YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Bayan Juwairah ta gama komai ta yi wanka ta kwanta tana hutawa, tasbihi take ta yi ga Allah bacci ya dauke ta, tafiyar tsutsa yake mata a qafar ta ta farka idon ta na qara lumshewa, juyi tai ta cusa kanta a cinyar shi ta ci gaba da baccin ta, a hankali ya janye ta dan ya kula a gajiyae take, yaje ya cire kayan shi ya aje inda take aje masu kayan wanki bayan ya ninke, ya tafi wanka dan har da ruwan wanka ta aje mai, bayan yai wanka ne yaga kamar bata ci abinci ba ya shirya ya zo ya qara tashin ta sai magagi take bacci ne sosai a idon ta a haka ya daga ta ya zubo abincin yana bata yana ci duk abinnan da ake idon ta rufe yake, ” Yah Jabeer ka dawo?” ” Eh na dawo princess” ” Sannu da xuwa” “yawwa, meke damun ki ne yau?” ” bacci nake ji na gaji ne sosai, ga jiri danake ji, tin shekaran jiya kuma sai naji cikina na ciwo, kamar ana min motsi a ciki” har yanzu ta qi bude idon,” Subhanallahi, gobe zamu asiniti mu ga likita dan shiyasa kk ji kwanaki ina ce maki sai naga kamar baki da lfy, abinda ke kwantar min da hankaki kawai ganin yanda jikin ki ba wani damuwa sai kyau da kk qarawa ma, nan din ki har wani kyalli suke” hannun shi ya kai saman rigar ta yana shafawa, a hankali ta janye hannun shi ta juya baya ta ci gaba da baccin ta, wani yawu ya hadiya, ganin yanda hips din ta suma suka ciko sosai kamar sui magana, tashi yai ya maida plate din ya wanke bakin shi da hannu ya rufe ko ina ya dawo” princess ko dai fushi kk ban dawo da wuri ba yanda na saba? Shi ne kk share ni kk son yin bacci?” Shiru yaji, matsawa yai jikin ya ya janyo ta, bacci yaga tana yi sosai, bai so haka ba, gaba daya ta rikita shi, amma haka ya hakura dan yasan ba halin ta bane kyale shi koda tana cikin fushi ne, ja masu abin rufa yai yai masu addua ya shafa masu, suka kwanta……..
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????

   BY HAERMEEBRAERH

Alhamdu lilLAAH ala kulli halin, naji sauqi sisters na gode da kulawa, Allah ya barmu tare da alkhairi mara yankewa. ME LOVE U XOXO❤

Page 12:

Da asuba ta tashi ta duba taga har ya fita masjid, addu’ar tashi daga bacci tai ” “Alhamdu lilLAAHi alladhi ahyani ba’ada maa amatani wa ilaikannushour” sannan ta sakko daga gadon ta je tai alwala ta dawo ta gabatar da raka’atanil fajr tai sallar subh,tai azkar din safiya, tana idarwa tai azkar din ta, tana gama wa wanka taje tayi ta sake yin brush, gaban madubi ta zo ta warware kitson da tai da yamma, guda biyu akan ta sakamakon ba ta son kitso sosai kuma shima Yah Jabeer din nata yafi son tana mai adon gashin haka ba tare da ta kitse ba( yana da kyau mace ta iya yin kitso biyu irin na indiawan nan da muke gani ana raba kai biyu a kwantar gefe da gefe a dame shi a kitse sai yai matuqar kyau in ke mai santsin gashi ce ma zakiga har sheqi yake da dare ake wannan kitson bayan kin gama wa oga kwalliya, ma’anar yin wannan kitson na farko dai zaki bacci ba tare da kanki yai buyaya ba, kinyi muni, da safe zaki tashi kan ki tsaf da shi, bai barbaje ba, sannan kuma in ma kun samu kusantar juna da me gida kin yi wanka kanki ba zai na lalacewa ba nan da nan kiji mata suna kai yasha ruwa gashi na.zubewa, akwai fa’ida sosai akan yin hakan da sai kin fara zaki gano su da kan ki) da sauri take yin komai ba son jiki, dan ba ta son sai ya dawo ne zatai wadannan abubuwan, ya na dawo wa daga masjid ya tsaya wajen Innar mu su gaisa, kamar kullum, riqe shi tai d surutai na ba gaira ba dalili, daga baya ne ta fara tura mai saqon dake ranta a wayon ce” Allah sarki Juwairah yarin yar nan akwai hakuri, kaga fa yanzu wata na wajen.shida kenan.da auren ku, qawayen ta sun haihu amma ita ko batan wata bata taba yi ba, amma bata damu ba, ko dake dama yaran zamani.ai ku ba ruwan ku, mu ne dake son yan jikoki mu za mu damu, waya sani ma ko maganin hana haihuwa take sha” wani irin faduwar gaba ne ya samu Jabeer ido ya zaro waje yace” Haba Innar mu Juwairan nawa take d zatai wannan tinanin? Kuma har ta aikata hakan? Inaaaa sam ba zatai haka.ba kima daina wannan tinanin dan Allah, kuma da kk zancen sa’o’in ta Innar mu Nafeesa ma fa sa’ar ta ce ita kinga ai har yanzu ma batai aure ba, in da zaki gane komai nufi ne na Allah ko” habaaa kamar ya watsa mata wuta, bala’i ta fara kamar ta ari baki” iyeeeee lallai e Jabeeru ka nuna min mata tafi ‘yar uwa ko? Har qanwar ka zaka duba kaiwa gorin aure? To bari na fada maka abin da nake boye maka, nifa na fara gajiya da wannan yarinyar, tin da ka aureta ka daina bamu lokacin ka, ka daina zama ai hira kamar ta da da kai, sannan gaba daya soyayyar ka da kulawar ka ta koma wajen ta, akqn me?” ” akan shi ne mijin ta, kuma hakan da yake shine yake nuna ya haifu dan sunna ne, yanzu dan Allah bakiji kunya ba? Kk hada kan ki da surukar ki? ‘Yar ki kuma ta wani bangaren? Habaaaa Hansai, wace irin rayuwa kk daukar wa kan ki yanzu, abinda ba halayyar ki ba kina neman shaidan ya maki huduba ki fara, to bari na fada maki abinda mata kan ku yake toshewa akai, kowacce mace dangin miji ce, kuna uwar miji ce wataran in ranta ya kai, dan haka in kikai wa matar dan ki adalci, kema sai wata taiwa taki yar, in kk kyautata wa matar wanki ko matat qanin ki, kema naki qannen mijin da matan yayun sa zasu tausaya maki su miki adalci, in kuma duk kin kiyaye amma ana maki abinda bai dace ba, to ki sani kowanne dan Adam akwai jarabawar shi, wataqila taki anan take, sai ku hakuri ki qoqari kuma ki cinye jarabawar taki, dan haka in kk kula, tin da Jabeeru yai aure kulawar da na ke ba ki ta qaru, ba dan komai ba sai dan kula da nai kin kai idon ki gidan matar dan ki, ki gyara hali ko kun samu rabauta a lahira, baki tafi da haqqin kowa ba, haihuwa ta Allah ce, ko bata haihuwa haka yaga zai zauna da ita ke baki isa ki ce dan me ba” Baba Balarabe kenan da ya dade a tsaye yana jin maganganun Innar mu, wata irin nadama da kunya ce ta kama ta,” Malam ka yi hakuri, Jabeeru ka yafe min sharrin zuciya da shaidan ne, ina ganin tin da ta zo komai namu yaja baya, ga shi kana nuna mata tsantsar so, idona ya rufe akan hakan na manta nima nawa mijin yana iya qoqarin shi akaina, ku yafen ba zan qara ba” nan ta zayyano yan sace2n da tai tayi wa Juwairah dan ta hada su fada amma sai taji shiru, saka makon iya zaman duniya da Juwairah ke da shi da ta kula hakan ta faru zata san dabarar da tai ta bashi hakuri, da jikin ta da kalaman tq, ” Ba komai Innar mu ya wuce ke uwa ce a wajen ta, da bata dauke ki uwa ba uwar miji ta dauke ku da ita kanta zaman sai ya mata wuya amma tasan ko da uwa da uba ana sabawa fiye da haka ma a kuma ci gaba da zama, dan haka na san ba ta qullace ki ba, jiya kwana tai ba lfy, asibiti xamu ma” Subhanallahi” suka hada baki dika ukun har da Nafeesa, ” meke damun ta?” Inji Innarm mu, ” Da ciwon jiki ta kwana ga zazzabi da ciwon kai, ciwon mara, da kasala, dan jiya wani irin bacci ta dinga yi” murmushi Innar mu tai tana” ikon Allah ai ya kamata a kaita ta ga likita bokan turai a fada mana wata nawa ne, na fara tanadin kayan kwalliya dan da alama bana zan yi ango nima, in kishiya ce na samu na gyaran daki,kar ta zo ta fini. Wajen Malam” Innar mu me kk nufi hakan?” Inji Nafeesa kenan, Jabeer kuma a ranshi cewa yake” Allahumma ameen” ” Innar mu bari na wuce naga ko ta shirya mu tafi” ” to Allah ya qara afuwa” tashi yai baki a washe kamar gonar audiga, ya isa, qamshin da yaji ne ya qara kwantar masa da hankali, ga nutsuwa da qaunar matar shi da yake ratsa shi, sallama yai ta amsa, durqusawa tai ta gaida shi, ya amsa tare da jawo ta jikin shi, daga kanta yai yana kallo, wata riga tasaka shara2 ko ina ana hangowa a jikin ta, sai wando guntu rigar bata gama rufe mata cibiya ba , tai parking gashin ta in to ponytail, fuskar ta tai fayau kyaunta na qara fitowa, the more yana kallon ta the more yana qara ganin kyaunta, bata cikawa fuskar ta makeup ba, iyakar ta powder da lipstick, sai tirare da ta fesa ta shafa mai, zame rigar yai yana shinshina wuyan ta, ita kuma maida kanta baya tai tare da miqa mai qirjin ta gaba, nan take hannun shi na rawa ya daga ta tsaye ya zame rigar ta ta yana qare mata kallo, duk wata tsiga a jikin shi ta gama tashi saboda wani irin kyau daya ga ta qara” Babe ni dai bana son wannan kallon da kk man yai yawa, tin da ka shigo kk kallona” ta fada cikin shagwaba da sake narkewa a jikin shi tana wani dan zame wa shi kuma da sauri ya janyo ta, gaba daya ta gama rikita shi, daukar ta yai cak sukai daki, bam qara sanin me ake ba sai da naje na wajen Innar mu na sha kokon safe na dawo???? a gadon na hango su suna manne da juna, ” My princess , jiya kin manta yau munyi zan kai ki asibiti ne? Gaba daya naga yanda jikin ki yake jiya da yamma yau kin tashi garau da ke” Eh My dear, kaga in banda da asuba dana tashi naji kaina na dan ciwo kadan, sai da na zo brush warin toothpast din ya sani amai, tin da nai aman nan naji dadi, yanzu inajin na warke ba sai mun je ba ma” ” Aa ba haka za ai ba, ya kamata mu je asibiti muji me ke saka motsin da kk ji ko ya daina” yana fada yana shafo cikin nata da tausayawa, nan da nan idon ta ya ciko da kwalla” Yah bai daina ba, dazu ma ya min, ga tsoro da yake ban in ya motsa din, sai naji kamar wani abu ne a ciki” ta qarasa tana mai yin kuka” Here, here my baby, stop crying , ba komai inshaa Allahu sai alkairi, u don’t have to worry ur self babe, koma meye zamu samu maganin shi tashi muje mui wanka mu shirya muje” tashi ya fara, ya miqa mata hannu ta kama, a hankali ta miqe, sai yanzu ya qara ganin qirman da qirjin ta yayi, ga cikin ta ya dan tasa ta qasa, ta yi wani fari sosai, kamata yai ya zura mata doguwar riga da dan hijab din da take zuwa wanka, tinda gidan akwai suruka, sannan kuma safiya tayi, shima ya zura tashi rigar , qofar su yaje ya rufe sannan suka shiga wankan bayan sun gama ne suka dawo suka shirya, suka fita, saida ta biya wajen Innar mu ta gaida su sannan ta tashi zasu tafi” Juwaireren Mama ki yafe wa Innar ki laifukan da ta miki domin Allah, sharrin shaidan ne ya shige ni da son zuciya, amma in Allah ya yarda ya wuce ba zan sake ba” wata kwalla ce ta fito mata ta godewa Allah da ya kawo mata komai da sauqi kuma da wuri,” Haba Innar mu ai ba komai, ni fa yar ki ce, ke uwa ta ce, ban dauki hakan.a komai ba, face gani.nake nice bana kyautata maki yanda ya kamata, nima ki yafe min”Baba balarabe na daki yana jin dadin kasancewar Juwairah a matsayin surukar shi, yarinyar dan uwan shi, da yake so, yarinyar data samu tarbiyyar iyaye na gari.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button