YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Su kuwa yan Abuja ana can ana shanawa, hanakali kwance, suna zaune ana kasafin sassan jikin su………
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????

           BY HAERMEEBRAERH

My Saerwwaermaerh
Ke ta daban ce Haermeen Hamma na son ki,

Billy shantali (Billisiou)
Hassana D
Ummul
And dikkan Surukaina na Tabital fullaku, har da surukar zamani????????duk ina gaida ku ba adadi, ur love is daban in my qalbi???? ANA MUGUN TARE.ME LOVE U XOXO❤

Page 20:

Alhj Kallah, Alhj Salihu, Oga Zaks, su ka dai na iya ganewa a qaton table din da yake kewaye da manyan Alhjzawa, wanda a qalla zasu kai ashirin , gaba dayan su da shigar tasu ta red and white, with a little black on it, kowa muzurai yake, irin nima wani shegen ne????, Oga Zaks ne yai gyaran murya, ya ci gaba da magana” A a Salihu, wannan qorafin naku bai karbu ba, kun san qa’idar qungiya, an baku dama, ku kadai na bawa damar da ban ba kowa ba, saboda koba komai ana qaruwa da ku sosai, amma wannan karon, u guys disappointed me so much, that u have to pay for what u did, dan haka , nake baku imarni ba shawara ba, u go back and bring ur wives here, dole ne a yanki abinda ake buqata daga wajen su, ba dan komai ba kuwa sai dan cika sharuddan Dodo, dan haka na baku nan da kwana uku, kuje ku gama sallama da su ku kawo su” miqewa yai cikin izza yai hanyar waje, guards din shi na biye, Alhj Salihu ne ya kife kan shin a table, dan a qashin gaskiya ya fara son Suwaiba duk da wautar ta da gabuntar ta,Alhj Kalla na kula da shi, taba shi yai akan su tafi, miqewa yai da kyar, suka fice , ana ta yan gulmace2 , ko ina ba a raba mutane da gulma????bayan sin isa gidan Saudat ne, suka shiga inda suke tattauna matsala irin haka, suka zauna, Alhj Kalla ne ya fara magana, dan ya kula in bai ba Alhj Salihu ba zai ce uppan ba, ” Salihu ni ban ga abin daga hankali a maganar nan ba fa, duk da ni kaina a yanzu haka na fara son yarinyar can,koba komai duk matan da muke hulda da su yaran nan na kula suna da na su sirrin daban a jikin su, ga yarin ta ga kyau, amma kasan bijirewa Oga Zaks na nufin qarewar arziqin mu, nikk dana talauce gwanda na aikata abinda yake so, mu kaisu kawai, nono ne kawai za a yanke, to meye? Naga dai ana ciwon cancer ma a yanke masu nan kuma su rayu” ” bazaka gane ba abokina, in ba wajen a ina mutum zai na hutawa? Kai ni fa bari kaji ba zan iya bane kawai, duk sokoncin yarinyar nan ina son ta, dan in tare kk da ita ta bara maka wani haukan sai kaji kamar kaita zane ta shegiya, amma tayi akwai zuma, banjin zan iya rabuwa da ita, yanzu ni dai shawarata shinr suje gida kawai su ga gida na kwana daya ko biyu su dawo muga ya za ai, tinda kaga bai kamata har in ma mutuwa za sui tsohon su bai gan su ba, dan ta uwar su ita tajiyo bamda case da ita ni” ” haka ne kayi gaskiya, to bari na fada masu kawai gobe su shirya zasu gida ko ya kace, dan da kaina zan hada mata kayan ta, amma ka tashi ka tafi gaskiya dan saina dana sosai kan ta tafi, bamu san ya abubuwam zasu kaya ba” dariya sukai suka tafa, ” shegen sama nima ba ri na hanzarta” aiko hakan akai washe gari da asussuba suka dau hanya kowa da drivern ta dan wadata, ga wata mota nan shaqe da kayan arziqi na bin su, haka suka iso gida cike da doki da murna, suna shiga gidan, Salma suka hango kanta akan cinyar Mama Bilki tana mata kitso, a kwance, kamar wata jaririyar ta, ” Kan ubancan, me nake gani haka ni Suwaiba? Yaushe gidan ya koma haka? Da jin muryar ta Salma ta miqe da gudun ta tai kansu, tana ihun murna,” Goggo fito ga su Adda sun zo, Mama kinga su Adda sun zo, ina Abba? Abba fito ka ga ikon Allah su Addana ne a gidan yau” suma basawa sukai aka ci gaba da murna amma cikin ransu akwai tambayoyi sosai, dakin suka shige tana ta kwasar bacci, tashin ta sukai, ta miqe tana mittsika ido, aiki tana wartsakewa ta gansu, sai kukan dadi ya kamata, ta ko hau kukan murna suma sunayi, Abba ne ya lallashe su, nan fa aka hau gaishe gaishe” Ayyyuririri, kai shiyasa nake son Allah, akwai shi da biyan buqatar bawa, dubi yarana , san kowa baqin cikin marashi, ga kudi ga kyau, ga hutu, naji dadin zuwan ku yarannan, ya mazajen naku?” Cikin murmushi da dagun kai an gama kumbura masu kan suke amsawa” suna lfy suna gaida ku, ga abubuwan kayan abinci nan da kudade da suka aiko a baku ke da Abba” cikin murna kamar zata kifa ta dafe kudin dika har na Abban nasu, shi ko ko wajen bai kalla ba, ya masu godiya, Mama Bilki ce ta shigo dauke da ruwan Pure water a plate ta doro masu sanyi ta kawo masu, ajewa tai ta zauna a gaisa” wai ni shin gaisuwar nan dole ce ne, a bar yara su huta, kuma in banda abin talaka, duba fa wa zai sha wannan ruwan, dan Allah kije an yafe Allah ya bada lada” Goggo Sarai ke maganar nan, cikin shewa suka hada baki” Hahaiiiiii Casssss sai Goggo, ashe ana nan ana ci gaba da gashi, Allah sassaka to” dariya tai cikin isa tana wani daga hanci, Mama Bilki ce ta tashi ta ja hannun Ammar da ke son shigowa sukai gaba, Salma ma tashi tai rai bace ta fita” wai Goggo me ke faruwa ne me nake gan? Salma da waccan matar?” Abba ne ya basu labarin komai, nan da nan suka hau kokawa yar uwar su wahalar da ta sha, sannan ya qara masu da hukuncin da ta yanke, anan ne ransu ya baci sosai, suka kwala mata kira, bayan ta shigo ne suka balbale ta da fada kowa da abinda yake fada, sai da ta tabbatar sum gama ta miqe tai waje ba ta tanka ma kowa ba a cikin su, da bala’i Suwaiba zata bita ta daka Goggo ta hana ta, “aini yanzu na cire ta a Yarana nima, taje can ta qarata, ina da ku kun ishen rayuwa, kuma yanda kukai jan nan da alamar kuma kuna dauke da ciki, dan haka jika ne nake matuqar kwadayi yanzu a duniya fiye da komai, taje tai ta fama, ita ta sani, naku sun ishen zaman duniya dai ba na qiyama ba” kallo suka bi junan su da shi, take Saudat ta fada jikin Goggo tana kuka, Suwaiba ma idon ta ya cika da kwalla sosai, “Adda Suwaiba akwai abinda na si fada maki tin da na qi dan nasan halin ki tona mu zaki su kuma su kashe” cimin zaro ido Goggo tace” Suwa….. suwaye zasu kashen ku?” ????” mazajen mu Goggo yan qungiyar shan jini ne,na gano hakan da jimawa, yanzu haka bamu da mahaifa da ni da Adda” wani mari taji guda biyu a fuskar ta, daya na suwaiba daya na Goggo” dan ubanki sharri kuma zaki masu, mutanen da suke kasuwanci a qasashe ko ta ina, arziqi ya wadata ya bunqasa shine zaki ce haka, so kk ki dawo kema ki xauna ki jamin asara, na haifi ya kamar ki da zan samu dukiya ki dankwafe kanki? To ki bude kunnen ki kiji, ko ya ake. Ciki gobe zaku koma va zan lamunci asara ba” cikin kuka ta rarrafa wajen Abban su,” Abba ka yarda da ni, wallahi gaskiya na fada, yan shan jini ne, naji da kunne na” ” na yara dake yata, dan baki taba fadan hakan ba kuma da dikkan alamu akwai gaskiya a zancen ki, wannan kudin nasu yayi yawa” ” Abba ya zaka yarda da wannan maqaryaciyar ? Qayra ne fa kawai dan sun taba dukan mu sau biyu, shine fa ta qullaci abun take son ta gudu, to in ke bazaki koma ba ni xan kma dakina” ” yauwa yar albarka, ai nasan in kowa zai juyan baya ke kin haifu” tashi akai inda kowa zuciya ba dadi, Saudat ta kafe bazata koma ba, inda Suwaiba tace ita zata koma, Salma kuma suna jiyo komai,hankalin ta ya tashi amma tasan bata da say a wannan kamarin,Mama Bilkince ta shawarce ta akan ta musu addua kawai, hakan akai kuwa ta kwantar da hankalin ta suka hau yankan farce bayan sun gama kitson.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button