YAN ABUJA HAUSA NOVEL

BY HAERMEEBRAERH
Page 24:
” Adda Saudat dan Allah ki ban dubu daya mana ina son in dan ja jari ne ko ba yawa, xaman haka baya min dadi,ke ma kuma ya kamata kafin kudin hannun ki su qare ki kama wata sana’ar saboda kin saba yanzu da kudi, randa kk da buqatar su kk rasa ba qaramin damuwa zaki shiga ba” tinani Saudat take mai zurfi, can ta nisa tace” gaskiya kin ce wani abu kema, zan baki dubu biyar ki ja jarin, ni kuma zan fara kasuwanci ta waya da naga qawaye na da nai a whatsapp da facebook sunayi, ana samu in ka riqe amanar mutane, sai kaga ka samu riba mai yawa kana daga zaune” ” yauwa Adda, sannan ina son nuna maki kinga Mama Bilki mace ce mai kirki, tana matuqar son mu, sai dai tabbas tana kishi da Goggo, wanda wannan dole ne a zaman kishiyoyi dama,mu sai mu kau da kai akan wannan, tinda iyayen mu ne, ba ruwan mu da hurumin su ta wannan bangaren, ya zama wajibi mu masu biyayya dikkan su, su a matsayin iyayen mu, itq a matsayin matar Abban mu” shiru Saudat tai domin maganar qanwar ta ta yau tana shigar ta, amma akwai nau’i na girman kai, da kishi a zuciyar ta, ” hmmmm zan duba na gani” ta miqe ta dakko mata kudin ta bata, akan idon Goggo kuwa, ” habaaaa Salma ai innice ke yanda na canja uwa, yan uwan ma canja su zan, auhoooo ba zaki iya canja yan uwa ba saboda kin same su su masu arziqi ne ko? Zaki roqa za a baki ko” ” ni fa Gogga ba haka bane, ya kamata ki bude idon ki ki gane inda gaskiya ta dosa, ki daina rufe idon ki akan abinda bai kamata ba” ” rufen baki sallamammiya kawai, an yi asiri da tuggu kala2 an rabani dake, to kije nima na huta da dawainiya, da dan wani da zanyi” juyawa tai tabar wajen Salma kuwa cikin qunan rai da baqin cikin halayya ta uwar ta ra shige dakin Mama Bilki, wadda taji komai, fadawa kan cinyar ta tai tana kukan takaicin hali irin na uwar tasu, shafa kanta kawai Mama Bilki take, bata furta mata komai ba,” Mama ni fa ba kwadayi ne ya sa na tambayi Adda Saudat kudi ba, na tambaye ta ne naga ko tirare bani da shi, ga shi yanzu sai da Alimun ko lemon tsami nake amfani a madadin tirare, ba dan komai ba sai babu da take neman ta min yawa,amma in ina sana’a kudin zasu taimakan wajen kula da abinda ke cikina, shine Goggo take fadan maganganu marasa dadi akaina” ” hakuri zaki Salma uwa ba abin wasa bane, dole mui mata biyayya in ba inda za a sabawa Allah bane, dan haka ki hakuri tin da kin samu jarin yanzu me zaki na yi na siyarwa?” ” Mama Bilki ni da ina son na fara saida Meatpie ne, naga kina da injin yin taliya, kuma na kula kayan flour ana cinikin su, in ba su ba ban san me zan iya yin sana’a akai ba” ” hakan ma shawara ce mai kyau, Allah ya sanya albarka” ” Ameen mamana” kwantar da kanta ta sake yi a jikin ta ita kuma tana shafa gashin ta.
Yau kusan sati daya da kwana uku kenan Suwaiba na kwance tana jinya, Alhj Salihu dayaga zata farka ya danna mata allurar bacci ta koma, ko ya shaqa mata wata powder ta koma baccin, a haka tai wadannan kwanakin, zai mata wanka, zai canja mata kaya,sannan ya saka mata drip dan tana samun abinci ta jikin shi, ya zama babban likita kawai a cikin gifan shi, a haka sai da ya kula wajen ya warke tas sannan ya kyale ta da allurai na bacci da yake mata, yau ne ranar data bude idon ta tana kallo. Wajen kamar sabon waje aka kaita, a hankali ta bude idon gaba daya, akan na Alhaj Salihu ta bude su, kanta ne taji ya mata nauyi,kwantar da kan ta sake yi a pillow, jikin ta a mace ta bude baki tai magana da kyar” Me ya samen Sweet? Me yasa nake jin zafi sama2 a qirjina kamar naji ciwo?” ” Shiiiiiiii karkina nagana sosai, hatsari muka samu a gidan, yan fashi ne suka suka shigo, kina bacci suka yanke maki Nono, ni kuma dana dawo na ganki kin suma shine nake ta kula da ke” a firgice ta miqe daga kwanciyar,” an cire man nono?” Ta fada tare da zaro ido waje wanda suka cika da kwalla mai dumi, ” na shiga uku ni Suwaiba,ya zan rayu ba mahaifa ba nono, gaba me zan rasa kenan, Alhj na fa san kai ne sanadin rasa nono na Saudat ta fadan ban ji ba ban yarda ba, saboda ina son ka, ko da ina son kudin ka, ya zan rayu yanzu ba nono ba mahaifa” rushewa tai da wani kuka mai ban tausayi, cikin tausaya mata Alhj ya fara magana” ki yi hakuri Baby yau zan…….. ka tse shi tai cike da bala’i” don’t baby me again, i hate u, i hate u, i hate u” ta qarasa tana kuka mai ban tausayi, matsawa yai ya kamo ta ta zame,” Don’t touch me u monster, if u touch me again i swear i will cut ur balls too” cike da fushin da bai san tana da shi ba, wani shakkar ta yaji ta shige shi, miqewa tai cike da jiri, zata fita, ” ina zaki kuma” ” gidan mu zani, na gama auren ka, na gama aure a ABUJA daga yau daga rana mai kamar ta yau” ” lallai ma Suwaiba, abinda baki sanj ba shine, ba inda zaki qara fita ko nam da can ne, kina tare da ni, dan yanzu ba zan iya rayuwa ba ke ba” ka mutu to, dan ba abinda zai hana ni barin gidannan, ko kana so ko baka so, in ka barni na tafi lafiya,ba hukumar da zan hadaka da ita, amma in ka hanani ba abinda zai hana ni hadaka da hukuma” wani murmushin rainin hankali ya mata ya ce” baki san wani abu ba, qungiyata babbar qungiya ce, manyan gwamnati da yan kasuwa ba wanda bab a ciki, ba yanda za ai ki hadani da hukuma kuma a samu hukunta ni din, mata dubin ki mun masu wannan aikin balle ke, dan haka hakuri zaki kawai mu qarasa rayuwa dake, in kin tafi wa zai na baki abun dadin danake baki?wa zaina debe maki kewa?wa zai zauna dake ba nono? Hakura zaki kawai mu zauna a haka” yana fada yana dhafa mata wuya, gaba daya ta qame ta dauke kantadaga ganin shi hawaye kawai take, ga wani tsoron shi a qasan zuciyar ta da take ji, yau ya zatai,kuka ne ya kwace mata sosai take yin kukan, key din motar shi ya dauka ya fice, anan ta durqushe tana kuka mai ban tausayi.
Talle kam ya saka marka a tsaka mai wuya ita da yayan shi, dan baya son maganar ta fita waje, gonar shi ta daji mai shegen nisa ya ke sasu zuwa gyaran ta, duba da cewar damuna ta kusa, kullum can suke tafiya ba abinci ba ruwa, amma shi zai je a machine din shi, da abincin shi da ruwan shi, saboda ya dinga ganin me suke masa, kar a masa ba daidai ba, su kuma su Baban gida gonar shi ta can wani qauyen dake kusa da su ya tura su, saboda ya yi yarjejeniya da su akan hakan, in ba haka ba ya kaisu birni ga hukuma, Kan kuce me Marka ta fita hayyacin ta, ‘yan duwaiwakan nan duk sun zube, tai qashin wuya da jiki, yan gari sai gulma suke amma sunnrasa dalilin Talle nayin hakan, da dama sai suka alaqanta hakan da tsantsar rashin mutuncin shi, su Huwaila kuwa kullum sai sun yi surfen abinda za ai tuwo da shi sun dake da hannun su sun mayar gari, sannan sui tuwon, ga aikin qannen su da ya dora masu, wahaka kamar zata kashe su,ga qaramin ciki. Jummala ce ta fito daga dakin tana riqe da cikin ta, tana ta murqususu, ” ke meye hakan zaki zo kina ma mutane kuka, kin gama aikin da na saka ki?”cikin kuka da tashin hankalin da take ji a jikin ta ne hasa ta budi baki zatai magana amma ta kasa, saboda wani abu da taji ya taho da gudu zai fita ta qasan ta, jini ne ya tsinke mata, nann d nan ta suma dan wuya, a gigice marka tai kanta,shi kanshi uban gayyar ya tsorata, daukar ta yai a hannu ya kai kan machin din shi, marka ma ta hau ta riqe ta, asinitin qauyen suka kaita, nan da nan aka tabbatar masu da bari tai, saboda ta sha wani magani na zubda ciki, ga jini yaqi daina zuba a jikin ta, suna buqatar a sai mata jini a qara mata zasui iya qoqarin su su tsaida jinin, Talle ne ya kalli matat shi, ” sai ki fito da kudade da kk ajewa ai mata magani ko” ya fada cikin hade fuska, ” to bari na koma gida” a qafa ta dibi hanyan duk tayi sanyi, ba cika da izzar nan ta da, kafin ta isa gidan ne ma likitan ta fito, take sanar da shu Jummala dai babu ita, sakamakon shan maganin zubda ciki da tai, yai resulting zub da jini mai tarin yawa a jikin ta, kuma sun kasa tsaida jinin har Allah yai cikawar ta, dafe kai Talle yai, nan take nadamar rayuwar shi ta baibaye shi, kuka yake kamar qaramin yaro suka samu wani mai machine din ya taimaka masa ya nemo mai motar da zasu kai ta gida tasha yaje ya samo masa motar, Tallen ya biya shi kudin, a motar aka maida su gida, Marka na shirin fotowa ta koma asibiti taga an fito da gawar Jummala, zubewa tai a qasa ta hau kuka da bori…….
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????