YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Page 19:

Da asuba yau Salma ta tashi da matsanancin ciwon kai da mara, in da Talle hankalin shi ya tashi ba kadan ba, kar ‘Yar mutane ta mutu a hannun shi, shi dai Allah ya gani ba wani son ta yake ba dama, kuma shi ba zai yarda ya kashe ‘yan kudaden dayake tarawa ba in sun rabu ya baro wata sabuwa ya dirza ba, tabbbb yaushe ma zai yarda ya taba bayan neman auren ma ya kankama, kuma yanzu haka dama wa’adi ya debar mata,” kawai bari Alhj ya fita nan dai da Kano na auna ta gida, nace sai nazo ba shikenan ba” yana maganar zucin nan ne ya ji Alhjn na kiran shi, da gudu ya fita, ” To ga wannan a kula da gida, ni zan tafi , wannan karon xan dan kwana biyu gaskiya wataqila bam dawo ba, dan amaryata kasan na fada maka ta samu qaruwar diya mace, so ina ganin zan dan jima kadan fiye da yanda aka saba, a kula da gida, kar na dawo na ji shigen labaran dana saba ji, ba zamu kwashe da kyau ba Talle” gyada kai yake kamar qadangare, Allah Allah kawai yake ya tafi ya kai Salma tasha ya dawo, kar ta mutu a hannun shi, ” Allah ya kiyaye Oga ba zaka taba samun wani labari mara dadi ba” daga kafada Alhj yai alamar” ruwan ka” yana fita bayan ya rufe gate din ne ya koma dakin da gudu, samu yai ta dan samu dama ba kamar yanda ya barta ba, ta fito daga toilet da alama amai tai,” ke hada kayan ki yau zaki ganin gida” cikin kaduwa da murna a gefe kuma kunya da tashin hankalin da wanne ido zata kalli su Juwairah da Mama Bilki? Uwa uba Goggon ta, tace mata waye mijin ta, driver? Ko gate man? Zubewa tai a katifa,” Nikam Sweet na fasa ba yanzu ba ka bari na murmure, sannan mu dan samu kudi, ko a haka zan tafi ai sai a zage ka” “a zage ki dai yo ni meye nawa in zaki miqe ki miqe ki kwashi dan abinda zaki iya dan kin ga ni daga yanzu ma barin gidanan zn ko kin dawo ba ganina zaki ba nima na bar aiki anan daga yau, dan na kwashi rabona wajen Alhj, qauye zan koma, na ji da iyalina, kuma ba yanda zaki ki san qauyen mu nan ma tinda ko sunan baki sani ba, ba kuma ki san hanyar bama, so in kin tafi ki manta mai suna Talle, ko Alhj Mansur da kk taba aura, ki manta kin sanni, sai dai in kin tashi tuna ni ki min godiya a ranki na sama maki hanyar zuwa ABUJA, harda qauyen ta ma, dan haka ga wannan” takarda da kudi dubu goma cass ya miqa mata, a zaunen ta daskare, bata gaskata me ake fada mata ba sai da taji tsawar shi yana maimaita mata da kuma bata umarnin tana bata mai lokaci zai fita ya gudu shi,( qarya yake mata ba inda zai gudu kawai sanin bata ko san sunan inda suke ba shi ya sa shi fadin haka, baya son ta yi tinanin dawowa ma) miqewa tai da taimakon shi, take ciwon kan ta ya dawo sabo, wani jiri ke diban ta, haka ta gama komai, ko nace ya gama hada mata komai, yana bata a hannu tana riqewa, idon ta a tsaye, hawaye na zuba, haka ya gama ya sata gaba ya kulle qofar ya dau wata jaka dan tsabar ya raina mata wayo ta zaci tare zasu bar gidan, mota suka dauka ya saka ta suka bar gidan kifa kanya tai a cinyar ta tai ta kuka sun isa ta tasha a bakin tashar ya sauke ta yai gaba ko waiwaye bai ba, a haka ta samu ta isa bata ko magana, in da taji ana kiran Kano nan ta isa ta shiga wata mota sauran mutum biyu, tana shiga wata arniya ta shiga itama, sunayen su aka basu su rubuta, amma ita tai shiru, kudi suka buqata ta miqa masu ko da ya qirgi kudin shi ya miqa mata sauran ta nade a hannun ta, tafiya sukai ta awanni haka ta zauna idon ta ya bushe qayau, har suka iso kano, adaidaita sahu ta dauka ya kaita har gida ta miqa mai kudi ya bata canji, har tai gaba ya bita ya miqa mata a hannun ta, yai gaba, yana ” Allah ya kyauta” shiga tai ba ko sallama, Goggo Sarai tana zaune hakimar ana kada qafa akan kujera, tana hango Salma sai da ta kusa tintsirawa, da gudun ta zani na warwarewa tana gyarawa ta taro ta” Lafiya ? Me nake gani haka? Ina mijin naki? Daga wace qasar kuka dawo haka? Fashi akai muku? ” duk wannan tambayoyin ne jere a bakin ta tana qoqarin shiga da ita daki, har Mama Bilki zata fita, Abba ya riqe ta, yace bassu, ni na je , yanzj da kinje kin ja magana,cewa za tai gulma ta kai ki” ” To Abban su Allah ya jiyar da mu alkairi” ” Ameen” fita yai ya isa dakin, zaune Salma take, idon ta na kallon waje daya kawai, ko qiftawa bata yi, kukan kuma ya tsaya, tambayar duniya taqi magana, Goggo banda kuka ba abinda take, ” Subhanallahi, me ke faruwa ne, kin saka yarinya a gaba kina ta kuka haka? Ke Salma ki mana bayani, me aka miki, ina mijin naki kuma? Daga ina kk haka?” A sannan ne Salma ta saki wani kuka mai cin rai, ta dakko takardar ta miqawa Abban nata, dan yanzu haushin Goggo take sosai, duk ita ce bata basu tarbiyya mai kyau ba, uban su na son basu ta musu hudubar shedan,ta hana su saurara, wannan wace irin rayuwa ce haka, Salati sukaji ya sake ya aje takardar ya zauna” Malam me ya faru? Ku sanar dani ko hankalina ya kwanta” ” mijin nata na can garin ABUJAN NE YA SAKE TA SAKI UKU” dora hannu a ka tai ta kurma ihu, ta hau jibgar Salma tana” Shegiyar yarinya me kk mai ya sakon ke, kk kama asara haka, mutumin da kuka fita qasar waje? Kuke shaqatawar ku cikin jin dadin rayuwa, ki zalunce ni ki zalunci kanki, ki sa ya sako ki, da dukkan alamu ma ciki ne da ke, amma ba zaki bar dan ki ya taso cikin jin dadi ba” kalmar ciki ne ya razana Salma kenan, tasan Talle ya mata illa, dan ko giyar wake ta sha, a yanda ta san waye Talle ba ma zatai gigin ta haihu ba ta kai dan ta qayen su, ai kamar yanda yace sun rabu ta manta da shi hakan za tai,ture hannun Goggo tai a jikin ta ta je gaban Abban ta ta durqusa,” Abba na ka yafe min, ka ji tausayi na ba dan halayyata mummuna da nai a baya ba, ka duba girman Allah da soyayyae da da iyayen shi, ka yafen, ka tausaya ma abinda ke cikina in ya tabbata ina dauke da cikin kenan, karkai fushi da mu, ka bamu wajen zama a gidannan karka kori abinda zan samu, zan wahala ta hanyar halal na kula da abinda Allah zai ban, amma kar ka ce za a sake daga zancen uban dannan na gama shafin shi, sabon shafi nake son budewa” kuka ne yaci qarfin ta sosai, wanda yasan ya Abban su hawayen tausayawa diyar tashi, yarinya fara mai kyau duk ‘ya’yan shi Juwairah ce kawai ta fisu komai, amma Salma na bayan ta, dubi yanda ta koma, ga qananan shekaru, har yau bata rufe ashirin din ba, daga ta yai tsaye ya rungume ta,aiko kamar jira take,dama she needs a shulder to cry on, ta rasa, for so long, ga strong and loving arms nan sun huging din ta, ya bazata ji gwarin guiwar fidda komai ba, kuka Abba ya barta tai har saida ta daina da kanta, yasan ta fidda koma meke cin ta a rai, zaunar da ita yai, yace ina zuwa, Mama Bilki ya kira bayan ya fada mata abinda ya faru, shigowa tai taje kusa da Salma, Salma na ganin ta taje da sauri ta rungume ta, tana neman gafarar ta, Mama Bilki yafe mata tai, ta zaunar da ita, ” fada mana me ya faru” a cewar Mama Bilki, da gudu Goggo Sarai ta iso gaban Salma” yi shirun ki wannan sirrin mu ne karki magana a gaban maqiya” wani kallo dukkan su suka watsa mata, kowa da irin nashi, Salma magana ta fara, ta sanar da su komai da ya faru tin daga tafiyar ta har dawowar ta yau din, kuka sosai Abba keyi duk jarumtar shi, ya tausayawa diyar tashi,Mama Bilki ma haka, Goggo Sarai ga tausayi ga kunya itan ma kukan take, Salma ce ta juya ta kalle ta” Yanzu Goggo a wanne hali su Adda Suwaiba suke? Baki sani ba, kawai suna aiko maki da kudi kina ajewa, Goggo baki san ina ne Abuja ba, da tin tasowar mu kk kimsa mana son ta, yanda kk saka mana son abun duniya da hutu, da haka kk sa mana son ku kadai da muku biyayya da anyi yaran kirki,amma baki wannnan ba ba a kaiga dasa mana tsoron Allah da son Allah da ma Annabin rahama biyayya akan saqon da ya zo mana da shi ba, Goggo kin ci amanar kiwon da Allah ya baki, Abba na qoqari akan mu kina rusawa, ni yanzu ba zan zauna anan dakin ba, Mama Bilki ina riqon arziqin komawa wajen ki na zauna, dan tabbas nima ina zargin ciki garen yanzu watana kusan hudu bana ganin al’ada ga yawan ciwon kai da mara, sai zazzabi danake yawan yi, ki koyan dukkan irin tarbiyyar data kamata nima inna haifi nawa na basu,ba irin wannan tarbiyyat mara kyau da ma’ana ba” Goggo Sarai ce ta kwade mata baki,” dan uban ki to ki dauki haihuwar ki da nai ma kice ita ce tai maki mana? Ku tashi ku fice man a daki gaba dayan ku bana buqatar kowa, yaran da suka san daraja ta da qimata za su zo su kula dani, dama ke tinda akai auren me kk tsinanan, baki tsaya kin nemi kamar na yan uwan ki ba , me kk samo banda wahala? Sai ku tattara ku je can, jikoki kuma yarannan biyu ba zan rasa su da ciki ba yanzu haka, dan ba zaman banza na aika su ba” miqewa sukai Mama na mata addu’ar shiriya a ranta, dakin ta ta kai Salma, abinci ta dakko ta bata, kamar mayya haka ta hau shi da ci tana hawaye, tana gama ci ta sha ruwa sai bacci, Mama Bilki ce ta gyara ta, tana tsananin tausayin ta, Abba sai godiya yake mata da sanya albarka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button