YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Qarfe biyar ta isa gida na yamma, hankali tashe ta fada gidan, tana kuka, da sauri Salma da Saudat dake tsakar gidan suna murza meatpie din da Salma ke sana’ar shi yanzu, tashi sukai suna zare ido ganin ta shigo da uban gudu ne ya sa suma suka so kwasa da gudu amma suka tsaya, da daya ta diba a guje nasan sai dayar ma ta bita, tsayawa sukai suga me ya koro ta, fadawa tai jikin Salma tana kuka, ” na shiga uku Salma, Saudat kinyi gaskiya, Alhj da kanshi yai confessing halayyar shi na shan jinin mutane, duba ku gani yanda aka maida ni” daga masu rigar tai qirjin ta ba komai, daidai nan Goggo Sarai ta fito sakamakon jin abinda Suwaiba ke fada…………
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ???????? ‘ YAN ABUJA ????????
BY HAERMEEBRAERH
Masoya na da masoyan wannan Novel na ‘YAN ABUJA, ina roqarwa wannan yaya tawa addu’a daga bakunan ku masu albarka, akan Allah ya biya mata dikka buqatun ta na alkairi, (Yah Ilham) Ina roqon Allah daya saka maki da alkairi ya biya maki buqatun ki na alkairi, Allah ya raya mana Naana, kin sani farin ciki jiya Allah kema ya faranta maki, na gode sosai Allah ya qara mana zumunci.❤
Page 26:
Nishi kawai take ita daya, gaba daya a gajiye take, ta gama shaving hammatar ta, tana son tai shaving HQ, duk ta gaji, tai zufa, shigowar shi ne yasa ta daga kai tana kallon shi, dariya ce ta zo mai amma ya san halin ta da yayi da ta fashe, ” Yah Jabeer i need some help here please” ta fada with a shaky voice, da ji ta kusa fashewar kamar yanda yace,” Au ai na zaci u don’t need any help, tinda ai ko da dai da ba cikin ni nake yi, ke kuma ki taimaka min nima, shine kawai daga fita gaida Innar mu gajen hakuri yasa kk fara” haba ai kamar jira take ta bara baki sai hawaye,” to ba na gaji da jiran ka bane, shine dan na ce ka taya ni kk son fadam magana ko, ba komai a barmin abuna zan yi da kaina” shi yanzu mamaki ne ke damun shi, kwata2 yarinyar ta canja, abu ba abu ba sai ta hau fada, ko ta hau fushi akai, yanzu dai me ye abun jin haushi anan? Murmushi yai na Allah dai ya raba ku lfy, na san meye matsalar ki, ni ne sanadi dole na lallaba ki,” Husshhh Husshhh my princess, bari kuka, Yayan ki is here to help,can i have d shaving stick?” Share hawayen tai ta miqa mai, komawa tai ta kwanta ya gama mata, miqa mai hannu tai ta tashi ta nufi waje, ruwannan nan da ta ke hadawa na tsarki shi ta dauka wannan karon harda kaninfari da ganyen magarya, dan tana son wanke wajen sosai, wankewa ta je tai ta gama ta fito, still fuskar ta ba walwala, ” Haba Juwaireren Mama Juwaireren Yah Jabeer, me kuma ya faru, me kk so gaba daya bana jin dadin rasa murmushin nan naki mai kwantar min da hankali, da ki hana ni murmushin ki gwanda ki hana ni ruwa inna dawo daga kasuwa a gajiye” bata san sanda murmushi ya kwace mata ba, dan tasan yanda yake matuqar son ruwan sanyi in ya dawo daga kasuwa, qarasawa inda yake tai, ta zauna a jikin shi tana kukan shagwaba, tana zamewa a jikin shi, gaba daya ta susuta shi, ” Babe, ni agwaluma nake son sha” cike da kasala yake kallon ta” kin tabbata ita kk so yanzu?”ya fada yana kashe mata ido daya, yana shafa cikin ta, saurin kauda kai tai dan ta fuskanci effect din da take da shi a wajen shi musamman in tana shagwaba a jikin shi tana murza ko ina na jikin ta a nashi, tashi tai tana son gudu, dan she is not ready for him, saurin riqeta yai yace “tin dazu nake daurewa, yanzu ke da kan ki kin san ke kk jawo dan haka muje na duba bbyna sai inna gama naje na siyo maki agwaluma ya kk ce?” Biga qafa ta fara cike da shagwaba sannan tana qara narkewa a jikin shi, ” Ni dai Honey ban da lfy” “muje na baki.magani to” ” ni dai Aa” kan tai wani yunquri tini ya dauke ta sun yi bedroom din su. Jan qofar yau ma yai nace da qarfi, ka daina min irin wannan in ba haka ba na fara maku leqe, ai ni bance zan biyo ku ba dama????????( yan uwana mata ina son fadakar damu akan murmushi, macen da ta cika mace ta san wacece ita, murmushin ta kawai ya wadatar da ita wajen bawa mijin ta farin ciki, komai bacin ran da mijin ta ke ciki, murmushin ta zai iya calming din shi daga dikkan damuwar shi, murmushin ta zai zama abun da mijin ta zai iya tinawa a ko ina yake ya jishi cikin nishadi yaji shima yana murmushin ba tare da ya sani ba, abu na biyu shine, da damar mata ba su iya shagwaba ba, shagwaba kala2 ce, amma wadda ta fi tasiri, ko da namiji na cikin fushi ki kwantar mai da hankali, ko da namiji bai da buqatar ki , ko bai da sha’awar ki yaji nan da nan ba wani abu da yake so a jikin shi ko kusa da shi sai ke, ba komai bane face shagwaba irin wadda yara suke yi dinnan suna hawa jikin mutum suna murza shi ko ina na jikin ki ya zama yana manne dana oga kina murza jikin ki da nashi kina zamewa, yanzu zakiji sauyin yanayi????)
Faduwar da sukaji anyi a bayan su ne yaja hankulan su sika juya gaba dayan su, Goggo Sarai suka gani zube a qasa, idonta bude hawaye ya wanke fuskar ta, ta sa hannu ta toshe bakin ta, da sauri Mama Bilki ta isa, dan ta kula gaba daya yaran nata kallo suka bita da shi, ba wacce ta motsa, daga ta tai, ta kaita kan kujerar dake daf da bakin qofar ta zaunar da ita, ruwa ta debo mata ta miqa mata a cup, kasa shan ruwan tai tana ta kallon Suwaiba da ta hade girar sama da qasa, tai hanyat dakin Mama Bilki, kuka ne ya kwacewa Goggo da taga yaran ta duk sun bar wajen sun yi dakin kishiyar ta da ta dasa musu tsanar ta a ransu, yau itace abin son su, wani gululun baqin ciki ta hadiya, ta kalli Mama Bilki da ita daya ce a kanta ta kauda kai taci gaba da zubda hawaye, Abban su ne yai sallama ya shigo, dakin Mama yake can ya nufa, kukan da yaji ana yi a dakin je ya ja hankalin shi ya qarasa da sauri, ” Suwaiba ke nake gani? Meke faruwa ne, naga kuna kuka, ku sanar dani damuwar ku yarana, duk da banda arziqin da zan maku maganij ta, Allah ya horen bakin yi maku addu’a akan komai” Suwaiba ce ta je gareshi da gudun ta ta rungume shi, shima eungume ta yai kuka take mai ban tausayi, bai dago ta ba, sai da tai kukan ta ya ishe ta, sannan ta zame ta zauna a qasan qafar shi” fadamin diyata, fadan damuwar ku naji” ” Abba…. Abba ka yafe min, Abba ka yi hakuri akan qin jin maganar ka da nai abaya, Abba nadama ta samen alokaci qurarre” ” Aaa Suwaiba karki ce haka, lokaci bai qure maki ba yata” ” Abba duba ka gani” daga mai rigat ta tai ta nuna mai qirjin ta da gefen cikin ta, anan ta juya wajen Saudat tace” Saudat nuna mai cikin ki kema” nuna mai tai itama tana kuka,” me ke faruwa haka” Abban ya fada cikin tashin hankali ganin da yai Suwaiba ta zama Nonoless, ” Abba mazajen da muka aura ta dalilin mugun son kudin mu, da influence na Goggo, Abba yan qungiyat shan jini ne su” ta qarashe cikin qunar rai da dacin da take ji a wuyan ta, a zabure Abban su yace ” me kk ce? Shan jini fa Suwaiba, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Ya Allah, wannan wace irin rayuwa ce haka? Ya salam” zama yai ya dafe kan shi,” to sanar dani me ya sami qirjin ki da kuma gefen cikin ki gaba dayan ku ke da yar uwar ki?” Kwashe komai tai ta fada mai, cikin kidima da tashin hankali ya miqe ranshi ya gama baci da jin abinda ya samu yaran shi, duk ta dalilin matar shi da ta kasa taimaka mai wajen ba yaran shi tarbiyya, ficewa yai a dakin ya nufi dakin Goggo,” hankalin ki ya kwanta, Saratu hankalin ku ya kwanta nace, an mai damin Yara marasa haihuwa, ba zan taba ganin jikokina ba ta bangaren su, ke baki saki jiki kin haifa min yaran ba,ga shi kin ja sanadin son kudi da abin duniyan ki ya sa jikokin nawa ma zasu zama ragaggu, ban manta wa ke da kan ki ki kai kutunkutun ki ka tsaida haihuwa, wai yaran sun ishe ki, wace irin mace ce ke? Ki duba kiga Suwaiba an yanke mata nono gaba daya, banda jinin yaran nan da ake diba duk wata, tsahon wata takwas, ina zaki kai alhakin su?” A wannan lokacin Abba kuka yake, Goggo kuka , yaran kuka, Mama Bilki hawayen tausayin yanda rayuwar gidan na su cikin qanqanin lokaci ta koma take, wannan rayuwa ! Goggo ta kasa cewa komai, bakin ta rawa kawai yake, sai zatai magana sai ta ji bazata iya cewa komai ba, Suwaiba ce ta katse su da cewar” Abba ina neman izinin ka barni nai mana daki a ta can wajen, dan ba zan iya ci gaba da zama da Goggo a daki daya ba” murmushin takaici Abban su yai yace” kinji ? Kinji da kunnen ki, Yar ki ba zata iya zama dake ba? Kar ki damu Suwaiba, wannan kudin bai kamata ki amfani da su ba, kamata yai a bada sadakar su, ina da qasa, da ciment, dan dama ina da aniyat yin daki dan ku, koda kun zo ganin gida, dan haka da kaina zan yi” juyawa yai ya fita, kamar abun wasa Abban su ya fata hada qasa da komai, nan da nan Suwaiba da yan uwanta suka hadu suna taimakawa mahaifin su wajen yin ginin, harda mai ciki, Ammar ne ya tako dugui2, ya isa wajen su ya debo qasar a hannun shi ya miqawa Abban su, dariya sukai gaba dayan su, a haka Ammar ya zama shi ne ke saka su nishadi har yamma ta gabato Mama Bilki ko tana can tana masu girki har ta kammala, Goggo ba wanda ya kula da yin ta, ko kukan ta, sun maida hankali akan son yin dakin da zasu nesanta kan su da ita, ginin ya masu nisa sosai, a haka suka bar wa gobe sukai wanka, suka zauna bangaren Mama Bilki, suka zauna gaba dayan su, a babban faranti ta zuba masu, kowa ya saka hannu har Abban su suka fara ci, Mama Bilki ce ta miqe Abba ya kalle ta” Ina zaki kuma Sarauniya ta?” ” Abban su zanje na kira Yaya ne, mu ci abincin dika” cikin zare hannayen su dika, tare da turo baki alamar basu yarda ba suke kallon ta” kin samu amsar ki a wajen su dan haka zauna mu ci bincin mu” komawq tai ta zauna, suka gama ci suka wanke hannaye suka sha ruwa, wanke kwanon Saudat tai ta aje ta dawo suka zauna suna ta hira, suna wasa da Ammar” Mama Ammar ya girma yai wayo sosai” ” aiko dai kinga dik sa’annin shi ya fisu girma da wayo” ” lallai kam” ” Suwaiba, Saudat, Salma” daga kai sukai suka kalle ta jin yanda ta ambaci sunan su alamar ba wsa, amsawa sukai gaba dayan su suka zuba mata ido” ina son na baku shawara a matsayina na uwa, sannan ina son ku duba abinda zan fada maku da da kyau, ku qoqarta amfani da shi, kun ga da farko dai uwa ba kamar ta a rayuwar duniya, Allah ya ce abi shi sannan abi iyaye, Annabin rahama ya jaddada bin uwa sau uku kan uba, dan haka ni ina son ku yafe ma mahaifiyar ku abinda tai maku, tabbas bata kasance uwa ta gari ba, mai ba yaranta tarbiyyar da musulunci ya tanadar, amma ta baku so, ta nuna maku qauna, na uwa da yaranta, in kun kula ita a tinanin ta tayi abinda ya dace daku ne, amma koma dai menene ina son ku sani, wanda bai yafe ma wani ba, shima ya ji tsoron kar Allah ya qi yafe mai nashi laifukan, dan haka nake mai baku hakuri a madadin ta, ku taimaka ku yafe mata, kar kuja wani ciwon ya kama ta dan Allah na roqe ku” cikin kuka suka matsa kusa da ita suka rungume ta, Suwaiba ce tai magana a cikim su” Mama Bilki ke alkhairi ce a rayuwar mu, ki yafe mana abubuwan da mukai maki a baya, tabbas mun cutar da ke sa kalaman mu, da ayyukan mu, bamu zama yara masu biyayya ba, ki hakuri ki yafe mana” ” indai nice na yafe maku baku ce man komai game da Yaya ba?” Salma ce ta amsa masu dan Suwaiba da Saudat har yanzu akwai daci da wata irin qiyayya da suke ji game da mahaifiyar tasu, amma sun sani dole su yafe mata, sui hakuri da abinda ta musu” mun yafe mata Mama Bilki Allah ya yafe mana” ” to ya kamata kuje ku sanar da ita kar ta kwana cikin damuwa” Suwaiba ce tai saurin miqewa” ni dai Mama ba zan iya zuwa yau ba, dan Allah kar ki tirsasa ni yin abinda ban jin zan iya yin shi a yanzu” ta qarasa cikin kuka,”Bilkisu Allah ya miki albarka, amma ki bar su haka, zuqatan su cike yake da abinda ta musu, daga baya a hankali komai zai warware masu” ” to Allah ya kaimu, Allah kuma yansanyaya zuqatan ku ku yafe mata gaba daya” amsawa sukai dika da ” Ameen” hankalin Goggo kam ya kai qololuwa wajen tashi, Wanj duhu take gani ya rufe mata ido……
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????