qanana gidan yake a cikin rikici, wanda Goggo ce sanadin komai wato Sarai, ita Mama Allah ya sa mata sanyin hali, amma kome za ai bata yarda a taba mata yar ta tilo ba, dan haka in aka ji rikicin ta to fa akan yar tane, ko shi ma ba zata tsaya aita bala’i ba , za dai ta tabbatar ta karbar wa yar ta ‘yanci sannan ta ja ta su bar wajen, a haka Allah ya raya masu yaran su guda hudu, Goggo Sarai nada, Suwaiba mai shekara 19, Saudat tana da shekara 18 wanda da watanni, sai Salma me shekara 16, Mama Bilkisu na da Juwaira wadda take sa’a ce ga Salma kwana uku ne tsakanin su, yanzu ta na dauke da tsohon ciki, wanda gashi nan haihuwa ko yau ko gobe. Sai dai mui fatan Allah ya amsa adduar Abba Baballiya domin kullum fatan shi Allah ya dube shi ya bashi namiji, mutum ne shi mai sanyin hali amma yana iya qoqarin shi na ganin ya isa da gidan shi, badan ma qoqarin da yake ba da tabbas Goggo Sarai zata zama itace mijin a gidan.

” wash Allah na, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Juwaira, taimaka ki kira min Abban ku a waje” da sauri ta dau mayafin ta da ke kan qofa ta yafa ta fita ” Abba Maman mu na kiran ka,kai sauri Abba bata da lfy kamar haihuwa zatai ina jin” da sauri ya shiga takalmin ma yaqi qarasa shiga qafar tashi, ” Subhanallahi Gimbiya, haihuwat ce?” ( yana kiranta da Gimbiya ne don a ilimin shi na addini ya san cewa kiran sunan mata da suna mai dadi sunna ne, inda yake kiran Goggo Sarai Sarauta) ” Malam taimaka min na samu na kai uwar daka bana son zama a nan na haihu a rumfa” kamata yai ya kaita daki ” amma mun shigo daka ko dai muje asibiti ?” Murmushi tai sanin cewa qarfin hali yai dan ya kwantar mata da hankali ya fadi hakan ta san bai da kudin yin hakan, ko na mota basu da shi, shi kuma ba mai kwadayi ba ne da zasu samu a wajen Goggo Balki, dan yayan ta kyawawa inji ta da fada YAN ABUJA ne su sai mai kudi, dalilin wannan ne yasa take samun kudi sosai, duk da fadan da Abba Baballiya keyi akan su daina biyewa samarin banza, amma sukai kunnen uwar shegu , da ya musu wuta2 kuma ya fara kulle sai ta saka su Islamiyya,daga sun fita zasu bi gidan qawaye su canja kayan su, su qara gaba neman mazan da zasu aure su su kai su Abuja, gaba daya basa hulda da qawyen su na unguwar, sai ‘ya’yan masu kudi, saboda anan suke saka ran samun nasara. Kukan jariri ne ya dawo da Abba daga tinanin ina zai samo kudin kai ta asibiti ta haihu lfy? Da hanzari ya qarasa taimaka mata ta haihun ya kuma gyarata ya aje jaririn ya fita qofar gida, “Juwaira doran ruwan zafi in ya yi ki kirani” to Mamana sannu” cikin zumudi da washe kyawawan haqoran ta farare masu dauke da hushirya a saman su, fita tai taje dora ruwan taga ba iccen, amma duk da haka sai ta je ta dakko tukunya ta wanke ta zuba ruwan ta kawo wajen murhun ta aje, zata juya kenan ta ga mahaifin ta na shigowa da icce a hannu da kuma leda, da hanzari ta isa ta karba, tana mai sannu, komawa tai ta hada wutar ta dora shi kuma yai dakin, tsaki taji anyi a gefen ta, qin juyawa tai dan tasan ba zai wuce daya daga cikin yan uwan ta ba” aikin banza sai rawar qafa ake, duk dai abun mutum mace ya qara haifa balle ai mana wani rawar kan uwa ta haihu????” hmmm Allah ya kyauta ya kuma shiryar da ku dika, to bari kiji yan baqin ciki, wannan karon namiji Mamana ta haifa a cikin gidannan, dan haka baqin ciki ya kashe duk wani dan hassda” wani uban ashar Salma ta saki ta tashi da hanzari zatai dakin su cikin rashin sa’a bokitin gaban ta ya bige tukunyar da take dafa abu, ai ko tini ta zube nama ne na kaza cike da tukunyat wanda yafi qarfin kaza daya, ko kulawa ba tai ba ta shiga dakin da gudu tana “Goggo ! Goggo ! Wai ni kina ina ne wannan mummunan labari ya same mu?” Da saurin su suka fito dikkan su an qule a daka ana hasafin kudin da suka samo, suna bata labarin mazajen da ke son su turo ai zancen auren su, ” ke meye haka duk kin fadar min da gaba kamar Bilki ta haofi saurayi” hmmmm ai kinji ashe ke kikai mana mugun fata baki da tinani sai wannan, gashi nan to ya tabbata ai” damqo ta tai da qarfu cikin zare ido take tambayar ta” me kk nufi salma?” Ina nufin Mama Balki ta haifu saurayin da kullum kk mana mugun baki akai????” ai wurgi tai da ita gefe, ta qume kai da hannun kujera sukai gaba ita da sauran yammatan nata, sai dakin Mama Balki” me nake ji? Me nake gani? ” Abba ne ya baje ma Mama Balki nama balangu sai shayi daya hada mata da madara ta gwangwani da bred, “No i cant belive this, what is going on here, ina jaririn yake?”A cewar Suwaiba yar boko kenan, don tana da NCE ita sai Saudat me kwalin secondary a hannu wanda duk daya take da su Maryam sai dai Juwaira tana son ta cu gaba ba halin ne yasa ta hakura, amma sakamakon ta yayi kyau sosai, both WAEC & NECO, ” Haba Sarauniya ta ya zaki shigo daki haka ba ko sallama? Kuma bama ki tambayi ya ta haihu lfy ba? Aa tambaya kuke ina jaririn?” Eh ban ga zan iya ba ne shiyasa ban ba, tambaya daya ko da zan yi shine me aka haifa?” Na miji Allah ya bani, me zai faru? Allahn da ya ban ba wai dan ya manta ki bane kema ai, in kin kwantar da hankalin ki kema naki na tafe, dan haka ku fita min a daki tinda ba arziqin yi min sannu ne ya kawo ku ba”Hahaiiiiii Cassssss, eh lallai ne, kinyi da na miji shine zaki fara min kitifi ko, to bari na baki wani labari, a da kam na damu amma yanzu wani tinani ya wanken damuwa ta, Shi Uban yaran me ya ke da shi ya tara da zan damu raina akan namiji? Bayan ga Yaya mata Allah ya bani na zuwa Abuja ? Yarana kowanne namiji mai lafiya ya gansu sai ya yaba, dan haka bama zan bar labarin nan ya kwana ba: bakin ta suwaiba ke son rufewa tana” Goggo ki bari ba yau ba kin sanar da su, ko kin manta halin yan baqin ciki ne?” Aa Suwai ba Banni na fada masu suji dan baqin xiki ya mutu, yarana guda biyunnan sun samu mazajen aure mazauna Abuja, dan haka sai ka bude kunnen ka kaji, zan basu izinin cewa su turo magaba tan su a zo ai komai,” hmmmm Sarai kenan wato kece ma mijin yau ni ne matar ko? Umarni kk ban akan mazajen auren si ko? Ba bincike ba komai kawai su turo b to bari ki ji na fada maki zan ba yayan ki mijin da suke so amma komai yaje yazo ki kuka da kanki kina jina ko? Fitsarartiya mara kunya mai raina mijin ta gaban Yayan ta dan su koya suma” ranshi bace ya matsa kusa da Maman yana bata naman a baki” Shewa Saudat tayi tace ” ikon Allah wai na kwance ya fadi” dariya Suwai ba tai da Salma suka tafa har da uwar tasu suka fice suna dariya, can qasan maqoshin Goggo balki kuwa kishi ne damfare, kada kai tai a ranta tace” Hmmmmm to ai ku gama da yayana sun tafi ABUJA aure kashin ku ya bushe a gidannan.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button