YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Ina qara bada hakuri dai dan Allah masu son Novel din nan ta PC ba zai yu nai ta sending from d begining ba, i am so sorry, kui man hakuri zuwa dan kwanaki kadan zan kammala dika na mayar Document, inshaa Allahu, Na gode sosai,Love u from qarqashin heart????, u guys ar awsome ❤
Page 23:
Gobe ne ranar da Jabeer zai dawo, waya suke da Juwaireren shi, gaba daya ta shagwabe ta susuta mai lissafi, ji yake kamar ya dawo a daren, ko da fuskar ta ne ya kalla, ya san zai ji nishadi, kwantar mai da hankali tai akan gobe suna tare, kar ya damu, tina mai tai akan yai addu’ar bacci kafin ya kwanta, sukai adduar tare suka kashe waya, bayan cika juna da “I love u”, da sukai bacci ne a bangaren Juwairiyya da Jabeer mara dadi, don tin da ya tafi hakan ne , baccin baya masu dadi ba junan su a kusa, a haka bacci barawo ya dauke ta bayan juye2 da ta sha, da sassafe ba yan tayi sallah, tayi abubuwan da suka zama na al’adar ta da safe kamar yanda kuka san Juwaireren Mama, tashi tai yau ranat gyaran lambun ta ne, taso ta bar shi tai gyaran gida tai ma Yah Jabeer din ta girke2, amma ta saka diguwar riga gajera, mai hannun vest, ta dau kayan gyara lambun ta taje, ta tattaba abubuwan da suke da buqatar gyaran, Juwairah akwai saurin aiki akwai kuma biyan buqata( ba a son mace ta kama aiki daya taita fama da an xo aga ba wani abun kirki da ta qulla bayan kuma ita a qasan ranta aikin nan take bil haqqi, gani take tana ta faman aiki amma an kushe ta, to yar uwa kin kama aiki daya kina ta yi kuma wataqila ba ma wanda ya fi zama dole ba, kin bata lokacin ki ya tafi baki qulla komai mai amfani ba, kinga in kina da miji mai mita akan komai dole zai magana, dan haka ana son mace mai zafin nama, mai saurin aiki, kuma tai aikin da kyau) tama gamawa ta wanke qafa da hannu ta shiga daki, ta hau gyaran ko ina, ta canja bedshit, ta dakko wancan ta fito da shi ta gyara palon ta, ta canja mazaunin kujerun ta, sallamar Nafee ne ya sa ta dan tsagaita da aikin ta, shigowa tai” haba matar Yayah ai sai ki kirani, da wannan tsohon cikin kk aiki irin haka, wata bakwai fa, kun shiga na takwas, ki ja mana aiki, habaa gaskiya banji dadi ba” ta fada tana turo dan bakin ta wai ita ba a kyauta mata ba, murmushi Juwairah tai ta kama kafadun ta” kar ki yi fushi da ni ‘Yar qanwata, taho ki taya ni, na dauka kina taya Innarmu aiki ne, shiyasa ban kira ki ba, tayata aiki ai yafi nawa” murmushi sukai tare suka ci gaba da aikin, bayan sun gama canja fasalin wajen ne, suka debo ruwa da tsumma nan ma suka goge ko ina, kitchen ta tafi ta barma Nafee ta qarasa nan din,taje ta mai na shi kyaran sosai kamar Jabeer din zai leqa in ya fara shigowa, bayan ta kammala da nan ne ta wuce toilet, Nafee ce ta bita ta amshe wankin toilet din , bayan sun gama ne aka fara gyara tsakar gidan, in da yake anyi siminti, nan wanke wa Juwairah tai qasan kuma suka share” wai nikam me zaki dafa mai ne naga baki fara batun girki ba” His favorite u know, da kudin da ya ban jiya nai aike kasuwa an siyo man kwai, nama dankalin turawa, da cabage sai carrot da green beans kindan bak da su a lambu, sai flour ina da mai, an siyon yan kayan qamshi da maggi, dan wake zan mishi, kin san shi a duniya na kula yana son abunnan” ” wai sosai ma kuwa, bakigan shi bane yana satar danwake a tukunyar Innar mu da dai kin sha dariya, Innar mu in ta kama shi sadaf2 take tafiya ta damqe hannun shi da ludayin tsamar danwaken, yai ta ihu ta qi saki” dariya sukai tayi sosai tinawa da wannan kabarin, miqewa sukai suka fara gyara dankalin, suka yanka veges harda na lambun nata, ta debi dan alayyahu kadan, da albasa mai ganye, suka gama yankawa sai ta soya dankalin nan ta dakko dafaffen naman ta da suka yanka qanana ta soya sama2 ta aje gefe, sannan ta rage man suyar ta dakko jajjagaggen kayan miyar ta, da ba timatir sosai guda biyu kawai tasa ba manya ba suma sosai, ta saka da tafarnuwa da kayan qamshi ta soya ta saka maggi da dan gishiri, sannan ta dakko wannan veges din ta zuba akai bayan ya fara soyuwa, ta juya suka tirara, sai ta juye akan wannan dankalin da daman, ta juya su, suka hade, dakko dafaffen kwanta tai shima bayan ta bare ta hada da shi ba tare da ta yanka ba, ta juya su tare,flask din ta ta dakko ta zuba wannan hadin ta rufe ta rage masu nasu, dakko flour tai naga ta dakko wani gari” Matar yayah wannan garin meye?” ” to tambaya an fara ne, garin wake ne na markada da yar dawa kadan, sai alabo, na niqo su shine zan hada da flour din yafi dadi sosai” ” Auuuuhooooo, to ai sai ana yi ana tambaya ko kinga laifina?” ” Aa aa matambayi baya bata ai” murmushi sukai ta debo kuka, mai dan yawa yanda zai santsi, ta dakko ruwan kanwar ta, ta zuba ta hada da wani ruwan dan bata son ta cika kanwa da yawa, ta kwaba yai laushi kwabin, ba tauri sosai ba ruwa, haka ta kwaba ruwan na tafara ta fara jefawa qanana, dan yafi dad, bayan ta gama ta tsame a ruwa mai kyau ta hada mai nashi a flask, ta miqe ta barma Nafee ta qarasa ita timatir daya ta dakko nunanne, ta fada mai sugar a tsakiya bayan ta yanka, ta hau goge fuskar ta da shi, sai da ga baya kuma ta dau rabin ta saka xuma ta goge fuskar shima, nan da nan wani duhun murhu da rana ya bace fuska ta dau kyalli da kyau, bayan ta gama kuma ta dakko lallen ta, ta saka mai man kwakwa kadan ta kwaba shi, ta hau murge jikin ta duk inda hannun ta ya kai musamman fuskar ta, kafin kace me Juwairere tai kamar ba ita ba,” tab lallai Yayah na shan dadi aradu, yau fa ba ranar gyaran jikin ki bane, bama ki dade da yi ba amma ji yanda kk koma kamar wata tauraruwa” ” Nafee kenan, ai ita mace ana son in mijin ta yai tafiya ko na kwana daya ne ya dawo yaga ta canja kawai ko ta ina, balle wannan da kk gane we ar talking about Yah Jabeer, My love, everything” dariya sukai, Nafee nata tsokanar ta ta gama ta shiga wanka, shigar da yake matuqar so tayi ta dakko kayan ta fara sakawa, doguwar rigar material ne aka mata irin na masi ciki, an daure sama kamar bra akai mata sai hannun ya zamana a wuya aka daure shi, cikin nan ya sha mai da gyara, sai kyalli yake gwanin sha’awa, sai dogon wando da akai mai fadi sosai ta zura, ta dakko kayan gyaran gashin ta, ta tsaga daga gefe, ta kwantar da shi, ta daure in a ponytail style, qamshi kam ranar kamar an barin turare, fuskar ta daga powder sai lipstick, ta gyara girar ta, ta saka kwalli,( kwalli na da matuqar tasiri ga mace, macen da ta saka kwalli ta iya kallo ta yi a rayuwa, in baki iya ba koyi ki fara)dogon hijab ta saka, tai sallar magrib ta zauna, tai azkar din ta, ta fara karanta qur’ani, ana kiran sallar isha’i ta tashi ta fara, Sallama yai ya shigo, yana ganin tana salla ya aje kayan shi yai alwala shima ya tafi masjid, tana idarwa qara gyara jikin ta tai duk da ba abin da yai, ta qara turare, ta gama, dauke kayan da ya shigo da su tai, na ajewa a kitchen ta kai ta fito da kayan nashi,masu datti ta fitar wamda bai amfani da su ba ta mayar wajen kayan su, sai wata leda da bata taba ba ta aje a gefe,daga alamu tsaraba ne, ruwan wanka ta je ta hada mai mai dumi, ta dawo kenan zata zauna taji shi, bayan qofa taje ta maqale tana ta dariya qasa2, shigowa yai yana ta dube2 bai ganta ba, sai da ya kama qugu sannan yace” Juwaireren Mama ko ki fito ko na zauna a qasa naita kukan rashin ganin ki, in an shigo nace baki son gani na ne” kan ya rufe baki yaji ta mai wata iriyar runguma ta baya wadda tasa shi fidda sautin da bai san ta ya akai yayi shi ba,( rungume mutum ta baya akwai yanayin da mace ko miji zasui ya zama ba wata runguma da ta fita dadi, ana yin ta ne ta hanyar zuro hannu a hankali ka zagaye mutum sai ka ja shi baya cikin shauqi ka manna shi da jikin ka) juyawa yai gaba daya ya daga ta sama, suna ta dariya, kisses kam kun san ranar an yi bari da ruwan su, zaunar da ita yai a cinyar shi, yana shafa cikin ta, yana ma cikin surutu kamar wanda yake hira damutum babba, dariya kawai take yi ita kam, ” sannu da zuwa hasken cikin gidana, tin da ja tafi kaga daya gidannan duhu ya mamaye shi, yau haske da ya bayyana daban ne, na gode Allah da ya ban kai a matsayin miji, Yah Jabeer ba zan iya rayuwa ba kai ba, i missed u so very much” ta qarasa tare da qanqame shi tana hawaye, dagota yai yana jin wani sabon qaunar ta na ratsa shi, dan yasan she meant every word, ” Hushhh Husshhhh my princess, ki daina kuka, Yah Jabeer na Juwaireren Mama ne ita kadai, bana fatan na wayi gari baki kusa dani, u ar my happiness, i cant do without u, u ar everything that i ever wanted in my life, so don’t be scared of loosing me, nine ya kamata naji wannan tsoron, amma ba zan damu ba dan nasan zuciyar ki, da ruhin ki , da gangar jikin ki nawa ne” wata runguma ta qara mashi da ta saka shi jin dadi sosai, daga shi tai ta ja hannun shi zuwa wanka ta taya shi yai wankan yai brush suka fito ta shirya shi bayan sun gama ne kan shimfidar da suke cin abinci ta jawo hannun shi ta zaunar da shi, shikk binta kawai yake kamar raqumi da akala, dan waken ta fara zubawa a gefe, wanda har wani kyalli yake dan santsi sannan ta zuba mai wannann hadin da tai na dankali, zobon da ta dafa da abarba, da cittta kaninfari, kai da kayan qamshi dai da suka dace dika, ta saka harda cocumber, ta sa sugar, ci yake yana lumshe ido kawai, yana wani gurnanin magana amma ba a ganewa me yake fada, daukan zobon da aka saka a randar sanyi yai dan basu da fridge yai ya kurba, saurin bude idon shi yai sannaj ya mayar ya kulle, ” Yah menene, yayi daci ne jo wani bu?” Ta fada tana zaro ido waje dan a tinanin ta ko bai mai bane, ” matso kiji me yai” yana dan yatsina fuska, ita kuma sai ta danji zuciyar ta ba dadi, saboda gani take ta bata xobon garin iyayin mai hade2, dan ba ta san dama ana saka cocumber ba qirqira tai, matsawa tai kanta a qasa, ” sai kin rufe ido zaki iya shan wannan abun, matso sosai na baki da kaina kiji ya yai” matsawa ta sake yi, ta rufe idon, jitai ya kama lips din ta yana masu wani salon da ya sa ta magana a qasan maqoshi, saida ya dade kan ya sake ta, ta kasa bude ido, dan wasu taurari ke mata yawo a kai” bude idon mana Princess, ni ba mai kudi bane bare na maki kyautar wannan kayan dadin da kk ban yau, amma na san i will make u feel something special, with every part of me” daukr ta yai sukai daki, zan bisu aka bugon qofa,nace ba sai an karya ma Hammana hanci na ba, zan tafi malamai????????????????????
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ???????? ‘ YAN ABUJA ????????