YAN ABUJA HAUSA NOVEL

……………
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????
BY HAERMEEBRAERH
Hey guys i am sorry yesterday i fogot to number the page, it suppose to be page 10 and this is page 11. Thanx me love u XoXo.
Page 11:
Wata qara da Goggo Sarai ta sake da sunan dariya, dan kawai ta ja hankulan su,”Hahhhhaaaaa kaiiii amma naji dadin haduwar ku gaba daya tare, ikon Allah ana can ana cin amarci sai yau aka samu haduwa kenan, to ya masu gidan? Ya rayuwar hutu da jin dadi?”
“Lfy qalaou Goggo, ina Abba?”
” Hmmmm ga shi can wajen waccan sallamammiyar matar tashi da ta shanye shi”
” Bashi mu gaisa kar yace bamu neme shi ba”
” Aiko bada wayata ba ehe ku kira shi a yar rakani kashin shi kawai”
Tana fada tana hura hanci tana turo dankwali gaba irin na fitsararrun matan nan? Kada kai Abban nasu yai yace” Allah ya kyauta” murguda baki tai kamar wata qaramar yarinya, irin na rashin kunyar nan,( dan kunsan murguda bakin ma kala2 ne, akwai sexy murguda baki mai daukan hankalin oga, yaji dole sai ya kai nashi bakin a naki sabida yanayin yanda kikai yi shi da salon jan hankali, sannan akwai na rashin kunya kamar na Goggo sarai dai) miqewa yai da niyyar fita sai wayar shi ta hau ringing, dagawa yai da sallama, su Suwaiba ne, gaida shi sukai kamar ba sa so ya amsa tare da tambayar su gidajen su,” hhhhhh Abba do u really have to ask ? We ar fyn, komai normal kamar dai yanda ka sani Abba mazajen mu masu kudi ne, so ina ganin ai bamu da wata matsala mu”
” Suwaiba ni mahaifin ku ne ba zan gaji da maku nasiha akan ku bi duniya a sannu ba, yau in kaine gibe ba kai bane, dukiya da abinda ke cikin duniyar nan ba komai bake face rudin shaidan ga wanda ya mai da su abin bauta, kuji tsoron Allah a lamarin ku, Hello ! Hello….. shiru yaji ashe sun dade ma da kashe wayar tin da ya fara wa’azi suna ta surutan yanzu zai takura masu, mamaki je cike da zuciyar shi, ” yarannan ni suka kashewa waya?” ” Abban su kai hakuri komai zai daidai ta da qarfin addu’ar da zaka dinga wa iyalan ka, Allah zai shirya maka su inshaa Allahu, adduar iyaye amsasshiya ce a wajen Allah, Allah ya shirya mana zuria” ” hmmmmm Ameen Gimbiya ta Allah ya albarkace ki da zuriar mu duka” dadi ne ya kamata mara musaltuwa a duk sanda ya mata wannan adduar” Ameen a bin sona” murmushi sukai, nan da nan yaji baqin cikin shi ya tafi, ruwan wankan da ta saka mai yaje ya shiga yai wankan shi, ita kuma ta fara qoqarin dora madu abinci.( magidan ta ku na qoqarin yi wa matan ku godiya da addua musamman ta nema masu albarka a wajen Allah, in albarkar nan ta wanzu a garesu ta shafe ku, da xuriar ku kenan, mata ku dinga dukkan abinda kk san zai faranta masu rai sui maku adduar, soyayya bata tsufa sai dai masoyan su tsufa).
Nafeesa ce ta shirya tsaf cikin riga da skirt na atampa, tayi kyau sosai ta taho bangaren su Juwairah” matar Yayah ya naga baki shirya ba kin saka dan guntun wando da vest an faka gashi gefe?” ” Nafeesa kenan ina ga alama kin manta yau Yaya da wuri zai dawo sannan yau ranar dana ware domin gyaran lambu na ne ko? Ga girki da zan da wasu aikace2n, kuma sanin kan ki ne ni fa yawon shiga nan shiga can dinnan ba son shi nake ba, shike kawo mace ta daina kula da iyalan ta da gida tana qarewa a titi” ” hakane kam gaskiya, ni dai zan tafi gidan Shamsiyya na gaida ta, dan na mata alkawarin zani yau din, na zaci zamu tare ne tinda naga ke kin dade baki je ba, sai na dawo to” ” to ki dawo lfy, ina gaida ta da yaran” fita tai ta tafi, ta je gidan Shamsiyya inda ita shamsiyyar yaran ta biyu mace da namiji, Farha da farhan, goyo take tana goyon macen , gaba daya gidannan sai a hankali, komai da kan shi yake zama, bai da muhalli, shiga tai palo ta zauna da sauri ta miqe tana duba skirt din ta daya jiqe, hannu ta kai hancin ta taji wani mugun xarnin fitsari, da sauri ta kauda kanta ta fita tsakar gidan,ruea ta sa ta wanke hannnun ta saka a skirt dinta tana masifa” ni gaskiya shiyasa bana son zuwa wajen ku shamsiyya, ga gida har gida Allah ya hore maki amma sai uwar qazanta, duba dan Allah daga zuwa na xauna akan fitsari , ko da Juwaira bata haihu ba na san.abin da ba za a taba samun ta da shi ba kenan, yanzu haka saboda gyaran gidan ta da kula da haqqin mijin ta yasa taqi biyo ni, Juwairah nada lokutan yin komai, tinda ba za a hadu ace kullum zaka hada kowanne aiki kayi ba zaka gajiya, sai wanda suka zama aikin yau da gobe, dan Allah ki gyara, dan yana daya daga abinda yasa Baban Farhan yake neman aure duk.da ya fada maki amma kinqi gyarawa” kaiiii hajiya bala’i daga zuwa.sai wannan dogon karatu? To dan Allah ya kuke so nayi? Ga aikin gida gana miji gana ‘ya’ya” sai ta fara hawaye wai ita a dole komai ya mata yawa, kama hannun ta Nafeesa tai suka koma palon ta zaunar da ita a kujera, sai da ta laluba wata taji ba jiqa ta zauna ta fiskance ta, ” qawata ni ba wai ina maki fada dan ranki ya baci bane” ” to dan meye? Saboda kowa ya tsane ni sai a dinga ce min qazama ? Kalmar qazama fa na da ciwo tsakani da Allah” majina ta sharba tana gige hancin da zanin ta, ” to yanzu kingq hakan da kikai ni ba zan yi shi ba, da na goge majina da zani gwara na je na wanke hancin, ai in kk ji ance qazama akwai kalmar tsafta kuma ko? To ni so nake ki cire kalmar da kowa ke kiran ki da shi na qazan ta ki mai da shi mai tsafta, yanzu ki fa duba kiga Mama Bilki, kullum kk dhiga wajen ta kinga dai ta tsufa ko, amma tsabar qamshi da tsafta bazaki so barin wajen ba, come to think of it ba fa ta da kudi da wadata kamar ki? Dan Allah ki gyara ki rage son jiki,son kallo da karancr2n nan na zamani har sai kin gama komai sannan ki dauka ki fara,ina fatan wannan ya zama na qarshe da wani zai baki shawara ko za a zage ki akan tsafta, in baki gyara ba Abban Farhan yace maki zai qara aure kuma ya fara nema in kk gyara nasan bari zai dan matsalar shi dake kenan ba wani abu ba” ” Na gode qawata, ba wanda ya taba zaunar da ni ya min bayanin ya shige ni” ” ba godiya a tsakanin mu” murmushi sukaiwa juna shamsiyya ta miqe ta fara tattara kayan wajen data loda a kujera, nan da nan Nafeesa ta taya ta suka gyara gidan ya dau hake da qamshi, girki sukai mai rai da lfy kala2, wajejen la’asar Nafeesa ta bar gidan cike da tsaraba daga wajen shamsiyya, a ranar ta sha wanka da gaye, Abban Farhan daya dawo ya sha mamaki amma bai nuna ba, sai ya nuna mata matuqar jin dadin shi, dakuma yabawar shi tashi yai yaje dakin shi yace ” ina xuwa” wata sarqace ta gold mai kyau ya zagaya ta bayan ta ya daura mata suna kallon madubi, dan harda koyawa yaranta baccin wuri sai da Nafeesa ta koya mata, godiya tai ta masa shima yana godiya, ba a jima ba taji zancen aure ya rushe, sai dai ya sanar da ita cewar” Baby ki kwantar da hankalin ki dan ni ba mai ra a yin mata biyu bane ko sama, tsaftar ki da rashin tsaftar ki in ni me ra ayi ne ba zata hana min yin aure ba, na fada maki ne dama dan ki gyara mu more ratuwar auren mu yan da ya kamata” taji dadi sosai inda ta qudurta ma ranta xama mace mai tsafta ta bugawa a jarida, yan dakowa ya mata tambarin qazan ta sai an buga mata na tsafta in Allah ya yarda. Ni ko na ce to Allah ya yarda ya shiryemu mu gane tsafta na da kaso mafi tsoka a rayuwar aure.