YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

    BY HERMEEBRAERH

Page 27:

Kuka kawai talle yake ya kasa tsaida hawayen shi, wannan rayuwar ba wanda ya ja ma su ita face shi, mugayen halayen shi ne da yi ma yaran mutane sakin wulaqanci, da zinace2n shi ne ya kai su ga haka, gashi tsabar lalacewa Yayan shi ke neman matar shi ta sunna, Yaran yayan shi na neman na shi yaran, kaiii jama’a wannan wace irin musiba ce ta sauko mana a wannan zamani, Marka kam irin kukan qabilun nan take, tai girgiza tai girgiza tai kukan sai kuma tai dif ta cigaba da gyada kai, abun ya shigeta sosai ba kadan ba, jummala ta mutu sakamakon yunqurin zubda ciki, ga Hawaila tana kallo a gaban ta da ciki dan kuyat a gaba, itama ga nata farkan a gefe, wace irin rayuwa suka jefa kansu a ciki? Maqota ba mai zama wai da sunan makoki, ko sun shigo yada magana ne yake kawo su, wasu daga ciki zakuji suna cewa” Tohhhh abinda ya faru kenan hmmmm Allah dai ya jiqan ta amma zunubu kam an kwasa” ire2n kalaman mutane kenan ana yi ana kyabe baki, wasu kuma bayan sunyi gaisuwar sai sun dora da” ikon Allah kamar ciki nake gani a jikin Huwaila, ni dai bani da labarin auren ta, sannan mun san ba a shan ciki a ruwa, hmmmm Allah ya kyauta,gidan Talle kenan, gidan uwa ba kwaba ya ba hantara” kowa da abinda yake furtawa, baqin ciki kamar ya kashe Haule, wai yanzu nan ne gidan ubanta, gidan da ba tarbiyya ba kwaba, yanzu itama tambarin ya shafeta, ai kuwa da an gama arba’in guduwa zatai qauyen da taji wata qawar Marka da tazo kwanaki ta fada da sunan wata mata a matsayin mahaifiya gareta, mai suna Husai, qauyen yana nan kusa da su, in ta zauna a gidannan ko mashinshini rasawa za tai, in ko ta koma can ko sunqi karbar ta ba zata dawo nan ba, kwalla ta share ta ja hanci, tana kallon su cike da tsana, da tsanar halayen su, tashi tai daha wajen kwata2 tai shigewar ta daki,addu’a take taima ‘Yar uwar ta a ranta na Allah ya yafe mata, Yayan Talle kuwa zaman daki ya kama shi, bai da damar fita waje dan abin kunyar da suka aikata, by now kowa ya san meke faruwa a gidan Talle, ba kowa a qofar gidan yan karbar gaisuwa ko yan gaisuwan, sai su Baban gida da Badamasin, Talle kallon su yake kamar ya shaqe su, amma yasan a iskancin da sukai shi yayi ninkin nasu sau ba adadi, nade tabarmar da yake kai yai ya shigo, fakam2 ya tsaya kan Huwaila, kwalama su Baban gida kira yai, suma shigowa sukai da tabarmin su a hannu, kai a qasa kamar munafukai,” a cikin ku waye me cikin Huwaila?” Badamasi ne ya nuna Bangis, shi kuma ya qara duqar da kai qasa,” Yanzu yarannan wai har kunyi girman dirkama wata ciki? Ko dake maganar wai kun yi girma ma bata taso ba tinda ga misali kun bayar, kun yi sanadin mutuwar daya, ga daya nan da tambarin abin kunyar da zai bi zuri’ar mu har abada, dan haka sai ka bari ta haihu a maku aure kun renu dan shegen cikin gidan da kuka samar tare,” cikin tsananin qunan rai yake maganar, ita dai Marka bata cewa umm bare Aa, tai dif sai hawayen nadamar rayuwar su ke fita mata, a cikin zuciyar ta tana ayyana wannan lamari ba laifin kowa bane face nashi, daya tsaya ya tsare mata sha’awar ta da buqatun ta da batai zina da auren ta ba,( dik d wannan ba hujja bace ga matan da suke ganin dan mijin su baya sauke haqqin shi akan su bari su bazama neman mazan waje, ko su fara aikata wani abun da ya kauce hanya, su sani Allah zai masu hukunci daidai da abinda suka aikata ne shima mijin Allah zai mai hukuncin abinda ya aikata, so ni a ganina ba dabara banw hakan, wadda ke da matsala haka maganij ta ya kamata su zauna suyi in ya gagara su tattauna da mijim to ta nemi waliyyan su su shiga lamarin haka islam ya tsara,bai halatta ta fada halaka ba da sunan rashin kulawar miji mu kiyaye)miqewa marka tai zata shiga dakin ta, ya dakatar da ita, ” Marka ina neman yafiyar ki akan dikkan abubuwan da suka faru tabbas laifi nane, da na tsaya na zama namijin kirki da duk haka bata faru ba, ki yafe min mu dawo mu gyara rayuwar mu,”kauda kan ta tai saboda kukan da yake neman cin qarfin ta ga wani haushin shi da take ji na jefa su wahala da yai, Yayan shi ne ya fito daga dan qaramin dakin shi ya zube akan guiwowin shi” Talle qanina ka yafeni na biye wa son zuciya, da rudin shedan na aikata mummunan abun da ko mutuwa mukai sai yabi zuri’ar mu, ka taimaka ba dan ni ba domin Allah da zumunci ka yafen” kuka ya kifa hannayen shi a fuskar yana yi, Talle daga shi yai kawai ya dan daki kafadar shi dan shima kukan yake ji, kauda kai yai zai shige daki yaji maganar yayan nashi,” a gaskiya sai mun gyata rayuwar gidannan namu kan komai ya tafi daidai, na farko yanayin yanda iyalin ka take yawo a tsakar gidannan ya jawo min matsananciyar sha’awar kasancewa da ita, dan zakaga tana yawo ba isasshen kayan da ya rufe dikkan jikin ta, tana tafe tana juya dikkan jikin ta, sannan ga maganganun ta danake jiyo wa yawancin su na batsa ne, wajen kallon ta da maganar ta bata kiyayewa, wadannan abubuwan sun ja ra’ayina matuqa, dan haka in muna son mu samu kwanciyar hankali da kiyaye war zinace2 a tsakanin mu sai mun kiyaye, sakewa yarannan da mukai shima ya jawo wannan bala’i da muka shiga har yai sanadin mutumar Jummai, ( sakacin iyayen yanzu da kusan nace kowanne gida hakan na faruwa,sai ace cousen din tane ai, kaji tana yayana ne, ko yana qanwata ce, amma da sun samu sarari su biyun su zai zauna ya lalube ta tsaf ya miqe, ita kuma tai dif da bakin ta, da wuya kaga cousens din da a wannan zamanin suke gida daya ko suke yawan ziyartae juna wata barna ba ta gilmawa, wanj sa’in gaba ga iyayen zakuga suna kallon yanda Yarinya ke mannewa namijin amma sai su dau hakan a wayewa, kuga tana wasan banza da namiji sai ace ai yayan ta ne ba komai,sai barna ta faru a zo ana dana sani wasu ma ba a sanin barna ta faru sai sun aurar da yaran, za a duba yarinya bata kai budurcin ta gidan miji ba cousen ya dauke a cikin gida, maybe ma a dakin uwar ta, can u imagen, wannan wace irin rayuwar zinace2 muka shiga? Mu yawaita nemawa kan mu tsari akan zina yan uwa Allah ya kare mu) Talle ne ya amshe maganar da gaskata yayan nashi, kuna ya basu tabbacin dawowar shi qauye da zama, don ya gama xaman birni kenan, murna kam Marka ta yi ta da jin wannan zance, amma ba ta ce komai ba har yanzu, a haka suka watse kowa ya kama inda zai yi cike da alhinin mutuwar Jummala.

Su suwaiba sun kammala ginin dakin su tsaf, sai dai ba flasta, ba fenti, sai ledar daki da suka fara shimfida qaton buhu a qasa sannan suka saka ta, katifa biyu suka saka, babba da qarama daya, sai kayan sunda suka kwaso suka zuba ciki, daki yayi ba laifi, amma ba wani wadata da yalwa sai godiya kawai, kullum dare Suwaiba sai tai kukan rashin mijin ta da kuma yanda ta koma, yanzj wa zai aure ta? Yaushe Salihu zai aiko mata da takardar sakin ta? Ko yazo ma ta ganshi? Haka za tai ta saqe saqe har bacci barawo ya dauke ta. Goggo ta kamu da mummunan hawan jini, sakamakon sanya tinani da damuwa da tai, sannan yanda ta saba Yaran ta na manne da ita yanzu tsakanin su gaisuwa, in suka gaida ta sai dai tajiyo hayaniyar su da Mama Bilki tana koya masu abubuwan da ya dace, suna kuma wasa da Ammar kamar ciki daya suka fito, abun ba qaramin daga mata hankali yake ba, asibiti kam taje shi a kwanakin nan yafi sau nawa, dan sai kawai tana zaune taji wani jiri da duhu ya mamaye ta, sai suma, haka za su kaita a bata magani sui qoqarinnda zasui ta farfado si sallame ta Abba ya maido ta gida, takan ce a ranta ” Oh ni Sarai naga duniya, Yarana danake taqama da su a idon duniya su suka juyan baya yanzu, Allah gani gare ka” yau Goggo ta tashi da matsanancin ciwon kai, in da ta dinga kiran Suwaiba ta na zaune tana jin ta tai shiru, Mama Bilki ce ta leqo ranta bace tace” Suwaiba kina son shiga aljanna kuwa? Mahaifiyar ki na kira kina ji ki shiru? Wallahi ki kiyayi Allah, ki kiyayi fushin uwa suwaiba, meyasa kk da ruqo ne, shi wancan mijin naki mai qaton ciki ba dan dan kyaun da yake da shi ba meye abin so a wajen shi, duk da wahalar da suka jefa ku kina nan kina faman son shi, kina begen shi, sai uwa wadda ta haife ki, itace baki san ki yafe wa ba ko? To na qara jin haka tana kiran ki kina ji ki zauna kiga ya zamu qare a gidannan da ke, shashasha kawai,kin miqe ko saina kwado maki wannan murfin kwanon?” A hanzarce ta miqe tana kallon hannun Mama Bilki mai kwanon, shigewa dakin Goggon tai tana zumbura baki” Gani” shine abinda tace ta ja ta tsaya, ” Suwaiba nice fa Goggon ki, abar son ki, Suwaiba ba dan Adam din daya wuce kuskure, nayi kuskure, na yi nadama ku yafe ni ke da yan uwan ki, na san ban zama uwa ta gari ba,ko wannan ciwon da nake fama da shi ya ishen ciwon kai ba qaqqautawa, na rasa ya zan kuma duk.sanadin juyan baya da kukai ne, a tinani na a da rayuwa mai kyau nake baku, dan Allah suwaiba ku yafe wa Goggon ku kunji?” Kuka Suwaiba take sosai, harda majina, kusa da goggon ta taje ta zauna ta dora kanta kan cinyar goggon ita kuma ta hau shafawa, ba wanda ya qara cewa komai, nan take Goggo sarai taji kamar ana zare mata ciwon kanta, damuwar ta na raguwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button