YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Hey guys, thank you all for ur love and support, ur comments……. ur comments ar awsome???? i love u all from my head over my heals ❤❤❤
Page 25:
Zanetake tana ta saqe saqe, tun fitar shi da safe har yanzu bai dawo ba, yana can ana sa toka sa katsi da shi, da Oga Zaks, akan deal din da sukai wanda ko Alhj Kalla bai san da shi ba, a baya sai da Alhj Salihu ya aminta da cewae ba za a kashe Suwaiba ba, za a san ya za ai a yanke mata nono kawai a bashi ita su tafi, ba za a sata a dakin duhun da aka saka sauran ba, dodon ya qarasa shanye jinin su suka mutu, in return, Alhj Salihu zai kai ma Oga Zaks Suwaiba for 2weeks, ya hanga ya hango, a gaskiya wannan karon ba zai iya ba, dan haka ne yau yaje akan a canja wani abun amma banda kai mai ita, a kyale ta haka mana ta wahala, shi yana son matar shi yanzu, amma sam Oga Zaks yace bai san zance ba, nan da sati daya zai buqace ta, idan bai kawo ta ba duk abinda ya same shi shi ya sani, hankalin shi tashe ya dawo gidan, ya isko ta ta fada dogon tinani, qarasa wa yai ya zauna kusa da ita, a doguwar kujera, ya zame ya dora kan shi a cinyar ta, ya rufe idon shi, cikin kulawa da tsoro ta fara shafa kanshi” Alhjna me ya faru? Me ke damun ka haka?” Bai bata amsa ba sai ma hawaye da ta gani ta gefen idon shi, hawaye ne na nadamar shigar shi wannan qungiya da yai tim farko, dan yanzu soyayyar Suwaiba tai mai yawan da ya farka daga baccin son abin duniya da yake duk da ita har yau tana nan akan bakan ta na cin daula, ” Baby ki kwantar da hankalin ki akwai maganar da zamui dake yanzu, wadda na san kin sani an sanar dake, amma kin rufe idon ki baki son yarda, tinda baki ga zahiri ba” tashi yai zaune ya riqe hannayen ta ya fuskance ta suna shaqar nunfashin junan su, kanta har juyawa yake, dan tana tsoron ya tabbatar mata da abinda Saudat ta fada, da kuma tabbatar da zargin ta na maida ita Nonoless and mahaifaless????tinanin ta ya katse ne a daidai lokacin da kalmar” ni dan qungiyar shan jini ne, dan samun kudi” wani ihu ta kurma ta dafe qirjin ta da yake a shafe kamar na Cute one kwaila????miqewa tai, amma jiri da duhun da take gani ya sa tana koma ta zauna , kallon shi take sosai ta tabbatar shine din? Taba fuskar shi tai, shi kuma ya dora hannun shi akan nata, saurin zamewa tai ta rushe da kuka sosai,” me yasa kk sanar dani? Sun ce ka kaini yanzu a yanken qafa ne ko hannu? Ko kaina suke so a yanke yanzu kai kuma ba zaka iya kai ni ba? Me yasa ka zabi shan jinin mutane kai kudi? Ina da son kudi da son abun duniya, qmma ba zan iya kashe mutum domin samun si ba, son kudi da abin duniya tane ya sa Saudat tana sanar dani na rufe ido kwakwalqata ta toshe zuciya ta ta rufe naqi yarda, mene ne hukumcin da ka yanke yanzu akaina har kk sanar dani wannan mummunan maganar?” “Babe pls calm down” ‘ calm what? U ar asking me to calm down after ur horrible confession? How would i ever trust u again? How do u espect me to trust u again with my life?” Ta qarasa cikin kuka mai cin rai, a idon ta kuwa ba wanda take hangowa sai Goggo Sarai, tai dana sanin kasamcewar ta uwa a garesu yanzu, da ta basu tarbiyyar da ta dace da basi zama masu son abun duniya ba, da basu zama idon su ya rife da son kudi ba duk hint din da ake bata akan su yan shan jini ne amma ta runtse ido, tsabar son abun duniya, now she is in a very big trouble that she kow that she cant escape it, ” Oh this life, ya zanyi yanzu ka fadan me ke faruwa yanzu to har kaji zaka fadan kai waye” hawaye ya share da sannan yace” Ogan mu ne da mukai deal da shi akan in ba a kashe ki ba zan kai masa ke, for 2weeks shine yake da buqatar ki ko ya dau fansa akaina, farkon zuwan ku ma sai da muka kai mai ku for 2weeks, ya dandana ku ya san akwai Ni’ima a tattare da ku mara misaltuwa, shine ya kwadaitu da na kai me ke akan alfarmar rashin kashe ki da ba ai ba aka yanke nonon ki dika” wani ihu Suwaiba ta sake ta hau kan Alhj ya na duka ko ta ina, qarshe da taga ko gezau bai ba sai ta kife tana ta rusar kuka” kaico na ni Suwaiba, kaico na, na shiga uku,yau ina zan saka kaina, ga abinda son abin duniya ya kaini, duniyar ta juyan baya, bata riqe ni a masoyiya ba, yanzu ni aka kaiwa dan shan jini for 2weeks” kuka ta sake mai tsima zuciyar mai sauraron ta, qanqame ta Alhj yayi yana shafa bayan ta, da sigar lallashi , fizgewa tai tace” to ina jin ka? Kana nufin kai mai ni za kai shiya sa kk sanar da ni wannan karon ko me?” ” ko daya, da ina son kai ki ai ba zaki sani ba zan kai ki, da da muke diban jinin ku dik wata sani kukai?” Zaro ido tai kamar su fado qasa dan firgita da tsoron shi, baya ta fara ja ta durqusa a guiwowin ta” dan son ka da annabin rahama kai min rai, kar ka qarasani, yanzu ni da mamaciya bamu da maraba, banda mahaifa, banda nono, jini na duk wata ake kwasa kamar a teku, an kaiwa wani qato ni ya gama sassaqata kamar tirmi, yanzu kana shirin maida ni sai ta Allah kuma” matsawa yai zai riqe ta ta ko falla da mugun gudu tai daki, kan ya isa ta fara qoqarin rufe qofar,yai saurin saka qafa ya tokare, ihu ta zunduma tana bashi hakurin yai mata rai ta tuba, ya maida ma Abban ta ita, dan yanzu ta tsani Goggo Sarai, ya taimaka kar ya tsotse mata sauran jinin nata, tura wa yai da qarfi ya janyo ta” ki nutsu dalla malama kar ki taran mutane ni, in da zan kai ki sauran duk sani kikai ba sai yanzu dana sanar dake ba? Na fada maki ne saboda ina son na maida ki gidan ku da kaina, in yaso duk abinda zai min ya min, na sadaukar da rayuwa ta domin taki ta tsira, Suwaiba this is how much i love u, i can give my life for urs” ya qarasa a hankali wanda ya sa jikin ta sanyi, qanqame shi tai tana kuka sosai,” i don’t want to lose u, i love u too, ban san sanda na fara son ka ba nima, a da kam tabbas kudin ka nake so, amma yanzu kai nake so, bana son abinda zai raba mu” sai ga Alhj Salihu na kuka kamar yaro, SO ba ruwan shi da girman ka ko qanqantar ka in ya shige ka yana saka aikata abinda ba hurumin ka bane aikatawa, haka sukai ta kuka ba mai lallashin wani, ba su ankara ba sai kiran sallan farko sukai na asuba, dan dama bai dawo da wuri ba sai 2am, miqewa tai jiki ba kwari for the first time, in her life da tai alwala dan wani abu na damun ta take son ta roqi Allah akai, shima dayaga haka alwalar ya yo, ya kabbara salla ta na bayan shi sukai nafila,suka hau addu’a akan Allah ya yafe masu, ya gafarta masu zunuban su, ya kubutar da su daga wannan al’amari da suka tsinci kansu a ciki, bayan sun idar da addu’ar ne suka yi subh prayer, suka tashi suka hau gado, bacci mai nauyi ne ya dauke Alhj amma ita inaaaa yaushe taga na barci, lallabawa tai ta bude wajen da take aje kudaden da yake bata, ta diba, ta dakko akwatin ta ta loda kayan ta a ciki, ta fita ta dau makullin mota babbar ciki a motocin shi, hawa tai ta nufi gate mai gadi ya bude mata, ta fice a dari, hanyar kano ta dauka, ko gajiya batai ba, haka ta iso gida a firgice, Alhj bai farka ba sai azahar, miqa hannu yai ya tabo Suwaiba yaji wayam, bai kawo komai ba, ya zaci ta shiga toilet ne, komar da kan shi yai ya lumshe ido,tinani yake ya kamata ya hada mata kaya ta tafi gida in yaso duk yanda sukai da Oga Zaks daga baya ya dawo da matar shi, miqewa yai zai shiga toilet din in ma wanka take suyi tare, yaga wayam, fita yai palo nan ma bata nan, leqa kitchen da sauran dakunan yai yaji shiru kuma bata nan, a hargitse ya fita waje wajen gate man yai,” kai Audi ina Hajiya?” ” Alhj ta fita da kaya da motar ka babbar” shafa kai yao daga gaba zuwa baya, komawa ciki yai, hankalin shi yana tsakanij tashi da kwanciya, na farko bata kware a tuqi ba bai fi sati biyu akai ana koya mata ba, gashi tana cikin tsoro, kar wani abu ya same ta, sannan can wani gefen yana jin haushin yanda ta iya gudun shi, duk da son daya nuna mata, kuma shima yaga soyayyar shi a tare da ita, miqewa yai ya dakko wayar shi ya hau kiran ta, tana ta ringing bata daga ba, hakura yai, ya je yai wanka yai sallah ya fita.