YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Bayan kwana arba’in da shida ne, anyi suna da kyar wanda ba wani tari da akai an sama yaro Ammar, yaro kaykkyawa kamar iyayen shi, amma yafi kama da Juwaira, ba qaramin so da gata yake samu ba a wajen su, musamman Juwaira din ma, yan zu haka wasa take mai ta shimfida tabarma a tsakar gidan inda ya sha shara ko ta ina yayi fes da shi, dakin su kuwa ba abinda ke fitowa sai qamshin tirarwn wuta na tainke, Sallama Abban su yai shigo jikin shi a mace, amma dik da haka sai da yai masu wasa ya sumbaci Ammar ya shafa kan Juwaira ya shiga cikin dakin Goggo Balki, kwalama Juwaira kira yai yace ta kira Mama………
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: ???????? YAN ABUJA ????????
BY HAERMEEBRAERH
Page 2:
Da isa da qasaita ta shigo palon, hakan ne yasa Abban murmusawa duk da qunan da ran shi ke masa na abin da take yi mishi” Sarauta kenan yi ki qaraso mui abinda zamui na fita sallah”isowa tao tana hura hanci ta zauna a gefen damar shi inda Mama Bilki ke zaune a gefen hagun shi,” da farko dai zan ma Allah godiya daya kawo man wannan rana danake ta buri, domin manema auren yaran nan ne Suwaiba da Saudat suka zo, kuma mun karbe su a gidan Yaya Balarabe cikin aminci da mutunci, inda suka damqa mana dukiyar auren yaran, Suwai ba kudin auren ta sadaki, na gani ina so da kudin da zata hada lefe dika, an bamu million daya da dubu dari biyu, sai na Saudat Ita kuma Million daya, a gaskiya na so naqi karba saboda kudin sunyi yawa, kamqr wanda zamu saida yayan?……. Abban su ina fatan dai bakai mana baqin cikin iyayen zamani ka sa an rage kudin nan ba?” Ta fada tana cike da tsoron ko dai an rage kudin ?” Amma dai na rasa me yasa baki da da’a wallahi? Ya ina magana ban qarasa ba zaki katse ni? Har kina ikirarin zan ma yayana baqin cikin iyayen zamani? Anya rayuwar da kk na da kyau kuwa? Gaba daya kin sa tarbiyyar yarana a lalace? Kin raina ni baki ganina da qima da mutunci? Kedai harka in ba ta kudi ba baki san komai ba? Na gode Allah da yasa ina iyakar qoqarin riqe gidana, ke kam na san da karuwanci zaki saka yayana yi su na kawo maki kudi, haba, bai ishe ki misali ba da Balki? Yarta daya amma ta tsaya wajen bata ilimin addini dana zamani daidai iyawar t, ke kuwa in ba Salma ba da tai sauka yarannan biyu ba zasu iya bude qur’ani sui karatu mai kyau ba, Salman ma gashi nan ne kawai, to ina mai maki nasiha da kiji tsoron Allah akan abinda kk, ina jiye maki ranar kuka, ranar dana sani, ranar ni yasu,…….. ” Aa faaaa, bafa zaka sani a gaba ba kana min mugun fata da kuma maganganu na nuna baqin ciki qarara a wannan al’amari, Yaya dai nawe ni nai naqudar su na haifa, ba wanda ya taya ni lokacin danake qafa daya lahira, daha duniya,ko akwai? Dan haka sai wanda naga damar su aura sannan zasu aura, nifa takura ce bana so tammm, yanzu ka bamu kudin lefen da sauran dan musulunci bai yarda kowa ya taba dukiyar auren yara ba sai su ehe” hmmmmm Sarai kenan to ai bari kiji iya kudin lefe zan baku, sauran kuwa sai sanda akai auren su zan baki su, da ke a taki qaramar kwakwalwar sai na dauku kudin na baki dika? Haka kawai aje wani abu ya faru bana fata ba ai aure ba ku barni da biya da tashin hankali? To bazai yu ba” Bala’i ta miqe tana zazzagawa son ranta ita sai an bata kudin, tashi yai ya kade rigar shi ya fice dika a gidan, daidai lokacin da Mama Balki ke cewa” Ubangiji ya sanya alkairi da albarka, Allah ya kare dukkan abinqi ya basu zaman lfy” Hahaiiiiiiiii Cassssss, ni zaki wa bariki? Zuciyar ki cike da baqin ciki amma wai kk addua mai dadi haka, dama ba daga bakin ki ta fito ba dana ce ameen” sa kai tai ta fice ta shiga madafin su ta hau aikace2, tana yi tana masifa kamar wadda ta zautu, yaran ne suka dawo daga yawon tazubar din su da sunan Islamiyya, ” wai Goggo me ke faruwa ne gaba daya muryar ki har qofar gida” hmmmm wannan sallamammen uban naku ne mana, an kawo kudin auren ku sun riqe shida Balarabe, to wallahi ni ba zasu nuna min isa da iko ba, sai sun kawo kudin dika” Goggo kwantar da hankalin ki tashi mu shiga ciki ki gani” inji Suwaiba, daki suka shiga ta dakko mata maqudan kudi.a jakar ta saida tai baya dan yawan su,” waya baki wannan kudi haka?” Alhaji Salihu mai tumbin Nera kk ji, cewa yai ga su ko zan qara wsu abubuwa a lefe yaso bayar wa a can ya fuskanci za a iya cewa sun yi yawa, shi kuma yana ganin ko nawa ne zai iya kashewa ya samu yar zuma, ( Sunan da yakan kirata kenan lokacin watsewar su) dariya Saudat tai ” Aaaaa kice Adda Suwaiba Alhaji yaji zuma yau” dariya sukai dika har uwar tasu suka tafa, baqin cikin ma da take ciki ta manta shi, ba sallah ba salati suna zaune ana maida tanda akai da yanda za ai.
Juwaiirah ce na hangi goshin asuba ta na ta ibada, kamar wata babbar mata, Maman ta ta saba mata da tashin dare, dan ta sanar da ita cewar duk abinda bawa ke so ya roqi Allah zaibiya masa buqatar shi musamman a lokutan karbar addua wanda qarfe uku zuwa asuba Allah na amsa adduar bayin shi dan lokaci ne mai mahimmanci ga bayin Allah, ” Ya Allah kaine masanin abin da ke zuciyata Allah ka biya min dikkan buqatu na na alkairi Ka sa Yaya Jabeer ya zama shine mafi alkairi a rayuwa ta duniya da lahira” wannan addu’ar ce tafi daukan hankali na, nace tooooo waye kuma Yaya Jabeer? Adduar ta ta ci gaba wanda tai wa iyayen ta da yan uwan ta da dikkan muslmi, bayan ta idar ne ta hau karanta Qur’ani da zazzaqar muryar ta, har aka kira sallah ta gabatar ta dora da azkar da karatu har gari ya waye, a sannan ne ta samu ta dan koma bacci zuwa qarfe takwas ta tashi, ta fara taya Maman ta aiki, bayan ta gama gyara gidan dan ba su ke girki ba balle ta taya ta aikin girki, wanka ta shiga ta fito,haka nan taji tana son yin kwalliya yau dan ita ba ma’abociyar yin ta bane sai dai tai kwalliya sama2 kawai , ta saka wata rigar ta doguwa ta atampa rigar na da fadi ta qasa unda ta sama aka dan tsuke ta da dogon hannu yanda rigar ta zauna mata abin kallo ne domin Juwairah akwai shape mai kyau, gyara gashin kanta tai da kyar dan yawan shi da tsaho, bayan ta gama ne ta kafa dauri me kyau, ta samu tiraren ta ta fesa, tana gamawa ta je wajen Maman ta zata dau Ammar, Maman ke tsokanar ta” Aa kaga Juwairere saraunuyar mata,Juwairere diyar Mamanta” ni mama na ce maki bana son Juwairere Allah dariya qawayena suke in suka zo sukaji kina fada musamman Nafeesa” to in banda abinki Nafi ai qanwar ki ce kin fa bata kwana bakwai masu kyau” kin ga kuwa data tsokane ki sai ki murmushi saboda yarinta ce ba wani abu ba” dariya suka saka sosai suke dariya saboda sarai ta san maman nata na tsokanar ta ne again, basuji sallama ba sai ji tai an kama hancin ta,” wannan dariyar taku Mama ba zata bari kuji komai ba , musamman wannan Juwaiirahn da ta bude wannan qaramin bakin nata take cikawa mutane gida da yar muryar nan ta ta”tsalle tai na murna ta kama hannayen shi dika” Yayana, wayyo Yayana kaine da gaske? I missed u so much Yayana, yaushe ka dawo? ” Oh Juwaiiraah ko zama bai ba fa wannan zumudi a bari ya dan zauna ya huta mana” Mama rabu da ita nima ba qaramin Missing din Juwairere na nai ba, ban ga laifin ta ba dan ta nuna murnar ta na gani na” murmushi Mama tai ta fita debo masa dan ruwa ya sha dan gidan haka suka tashi ko na karyawa ba a miqo masu ba, jawo ta yai kusa da shi ” Amma da Juwairere kin san na hana kwalliya ko?what if wani ya zo ya gan min kwalliyar mata? Ko a aike ki a haka kowa ya kallen ke? A gaskiya ni dai bana so, anyways yanzu ai ta qare tinda ga angon ki nan ya gani” ???????? duqar da kan ta tai murna na ratsa ta daya kira kanshi angon ta, ga hannun ta dayake murzawa a hankali, karbe hannun ta tai ta canja mazauni tana turo baki, ita a dole fushi take,Mama ce ta shigo dauke da kofi a hannun ta ta aje mai a gaban shi ta samu wajen zama,” Mama kin ga wannan yar rigimar ta turo baki, lallai akwai magana yau” Aaa ni kam ba ruwana ina gefe ba a shiga tsakanin ku ai ku” komawa yai kusa da ita ya dago kanta” Juwairere na me ya faru?”to ba ga shi nan ba wai Juwairere???? ni Allah bana son sunan nan,gaba daya ka sa Nafee na tsokana ta, Kullum ta ganni sai ta hau ce man Juwairere ta qarasa yar kwallar ta na fita baki a gaba, dariya ta bashi ba kadan ba wauta da shagwabar ta na burge shi sosai” ki kwantar da hankalin ki princess ba zan qara fada ba inshaa Allah sai munyi aure” harara wasa ta mai tare da jin kunyar kalmar aure da ya ce ta fita a dakin da gudu tai tsakar gid tana dariya, kada kai Mama tai tace “Allah dariya kuke ban yaran nan ba kadan ba kun iya wauta” Mama kenan ba wauta bane da gaske auren ta nake son yi in Baba zai ban ita, itamma ba Abujan za a kaita ba, dan dalilin zuwana kenan, naji an kawi kudin wadan can marasa kunyar” hmmm haka ne Jabeer amma kasan ni ba ruwana da wannan kalmar ta yan unguwar nan ko, na cewar yaran gidan nan YAN ABUJA NE ba zasu auri kowa ba sai dan can, in su suna fda kuma sun yarda zasu aure su ni ban fada ba kuma ban ba yata izini ba , in da rabon can ne gidan auren ta yake Allah ya zaba mafi alkairi in ba can bane ni ko ina albarka na ke nema mata kullum” haka ne Mama, Allah ya shige mana gaba” Jabeer dan gidan Yaya Balarabe ne ya dawo daga bautar qasa inda aka tura shi illorin, ya kammala karatin shi bangare kasuwanci, to a yanzu haka yana taba saida jakunkuna da takalma, ba wani arziqi ne da shi ba, yayun ta sun so matuqa ace me kudi ne da sun aure shi ko dan kyaun shi, amma inaaaa talauci a cewar su ya dakushe tauraruwae shi.